ARBA'UNA HADIT (5) HADISI NA BIYAR
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=696

 
ARBA'UNA HADIT (5) HADISI NA BIYAR

An karbo daga Ummul Mu'uminina Ummu Abdullahi Aishatu (R.A) tace manzon Allah (SAW) ''yace wanda ya kirkiro wani abu cikin lamarinmu wannan abin da baya cikinsa to a mayar masa da kayansa.'' Bukhari ( 2695) Muslim (1718) Aruwayar Muslim Wanda duk ya aikata wani aiki daba umarninmu a kai an mayar masa da shi.

SHARHI Aisha daya ce daga cikin matan Annabi (S.A.W) ta samu falalar kasanecwar matar Annabi (S.A.W) duk cikin matan Annabi (S.A.W) Annabi yafi kaunar ta sama da kowa don an tambayi Annabi (S.A.W) waka fi so ?

yace, Aisha, Aka ce '' aciki maza fa ? yace Babanta Abubakar (Bukhari ( 3662) Amma duk da Annabi (S.A.W) ya fi son Aisha baya zaluntar sauran matansa saboda ita A hannunta Annabi(S.A.W) ya cika ya bar duniya tace, '' Allah ya karbi ran Annabi (S.A.W) a lokacin ina tallafe da shi a tsakanin cinyoyina da kirjina kuma aka binne shi a dakinta ( Duba Bukhari (1389) da Muslim ( 2443) domin bayan rasuwarsa aka ce ina za akai shi wadansu sukace a kai shi masallaci wadansu suka ce ''A kaishi baki'a wadansu sukace '' akaishi wuri kaza sai sayyadina Abubakar yace '' Annabi (S.A.W)
ya fada cewa babu wani Annabi da ya taba mutuwa face sai an binne shi a in da Allah ya karbi ransa 1. [ Duba Al'musnad na abu Ya'ala (22)] ba daukar sa a akai shi wani wuri don haka sai aka binne shi a dakin Aisha wannnan falala ce ! don da ma Imamu Malik ya rawaito a cikin Muwadda cewa Aisha ta yi mafarkin taurari guda uku sun fada sai aka wayi gari sai ta tambayi abubakar sai yayi shiru ya kyale ta bai ce mata komai ba. 
Annabi (S.A.W) ya bar duniya aka binne shi a dakinta sai yace to wannan daya daga cikin taurarin kenan biyun suna tafe (Duba`Muwadda-Babu Ma ja'a fi dafnil mayyit) sai sayyadina Abubakar kuma ya bar duniya shi ma sai aka binne shi a dakinta kusa da kabari Annabi (S.A.W) Aisha tace, so nake in mutu a binne ni a a wajen '' sai kawai Umar dan khaddab ya nemi Alfarma wajen Aisha cewa in ya riga ta mutuwa yana so a binne shi a kusa da Abubakar ta amince in ya riga ta a sashi sai Umar ya riga ta mutuwa ''Wannan mafarki ya tabbata.

Ana ce mata Ummu Abdullahi ba don ta taba haihuwa ba, sai dai kawai ya yarta mai suna Asma'u bintu Abubakar, tana da da Abdullahi dan gidan Zubair bin Auwam, daya daga cikin Mutum goma da aka yi musu Albishir da Aljanna to wannan Abdullahi dan Zubair bin Auwam din, shi ne Annabi (S.A.W) yake jingina wa Aisha yace mata ummu Abdullahi. Kuma daga wannan ne Malamai suka ce ya halattar mutum yayi alkunya ko da bashi dada.

Lafazin ''lamarinmu'' Da yazo a wannan hadisi yana nufin Musulunci ma'ana wanda ya kirkiro wani abu a cikin addininmu na musulunci abin da baya cikin musulunci (Duba Jami'ul Ulum wal-hikam na Ibnu Rajab 1/63)
Wannan hadisi shi ne kashin bayan rusa dukkan bidi'a a akan kasa duk abin da yake bidi'a ne wannan hadisi ya rusa shi abin da duk mutum ya gina a kan bidi'a, Allah ba zai ba shi lada ba, don ma ba zai karba ba.

Akwai wasu wadanda za su zo wajen maganar bidi'a sai su ce to ai idan kace bidi'a a kamar ka ce kar mu hau keke kar mu hau babur kar muyi amfani da dukkan wani abu kirkirarre don wadannan abubuwan bidi'a ne, don lokacin Annabi (S.A.W) babu su. Sai ka ce da shi, wadannan al'umura da ka zana. Ba addinin ba ne su.

Wani abu ne na bukatar rayuwa. Annabi (S.A.W) kuwa ya rasu duk abin da an kirkire shi ne sunansa addini, y ace ''Wanda ya kirkiro cikin wannan.....'' Lafazin wannan kuwa daya zo a nan, nuni ne zuwa Musulunci. Babu wanda zai ce idan nahau babur daga nan wurin na tafi Damaturu, ladana bai kai na wanda ya hau mota ba; wanda yahau mota gingimari ta katako, ladansa bai kai wanda ya haubambalasta ba. Babu wanda zai fadi haka, duk bidi'a da ta shafi lamarin duniya, kirkira kenan. A duniyance ka kirkiro mota, ka kirkiro kwamfuta da dukkan abin da zai taimaka wa rayuwa ta ci gaba, wannan shari'a ba ta hana ka ba, amma kirkira ta fuskar addinin, ka kara ko ka rage, ka kawo wani zikiri, ko wata falala, ko wata sallah, ko wani sallo na istigfari, to wannan shari'a ta rushe. Ya tabbata a sahihi Muslim (#2363), Annabi (S.A.W) an tambaye shi cewa, ga wasu mutane suna yin kilili. Shi ne su dauki dabino idan ya yi huda, su tsaga su dauko irin nan. Su sa a nan, don ya ba da mai kyau.

Sai Annabi (S.A.W) yace, ''Wannan ba zai yi amfani ba.'' Sai sahabbai suka ce, ''Ai mun sha yi, kuma yana amfani.'' Sai Annabi (S.A.W) ya ce ''Ku kuka fi ni sanin lamarin duniya, ku je ku yi kayanku.'' Saboda wannan ba hailala bane, ba istigfari bane, don haka baya jiran sai Annabi (S.A.W) ya bayar da umarni kafin su je su yi. Domin duk abin da yake gwaji ya tabbatar, idan aka hada sinadari kaza da kaza zai bayar da kaza, wannan a duniyarka ka je ka yi ta kirkire-kirkirenka, ba a hana ka ba. Amma a cikin lamarin addini dole, ka bi fadin Allah.

( ﻭﻣﺎ ﺀﺍﺗﻜﻢ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﻓﺨﺬﻭﻩ ﻭﻣﺎﻧﻬﻜﻢ ﻋﻪ ﻓﺎﻧﺘﻬﻢ ﻭﺍﺗﻘﻮﺍ ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺷﺪﻳﺪ ﺍﻟﻌﻘﺎﺏ ( )7 ( )ﺍﻟﺤﺸﺮ7 : ).


(Duk abin da Mazon Allah ya zo muku dashi ku karbe shi, abin daya hana ku, ku hanu.

Lallai Allah mai tsananin ukuba be.) {Al- Hashr: 7} Kuma babu wata bidi'a mai suna kyakykyawa, dukkan bidi'a batace, kar ka taba zaton akwai wata bidi'a sunanta Mustahibbiya ko bidi'a hasana. Wannan duk rabe-raben, wanda ya fara kawo shi a cikin duniyar ilimi, shi ne izzuddeen bin Abdussalam, wanda ake kira Suldanil Ulama a cikin littafinsa Kawa'idul Ahkam Fi Masalihul Anam, kuma shi dan mazahabar Shafi'iyya ne, daga wurinsa Imamul karafi, daya daga cikin malaman Malikiyya ya dauko wannan, ya rubuta cikin littafinsa. To tunda yake shi dan Malikiyya ne. Shehu Usman Dan Fodiyo shi kuma ya dauko daga cikin littafin Imamul Karafi ya sa a nasa. Abu Ishak Assahadibi ya yi ragaraga da wannan abun (cikin littafinsa Al-I'itisan), kuma shi ma dan Malikiyya ne, y ace babu wata bidi'a mai suna hasana, wannan kullu Ala Babiha.
Batun: Al'Adun Musulmi Da Darajoji