ME AKE NUFI DA SUNNAH?
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=674

 
DAGA ZAUREN SUNNAH DA TAMBAYOYI:

ME AKE NUFI DA SUNNAH?

Kalmar SUNNAH tana da ma'anoni masu yawa duba da yadda malamai sukayi bayaninta a fannonin ilmi daban- daban.

Ga wasu daga cikin ma'anoninta:

1- Sunnah a wurin malaman Lugah(wato malaman harshen larabci): Shine hanya ko turba.

2- Sunnah a wurin malaman hadisi: Shine abunda aka samo ko aka jingina ga Manzon Allaah sallallaahu alaihi wa alihi wasallam na magana ko aiki ko tabbatarwa(ma'ana abunda akayi a gabanshi ko a zamaninsa yayi shiru baiyi inkarinsa ba) ko sifa na halitta da dabi'unsa.

3- Sunnah a wurin malaman usulul- fiqh:

Shine abunda aka samo daga Manzon Allaah (s.a.w) na magana ko aiki ko tabbatarwa wanda zai iya kasancewa dalili a shar'ance.
4- Sunnah a wurin malaman fiqhu: Shine abunda idan musulmi ya aikatashi za'a bashi lada, idan kuma yabarshi baza'ayi mishi u'kubah ko rubuta mishi zunubi ba. Misali kamar karanta sura bayan fatihah a cikin sallaah.

Sai dai ba'a kiran abu sunnah sai idan ya inganta daga Manzon Allaah(s.a.w), a karkashin haka ba daidai bane mutum yace: wannan sunnar bata inganta ba, sai dai yace wannan hadisin bai inganta ba, amma shima sai idan yakai matsayin fadin hakan, domin inganta hadisi ko raunatashi ba da molon kai akeyi ba; da ilmi akeyi. Idan kuma mutum bashi da ilmin dazai iya gano inganci ko rashin ingancin hadisi to sai ya dogara da ingantawar wani daga cikin malaman hadisi kwararru wadanda sukayi nutso a cikin ilmin, kamar: Al-imam Malik, Al-imam As- shafi'iy, Al-imam Ahmad bn Hanbal, Masu alkutubus-Sittah, Aliyu bnul Madiniy, Ad- daraqu'dniy, Al-kha'dibul Baghdaadiy, Azh- zahabiy, Ibn Rajab, Ibn Hajr, Ahmda Shaakir, Muhammad Nasiruddenil Albaniy, d.s.

Kuma ita sunnah wajibine abita a kuma yi aiki da ita, babu banbanci tsakanin farilla da sunnah(a wurin malaman fiqhu) da mustahabbi, domin karkasa abunda ya tabbata a shari'ah zuwa farilla ko sunnah ko mustahabbi anyishine domin idan akasamu matsala ko tangarda a cikin ibadah asan yadda za'a gyarata. Ba an karkasasu bane domin ayi aiki da wani abar wani ba.

Kuma ita sunnah ba a baki bane kadai ko a rubuce ba; a'a dole sai anhada da aiki, domin shi imani da Manzon Allaah(s.a.w) baya tabbata sai idan ka yarda da sunnarsa, sannan ka furta, sannan kuma kayi aiki da ita.

Muna rokon Allaah ya rayamu akan sunnah, yadauki ranmu akan sunnah, ya tashemu ranar Alkiyamah tareda Ahlussunnah, yakuma hadamu da maigidan sunnar bakidaya a Aljannar Firdausi.
Batun: Al'Adun Musulmi Da Darajoji