JAHILCI DA AUREN MUTU'A KE JEFA MATASA CIKIN AKIDAR SHI'A, INJI SHEIK
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=679

 
JAHILCI DA AUREN MUTU'A KE JEFA MATASA CIKIN AKIDAR SHI'A, INJI SHEIK YUSUF SAMBO RIGACHIKUM

Rariya Jahilci Da Auren Mutu'a Ke Jefa Matasa Cikin Akidar Shi'a, Inji Sheik Yusuf Sambo Rigachikum DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA Mataimakin shugaban majalisar Malamai na Kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'a Wa Ikamatus Sunnah na kasa baki daya, Sheik Yusuf Muhammad Sambo Rigachikum, ya bayyana cewa tsagwaron bakin jahilci na addini daga bangaren Kauyawa, da kuma tsananin sha'awa ta mata daga sashin matasa 'yan birni, ke jefa su cikin abin da ya kira munmunan akida ta Shi'anci a kasar nan.

Sanannen Malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai dangane da arangamar da ta gudana tsakanin sojoji da 'yan Shi'a kwanakin baya, a gidanshi da ke Rigachikum, Kaduna.

Sheik Sambo Rigachikum ya kara da cewar babu wata shakka 'yan Shi'a sun kafirta ta fuskoki da dama, da hujjoji masu karfi a cikin Al kur'ani da Hadisai, amma su kan yi amfani da jahilcin kauyawa su tsunduma su ciki, sannan su yi amfani da sha'awar matasa 'yan Boko su yaudare su da Auren Mutu'a.
Babban Malamin ya kara da cewar, tuni tunda dadewa, shugaban majalisar Malamai na kungiyar Izala na farko, Sheik Isma'il Zakariyya Jos, ya bayyanawa gwamnati a wancan lokacin da cewar akidar Shi'a ta kutso kai a tarayyar Nijeriya, ya dace a yi wa tufkar hanci, amma abin takaici gwamnati ta yi biris da wannan magana sai ga shi yanzu abin ya girma har yana neman gagarar Kundila.

Sheik Rigachikum ya tabbatar da cewa Shi'a sun dade suna cin zarafi da keta alfarmar manyan mutane, amma aka kyale su suka yi ta cin karensu babu babbaka, saida a yanzu suka yi gigin taba shugaban dakarun sojin Nijeriya, da yake abin ya shafi gwamnati kai tsaye shine aka yi maganinsu, kuma da sun yi nasara Buratai ya koma da baya, to da shike nan sun ci Nijeriya da yaki kenan, gwamnatoci biyu a kasa.

Malamin ya kara da cewar abubuwa uku ba a yin gaba da gaba dasu, kuma dukkanin wanda yayi kasadar yin gaba dasu, to babu shakka zasu karyashi, na farko inji malamin shine yin fito na fito Allah, sai fito na fito da gwamnati, na karshe shine yin fito na fito da Bindiga, wanda kuma 'yan Shi'ah sunyi gaba da gaba da duka ukun.

Sheik Sambo Rigachikum ya kara da cewar, 'yan Shi'ah sunyi gaba da gaba da Allah, ta hanyar zagin manyan waliyansa, Sayyidina Abubakar, Umar, Usman da Uwayen muminai Aisha da Hafsah. Sannan sunyi fito na fito da gwamnati ta hanyar kin martaba dokokin kasa, sannan sunyi fito na fito da Bindiga ta hanyar kasadar tarewa Buratai hanya.

Babban malamin addinin, ya kuma soki lamirin kungiyoyi dake karyar kare hakkin 'yan Adam, inda yace menene yasa sukayi gum da bakunansu, lokacin da aka farmaki musulmai a filin sallar idi na garin Jos, aka hallaka dimbin jama'a, bayan wannan aka yanyankasu aka rinka gashi anaci kamar balangu, hakazalika Sheik Sani Yahaya Jingir na gabatar da tafsiri da Azumi, aka dira masallacin shi aka karkashe daruruwan mutane, sannan a masallacin kofar fadar Sarkin Kano aka dirarwa bayin Allah suna sallah aka jefa musu bama bamai, sannan aka tare kofar shiga akayi ta kisan jama'a ba kakkautawa, me yasa masu kare hakkin dan Adam ba suyi magana ba, saida aka kashe 'yan Shi'ah wadanda su suka jawo rigimar da kansu?

Sheik Sambo Rigachikum ya kuma kalubalanci kasar Farisa wato Iran, da su shiga taitayinsu dangane da katsalandan da suke yi wa Nijeriya akan batun kisan 'yan Shi'a, inda ya ce a kasar Iran 'yan Shi'a sun isa su tarewa shugaban rundunar dakarun sojin kasar hanya, sannan a kyale su? To ashe da akwai lauje cikin nadi kenan.
Batun: Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc