SAKON KHUDUBAR JUMU'AH DAGA MASALLACIN MANZON ALLAH (SAW) DAKE GARIN MADINA
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=678

 
Sheikh Isa Ali Pantami

SAKON KHUDUBAR JUMU'AH DAGA MASALLACIN MANZON ALLAH (SAW) DAKE GARIN MADINA

SAKON KHUDUBAR JUMU'AH DAGA MASALLACIN MANZON ALLAH (SAW) DAKE GARIN MADINA DAGA BAKIN SHEIKH, DR, IMAM BABA ALIYYU BN ABDURRAHMAN AL- HUZHAIFIY (Rahimahul Laah). JUMU'AH 21/ Rabiul-Awwal/ 1437AH (1/1/2016CE).

Dattijon Arziki, Dr Huzhaifiy (Hafizhahul Laah) yayi khudubar akan "DARAJAR ADDU'AH DA MATSAYINTA GA MUSULMI." 1) Imam ya fara khuduba da yabo ga Allah (SWT) da Salati ga Annabi (SAW) da adduar alheri ga Sahabbai (RH) da sauran Salihan bayi.

2) Sannan yayi wasiyyar Taqawah ga Musulmai, cewa ita taqawah ribar rayuwa dukka ya tattara gare ta ne.

3) Allah ya kaddara dukkan alheri yana da sababin aukuwarsa, haka kuma kuma dukkan sharri yana da dalilan faruwarsa. Wajibi ne muyi riko da dalilan alheri, kuma mu nisanci dalilan aukuwar sharri.

4) Duk wanda yayi riko da alheri da kuma hanyoyin alheri na Duniya da Lahira, Allah zai saka masa da Aljannah. Allah (SWT)
yana cewa: Shin akwai sakamakon alheri in ba alheri ba? Maanarsa duk wanda ya aikata alheri, Allah zai saka masa da alherin Duniya da lahira.

5) Addu'ah tana da amfani cikin dukka abun da ya faru ga Mutum a rayuwa, da cikin dukkan abunda bai faru ba.

6) Dalilan da ke kawo wa mutum gyaruwa, da rabautuwa, da nagarta shine "Adduah bil Ikhlas" wato yin addu'ah da tsarkake zuciya a cikinta.

7) Lalle Allah yace mu roke Shi zai amsa mana.

Allah yana cewa a cikin Qur'ani: "....Ku roke Ni zan amsa muku. Lalle ne wadanda suka yi girman kai daga yimin ibadah (addu'ah) zasu shiga Jahannama...." 8) Annabi (SAW) yana cewa: addu'ah itace ibadah. (Abu-Daud da Tirmizhiy suka ruwaito)
9) Allah ya karantar da mu adduah, idan ba dan ya koya mana ba, da bamu iya ba.

10) Babu lokacin da Musulmai ke bukatar addu'ah kamar wannan zamani na FITINTINU.

Zamani ne da musifu suka yi yawa a Duniya.

Zamani da MUNANAN AQIDU, MASU BATAR DA JAMA'AH SUKA YAWAITA. Zamani da KAFURAI suka yi chaaaaa akan Musulmai.

11) Wannan zamani dole mu dage da adduah. Domin shine zamanin da Allah yake cewa: "Wallahi zamu jarrabeku da wani abu na tsoro, da yunwa, da tauyewan dukiyoyi da rayuka. Amma kayi bushara ga masu hakuri." 12) Annabi (SAW) ya karantar da mu addu'ar Yunus (AS) na cewa:

Laa'ilaha illa Anta, subhaaanaKa inni kuntu minaz Zhalimin." Annabinmu yace: babu musulmin da zai yi addu'ah da wannan addu'ah face Allah ya amsa ma sa.

13) Adduah tana saukar da ALBARKA a rayuwa kuma tana bada kariya daga sharri. Kamar yadda Allah ya amsa addu'ar Annabi Ayyub (AS) ya ba shi waraka daga cuta.

14) Zuwan Dujal shine mafi girman fitina da Duniya ke fustanka.

Amma duk da haka addu'ah tana taimakawa wajen samun tsira daga fitintinun Dujal din.

15) addu'ar da Annabi (SAW) yayi wa Sahabbansa (RA) a Badar na daga cikin dalilin NASARAR MUSULMAI A DUNIYA.

Wannan Nasara kuma har zuwa ranar Kiyaamah.

ADDU'AH TANA DA SHARUDDA DA YAWA.

DAGA CIKINSU AKWAI:

16) CIN HALAL yana daga cikin sharuddan karban addu'ah. Kamar yadda Annabi (SAW) ya karantar da Sa'ad Bn Abi Waqqas (RA).

17) RIKO DA SUNNAH yana daga cikin sharuddan karban addu'ah.

18) Duk wanda aka zalunce shi, Allah yana amsa addu'ar sa, ko da KAFURI ne, ko da DAN BIDI'AH ne, Allah yana amsa addu'ar su idan an ZALUNCE SU.

19) Ikhlasi shima sharadin amsa addu'ah ne.

20) Yabon Allah lokacin adduar.

21) Rashin gaggawa lokacin adduah.

22) Dauwama kan yin adduah shima sharadin karban adduah ne.

AKWAI LOKUTAN KARBAN ADDUAH SUNE:

23) Sulusin dare na karshe. Wato ka shi daya na ukun dare na karshe.

24) Tsakanin kiran Sallah da ta da iqamah.

25) bayan kammala saukan karatun Qur'ani.

26) Lokacin ganin Ka'abah.

27) lokacin ba da Sadaqa.

28) Lokacin saukan ruwan sama.

29) sannan haramun ne yin adduah ta hanyar rokon matattu.

30) Duk wanda yayi wa Allah tarayya da wani a cikin adduah, kuma ya daidai Allah da waninSa lalle yayi SHIRKA MAI GIRMA.

RUFEWA:

31) Babban limamin yayi Salati ga Annabi (SAW)
da salatin Ibraahimiyya.

32) Adduah da Sahabbai da Tabi'ai da wanda suka biyo bayansu da kyautatawa.

33) Adduah ta Musamman ga Alkhulaafu Arrashidun, Abubakar da Umar da Uthman da Aliyyu (Radhiyallahu anhum), Allah ya kara yarda da su.

34) Yayi Adduar neman gafara ga Matattunmu gaba daya, Allah ya gafarta musu.

35) Yayi Addu'ah ga marassa lafiya, Allah ya basu lafiya.

36) Yayi Allah ya karya Azzuluman da ke kashe bayin Allah a kasar Sham.

37) Yaa Allah ka taimaki addininKa.

38) Yayi addu'ar Yaa Allah ka datar da "Khaadimul Haramayn" ga duk abun da Ka ke so, kuma ka yar da da shi.

39) Allah ka bamu ruwa mai albarka.

Fassarawa: Isa Ali Ibrahim Pantami (21/03/1437AH. Kai tsaye daga Haramin Madinah).

Yaa Allah ka bamu ikon aiki da khudubar da darussa da ke cikinta, kuma ka amsa mana addu'o'inmu,....
Batun: Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi