ARBA'UNA HADITH (4) HADISI NA HUDU
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=695

 
ARBA'UNA HADITH (4) HADISI NA HUDU

 An karbo daga abu Abdurrahaman Abdullahi dan Mas'ud (R.A) yace manzon Allah (S.A.W) ya bamu labari shi ne mai gaskiya cikin dukkan al'amuran da yake kuma abin gasgatawa yace lallai kowanne dayanku ana tara halittarsaa cikin mahaifiyarsa, tsawon kwana arba'in yana maniyyi sannan , ya canja ya zama gudan jinni kwatankwacin wannan sannan ya juya ya zama tsoka kwatankwacin wannan sannan, ya juya ya zama tsoka kwatankwain haka, sai a aiko mala'ika ya busa masa rai a umarce shi da rubuta kalmomi guda hudu: A rubuta arzikinsa da ajalinsa dad a ayyukansa da kuma dan wuta ne ko aljanna na rantse da wanda babu wani abin bautawa da gaskiya lallai dayanku zai yi aiki irin na 'yan Aljanna har ya zamanto baa bin da ke tsakaninsa da Aljanna sai zira'I daya sai rubutun can ya rigaya shi yayi aiki irin na 'yan wuta, sai ya shige ta lallai dayannku zai yi aiki irin na 'yan wuta har abin da ke tsakaninsa da ita bai zira'I daya ba sai littafi ya rigaye shi si yayi aiki irin aikin yan aljanna sai ya shige ta Bukhari ( 3208) Muslim (2643).

 SHARHI Abdullahi bin mas'ud (R.T.A) yana cikin sahabban farko da suka musulunta kuma suka yi hijira shi mutum ne wanda yake mai karamar halitta har wata rana yah au kan wata itaciya sai sahabbai suke dariya saboda gashi gajere ga kuma kwaurin Abdullahi dan Mas''ud keke yi dariya, na rantse da wanda ran Annabi Muhammadu (S.A.W) hannunsa kwaurin nasa guda biyu in an dora akan mizani sun karfin dutsen uhudu '' (Iman Ahmad ne rawaito shi ) shi mutum da Annabi (S.A.W) yace ''Karanta min Alqur'ani sai Abdullahi dan Mas'ud yace, ''Ai kai aka saukarwa '' sai yace, ni aka saukarwa amma ina so in ji daga bakin wanina karanta min in ji sai ya karanta masa suratun Nisa'I zuwa wajen fadin Allah s ﻓﻜﻴﻒ ﺍﺫ ﺟﻌﻨﺎ ﻣﻦ ﻛﻞ ﺃﻣﺔ ﺑﺸﻬﻴﺪ ﻭ ﺟﻌﻨﺎ ﺑﻚ ﻋﻠﻰ ﻫﺆ ﻻ ﺀ ﺷﻬﻴﺪﺍ )41 ). 

(yaya matsayin mutane zai zama idan muka zo da kowacce al'umma tare da mai mata shaida kai kuma zo da kai kana mai yin shaida kan wannan al'ummar Abin da ake nufi da cewa sai littafinsa ya yi rinjaye shi ne sai rubutun can da ka yi tun yana ciki sai ya rinjaye shi sai yazo yayi aikin da shi aka rubuta sai ya shi ga ciki masu iri wannan aikin abin wannan hadisin ke nunawa idan ka ganka a ayyukan da'a kana aiki na da'a ka roki allah dorewa har zuwa mutuwa akan wannan aikin don ba ka san karshen wannan ya sa Annabi (S.A.W) yake cewa ''Ya Allah mai jujjuya zukata! tabbatar da zuciyata akan addinnka (Tirmizi ya rawaito shi (2140) da Imam Ahmad, saboda haka kullum ka ganka ka a cikin alheri sai ka rinka yi wa kanka addu'a a cikin dare sannna kuma idan mutum ya yi aiki barna kar ya debe tsammani yace, to ai yanzu ni da nayi aikin barna iri kaza, watakila ko na tuba ba za'a karba ba Allah yace, ﻗﻞ ﻳﻌﺒﺎﺩﻯ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺍﺳﺮ ﻓﻮ ﻋﻠﻰ ﺍﻧﻔﺴﻬﻢ ﻻ ﺗﻘﻨﻄﻮ ﻣﻦ ﺭﺟﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻐﻔﺮ ﺍﻟﺬ ﻧﻮ ﺏ ﺟﻤﻴﻊ ﺍﻧﻪ ﻫﻮ ﺍﻟﻐﻔﻮﺭ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ )53 ( ﺍﻟﺰ ﻣﺮ :

Kace 'ya ku bayina wadanda suka yi wa kansu barna! Kada ku yanke kauna daga rahamar Allah hakika Allah yana gafarta zunubai gaba daya hakika shi (Allah) mai yawan gafara ne mai jin kai (Azzumar 53)
Don haka ba a so ka debe tsammani duk yawan zunubanka in ka tuba Allah zai gafarta maka zunubi na karshe shi ne shirka, amma idan mutum ya tuba Allah zia canza munanan ayyukanasa, su zamamto kyawawa wannan hadisin abin da yake nunawa kenan.

Wadansu kuma suka zo wajen Annabi (S.A.W) suka ce dashi in dai ya zamanto an rubuta komai tun mutum na ciki to me ya sa za a samu muyui aiki ? a kyale mu tsaya a kan rubutun da aka yi tun muna ciki mana!

Sai Annabi (S.A.W) yace '' Ku yi aiki kowanne da sannu za a karkatar da shi izuwa ga abin da aka rubuta shi akai'' {Duba Bukhari (6217) Muslim (2647)
saboda haka za ka kafa hujja ne da abin da Allah yace, ba abinda Allah ya rubuta ba, don abin day a rubuta ya Riga ya rubuta amma bai fada maka a inda ya rubuta ka ba? Amma a Alkur'ani mai girma yace, kayi sallah kayi zakka kayi imani ka kyautata w iyaye to sai kabi wannan umarnin na Alkur'an ma girma yace ''kayi sallah kayi zakka kayi imani ka kyautata wa iyaye to si ka bi wannan umarnin ka Al'kur'ani don shi ne tabbas don waccan rubutun ba ka san inda aka rubuta ba.

Haka nan wannan hadisi yana nuna matakan halittar dan Adan: matakin farko digon maniyyi, mataki na biyu ya zama dan Adam sai ya kai wata hudu sannna yake zama dan adam amma a wancan lokacin duk wadansu zango ne na daya da na biyu da na uku wanda ba a riga an busa rai ba shi yasa sa malaman fikihu suke bayani dangane da wanda yayi yunkurin da mace cikinta ko ya doke ta har cikinsa ya zube akwai wata hudu saboda in ba a kai wata hudu ba, bai riga ya zama rai ba in an kai wata hudu sya riga ya zama rai. Sai dai akwai hadisi a cikin sahihu Muslim (2645)
wanda yake nuna a cikin halittar dan Adam to yaya umartar mala'ikan ya sawwara halittar dan Adam. To yaya za ayi a hada su?

sai wadansu suke ce ai can taswira akace, babu busa rai taswira daban, busa rai daban A wadansu ayoyin sai aka nuna matakai guda bakwai ake bi wasu kuma suna nuna guda biya r a karshe zaka ga sun kai guda bakwai Allahi yace, ﻭ ﻟﻘﺪ ﺧﻠﻘﻨﺎ ﺍﻻ ﻧﺴﻦ ﻣﻦ ﺳﻠﻠﺔ ﻣﻦ ﻃﻴﻦ )12 ( ﺛﻢ ﺟﻌﻠﻦ ﻧﻄﻔﺔ ﻓﻰ ﻗﺮﺍﺭ ﻣﻜﻴﻦ )13 ( ﺛﻢ ﺧﻠﻘﻨﺎ ﻋﻠﻘﺔ ﻓﺨﻠﻘﻨﺎ ﺍﻟﻌﻠﻘﺔ ﻣﻀﻐﺔ ﻋﻈﻤﺎ ﻓﻜﺴﻮﻧﺎ ﺍﻟﻌﻈﻢ ﻟﺤﻤﺎ ﺛﻢ ﺍﻧﺸﺄ ﻧﻪ ﺀﺍ ﺧﺮ ﻓﺘﺒﺮﻙ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﺣﺴﻦ ﺍﻟﺨﻠﻘﻨﻲ ) 14 ( ﺍﻟﻢ ﻣﻨﻮ 13- 12 :

(Hakika mun halicci mutum daga tsantsar tabo sanna muka sanya shi digon maniyyi a cikin wata matabbata amintacciya. Sai muka kashi sannan muka lullube kashin da nama, sannan muka samara da shi a wata halitta dabam. Albarkar Allah wanda ya fi kowa iya halitta ta yawaita ) Amu'uminun: 12-14 Wannan hadisi ya kawo guda hudu ashe sai ka dauki nan ka dauki can, sannan ka hada dan Adam gaba daya. In ka dauki wuri daya sannan ka hada dan Adam gaba daya in ka dauki wuri daya ba zaka iya hadaba
Batun: Al'Adun Musulmi Da Darajoji