ARBA'UNA HADITH (6) HADISI NA SHIDA
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=697

 
ARBA'UNA HADITH (6) HADISI NA SHIDA

An karbo daga abu Abdullahi Nu'umanu dan Bashir, (R.A) y ace ''Na ji Manzon Allah (S.A.W) yana cewa, ''Lallai halal a bayyane take, kuma lallai haramun a bayyane take, amma a tsakaninsu akwai al'amura masu rikitarwa, da yawa daga cikin mutane ba su san sub a. Duk wanda ya nisanci abubuwa masu rikitarwa, hakika ya nemi kubutar da addininsa da mutuncinsa. Wanda ya auka cikin abubuwa masu rikitarwa, to ta auka cikin haram. Kamar makiyayi ne da yake kiwo a gefen shinge, ya kusanta ya shiga (Ya yi kiwo) a cikinsa. Ku saurara! Kowane sarki yana da iyaka. Ku saurara! Iyakar Ubangiji it ace abubuwan day a haramta. Ku saurara! Lallai a cikin jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru, dukkan jiki ya gyaru, idan ta lalace, dukkan jiki ya lalace. Ku saurara!

(Wannan tsokar daya) it ace zuciya.'' Bukhari (#59) da Muslim.

SHARHI Ma'ana, halal a bayyane yake a cikin Alkur'ani da hadisai tabbatattu daga Annabi (S.A.W), haka kuma haramun a bayyane take a cikin Alkur'ani da hadisai tabbatattu daga Annabi (S.A.W), amma a tsakanin halal da haram, akwai wadansu al'amura masu rikitarwa; su ba su da sifa ta halal tsantsa, ballantana mu sa su a layin halal, bas u da siffa ta haram tsanrsa, ballantana mu sa su a layin haram. Don haka sai suka zamanto masu kama da juna, ko masu rikitarwa, ta yadda ba ka san ajin da za ka ajiye su ba.
Wadannan abubuwa masu rikitarwa, da yawa daga cikin mutane ba su san su bu, ba su san hukuncinsu ba. Wannan yana nuna akwai wadansu kadan cikin munate sun san su, su ne malamai tabbattu a cikin ilimi, su bas u da rikici a cikin abin, da sun ga su kasa gane wane ayi ya kamata su ba su. {Duba; Jami'ul Ulum wal Hikam Na Ibnu Rajab 1/181}.

A nan wurin abin da malamai suke cewa shi ne, akwai abubuwan da dama da asalinsu ana daukar su a halal ne, ba ka da dammar ka cire su daga halacci, said a nassi, akwai kuma abubuwan da ake daukar su a matsayin haramci, ba ka da dammar ka cire su daga haramci, sai da nassi, kamar misalign duk wani dangin abinci wanda zai karbi sunan addayyib, wanda kuma bincike ya nuna ba ya cutar da tunani, ba ya gurbata masa tunani, to wannan abin halal ne . idan ka bad a fatawa a kan halaccinsa, ba a abin ka bashin dalili, duk wanda ya bi ka bashin dalili, bai san abin da yake ba.

Amma in wani ya zo ya yi da'awar haramci kana abin da yake yana cikin Addayyibat, to wanda ya yi da'awar haramcin, shi ne za'a ce ina dalilinsa? Saboda haka, asali dangane da abinci ko abin sha, matukar ya zama baya cutar da jiki, ko hankali to ya zama dayyib, shi kuma halal ne, Allah ya ce:

( ﻗﻞ ﺃﺣﻞ ﻟﻜﻢ ﺍﻟﻄﻴﺒﺖ ( )ﺍﻟﻤﺎﺋﺪﺓ4 : )

(Ka ce an halatta muku dukkan dangin abinci ko abin sha wanda yake daddada)

Asali kuma cikin dukkan abinci ko abin shha wanda zai cutar da hankali, ko zai cutar da lakar jiki, yana shiga cikin babin haramun, idan ka ba fatawa da haramcinsa, ba ka neman dalilin da zai karfafa maka fatawarka. Sai dai zai iya yiwuwa ka samu wani abu dab a ya cutarwa a jiki ko a hankali, amma duk da haka haram ne, saboda da mallakarka ne, sato shi ka yi, ko kwato shi ka yi. To a nan wurin sai ya zama ya tashi daga suna halal, ya zama haram.

Wadannan al'amura masu rikitarwa, malamai sun yi maganganu a kansu; wandansu suka ce kamar a sami wani abu wanda nassi guda biyu suka zo a kansa, daya nassi yana nuna hallacinsa, daya nassi yana nuna haramcinsa, kuma mun kasa tantance wane nassi ne ya riga zuwa, ballantana mu ce nassin karshe ya shafe na farko. Wato an sami Annasikh Wal Mansukh!

To wannan yana cikin al'amura masu rikitarwa, in mun vce halal ne ga, wani nassin can ya ce haramun ne, in mun ce haramun ne, ga wani nassin can ya ce halal ne, (Don Karin bayani duba: Jami'ul Ulum Wal-Hikam Na Ibnu Rajab 1/183). Amma idan ka je wajen malamai masu zurfin ilimi sai su ce, wannan nassi na farko day a bad a hallaci, nassi ne na Makka, wancan nassin dayan da ya bad a haramci, nassi ne na Madina, na Madina ya shafe na Makka, don haka ya zama haramun.

Wadansu suka ce, ''..... Al'amura masu rikitarwa....'' da aka ambata a wannan hadisin, sun kunshi sabon abu da zai faru wanda bai taba faruwa ba loakcin Annabi (S.A.W) a yanzu kuma sai muka kasa sanin a ina za mu ajiye shi. Ya yi kama da halal, ya yi kama da haram, kuma mun kasa sanin a ina za mu ajiye shi? To irin wadannan sun e, ''...... al'amura masu rikitarwa.....'', kuma suna bukatar malamai masu zurfin ilimi, masana game da nassosin shari'a, masana game da abin da ke faruwa a duniya yau, a zamanin yau, sai su hada nassosin shari'a da sabbabin abubuwan da ke faruwa don a san wane irin hukuncin ya kamata a ba su.

Fadin Manzon Allah (S.A.W) cewa ''..... Duk wanda ya smnisanci abubuwa masu rikitarwa, to hakika ya nemi bukatar da addininsa da mutuncinsa.....'' Yana nuna kai musulmi, yayin da duk ka ga wani abu wanda ba ka iya tantance halacci ko haramcinsa ba, ya rikitar da kai, to a nan tsira da addinka, tsira da muntuncinka, shi ne ka bar wannan abin. Yayin da duk abu ya rikitar da kai, sai ka guje shi daga daya don ka kubuta da addininka. Misali kai ne kake da wani samfuri na takalmi, sai ka zo kashiga masallaci, da ka fito, sai ka nemi takalminka ka rasa, can sai ka hangi wani takalmi inda ba ana ka ajeye naka ba, da nisa daga inda ka ajiye naka, amma da ka je sai ka gan shi kamfani daya, kira daya, kila har sabunta iri daya da naka, sai da in da mastambayi zai tambaye ka, shin kana da tabbas wannan takalminka ne? Za ka iya rantsewa kan takalaminka ne, Za ka ce Eh!

Irinsu dai daya da nawa, amma ba zan iya ba ka tabas cewa nawa ne ba.'' To wannan ya shiga cikin ''..... Al'amuran masu rikitarwa....'' idan kana da tabbas din naka da yakinin wannan, to dama-dama ka iya dauka ka rike kafin ka je ka yi bincike, amma in ba ka da wannan yakini, ba ka da wannan t abbas din, zato ne kake da shi, ba za ka gina hukunci kan zato ba.

Na biyu suka ce, kamar yara ne guda biyu 'yan tagwaye mata, aka haife su a gida daya, daya daha cikin yaran matan, kun yi tarayya da ita wajen shan mama. Ma'ana mace daya ta shayar da ku, kai da ita. Ka gay a Zama tabbas wannan ta zama haram, ba za aure tab a, saboda an shayar da ku. Sai aka maid a ita gidansu bayan an yaye ta, ta girma tare da 'yar uwarta wacce aka shayar da su ita a wani gida na daban. Da suka girma, sai ka ga daya daga cikinsu kana so, amma da aka zo bincike sai aka kasa gane wacce ce kuka sha nono tare da ita, wacce ce baku sha tare da ita ba, tunda gashi Hassana da Hussaina ne gida daya suka taso, wacce aka samu tabbas baku sha tare da ita ba, ya halatta ka aure ta,wacce aka samu tabbas in kun sha mama tare da ita, bai halatta ba ka aure ta yanzu kuma ba ka da tabbacin da zaka tantance wannan. Abin day a kamata kayi sai ka bar su duka biyun kaje wani gidan ka yi aure, wannan shi ne zai tabbatar da ka kubutar da addininka ka kubutar da mutuncinka ba ka fada cikin abin da Allah ya haramta maka ba.

Shi kuwa fadin manzon allah (S.A.W) cewa '' Wanda ya auka cikin abubuwa masu rikitarwa to ya auka cikin haram '' shi ne malamai suke cewa duk abin day a rikitar da kai ka kasa gane halaccin ko haramci to nisantarsa shi ne addini ka nisance abin aba daya don ka huta wa kanka don idan ka afka ciki mai yiwuwa ka iya afkawa cikin harama ba tare da kasani ba kama makiyayi ne da yake kiwo a gefen shinge wato iyaka duk makiyayain da yazo dabarsa na cin ciyawar da ke kan iyaka, to za ta shiga cikin gona ne kai tsaye, to tun asali da ta je iyaka sai kahana duk abid da yake kusa da haram mafi kyau ka nisasce shi saboda kusantarsa shi ne zai iya aukar da kai cikin haramun gaba daya tsundum.

A gaba sai manzon Allah (S.A.W) yace lallai kowanne sarki yana da iyaka '' ta ikonsa yana da iyakar kasarsa iyakar da Ubangiji ya dora bay a son a ketare ta shi ne abubuwan day a haramata Ma'ana yadda ka san sarki ba zai so ka shigo kasarsa ba to haka ubangiji Ta'ala ba yason ka ketare abin day a haramata maka: abinda duk ya haramta mafi kyau ka nisanec shi, kar ka kusanci inda yake dukkan abin da yake mai rikitarwa to ana son mutum ya nisance shi saboda tabbatar da kariyar mutuncinsa shi yasa wata rana Annabi (S.A.W) yana I'itikafi a masallaci sai matarsa safiyya ta kawo masa ziyara bayan ta dade tana hira da annabi (S.A.W) sai ta tashi cikin duhun dare zata tafi, sai Annabi(S.A.W) yace muje in raka ki zuwa kofar Masallaci ''ya raka ta har wajen Masallaci sai ga wadansu mutane guda biyu daga nesa sun gane Annabi ne Amma basu san wacece wadda Annabi (S.A.W) yake tare da ita ba, sun dai ganshi da wata mace. Da suka ga haka, sai suka ja baya zasu tafi sai Annabi (S.A.W) yace ku tsaya inda kuke ! suka tsaya ya kama hannun matarsa, suka je yace matata sai sai sukace, ''Ya Annabin Allah ! me ya kawo haka ? ai ba zamu munana zato gare ka ba.

''sai yace ''A/ a shaidanna gudana cikin jikin 'dan adam duk inda jinni yake zirga-zirga shaidan yana shiga, sai naji tsoran kada ya jefa muku wani sharri a cikin zuciyarku (Duba Bukhari 2035) da muslim ( 2174)
kaga wannan shubuha ce ta faru, don wani na iya zuwa yace ya ganshi da wance, sai ya yi maza yak are kansa, ya nuna cewa matarsa ce.

Haka kuma anas dan Malik za shi masallacin juma'a ashe ya makara bai sani ba yana fitowa ya kusa zuwa masallaci asi yaga ana dawowa an gama sallah a masallaci a matsayinsa kuma idan wadansu mutane sun ganshi zasu ce kaga ma ko juma'a ba zuwa sai ya ruga a guje ya sami lungu ya buya don kar ya tsaya a inda za ganshi wurin tuhuma, ace gashi ma yanzu yake zuwa masallaci yanzu yazo kila baya son yabi limamin ne kila kaza ne kila kaza ne, don yak ore wa kansa wannan tuhumar sai ya buya bai fito fili ba sun ganshi ba.

Faadin manzon Allah (S.A.W) cewa lallai a cikin jiki a kwai wata tsoka, idan ta gyaru jikan jiki ya gyaru idan ta lalace dukkan jiki y abaci ku saurara, (wannan tsokar daya )
itace zuciya yana nufin baa bin da ke sa shiga aljanna sai gyaruwar zuciya ba gyaruwar jiki ba, ba ba abin da ke sa a shiga wuta sai lalacewar zuciya ba lalacewar gangar jiki ba.ka rasa hannuko wannan baa bin da zai kawo maka cikas wajen shiga Aljanna ban e kuma ranar Alkiyama duk sai amn mayar ma da gabbanka kamar yadda suke lafyayyu ko gurgu sai an tayar da kafarsa ta mike, saboda zuciyarsa ta rayu da imani sai a gyara jikinsa gaba daya. Amma kana da dafin zuciya, shirka ta mamaye zuciyarka ta ko'ina ga lafiyar gabbai wannan baa bin da zai hana mutum shiga wuta shi yasa Allahyace, ﻳﻮﻡ ﻻ ﻳﻨﻔﻊ ﻣﺎﻝ ﻭﻻ ﺑﻨﻮﻥ )88 ( ﺍﻻ ﻣﻦ ﺍﺗﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻘﻠﺐ ﺳﻠﻴﻢ )89 ( ﺍﻟﺸﻌﺮﺍﺀ :

Ranar da dukiya da 'yaya bas a amfani sai wanda yaje wa Allah da zuciya lafiyayya)

Asshu-ara: 88-89)

Anan Allah (S.W.A) bai ce ''Sai wanda yazo da jiki lafiyye ba, cewa yayi '' Sai wanda yazo da zuciya lafiyya. ''warkakkiya, wankakkiyar zuciya, tabbas babu hassada ba ganin kyashi to dangane da gyaruwar zuciya ba abinda zai gyara ta, si abin da Allah ya saukar na wahyi sai sunnonin Annabi (S.A.W) kullum kayi kokarin raya zuciyarka da Alkur'ani mai girma, kayi kokarin raya zuciyarka sauraron hadisin Annabi (S.A.W).
Batun: Al'Adun Musulmi Da Darajoji