ARBA'UNA HADITH (9) HADISI NA TARA
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=700

 
ARBA'UNA HADITH (9) HADISI NA TARA

An karbo daga Abu Hurair Abdur-rahman dan Sakhirin (R, A) yace, naji manzon Allah (S.A.W) yana cewa duk abin dana hane ku (da bari) to ku nisance shi abin da na umarce ku ku zo dashi (wannan abin ) gwargwadon iko abin daya hallakar da wadanada suke kafi ku yawan tambayoyinsu da sabawarsu ga Annabawansu (Bukhari 7288) da Muslim 1337).

SHARHI Wannan hadisin an karbo shi daga Abu huraira limamin masu hadisi cikin sahabban Annabi (S.A.W) sunansa ne Abdur'rahman bi sakhirinn Addausiy.

Malamai sun sabani wajen sunansa, amma wannan shi ne mafi inganci ya musulunta a shekarata bakwai bayan hijirar Annabi (S.A.W) amma tare da haka, ya haddace hadisai masu dimbin yawa cikin hadisin annabi (S.A.W) Abu huraira yace '' da yazo madina (da ma bad an madina bane )
Sahabbai wadansu suna gonakinsu suna noma wadansu suna tafiya kasuwa yace : ni kuwa abin da nake bukata in sami abin d azan ci kawai in na sami abin d azan ci a wannan yinin si in zo in zauna a wurin Annabi (S.A.W) ban a rabuwa da shi duk abin day a fada ina rike'' har wata rana Annabi (S.A.W) yasa ya shimfida mayafinsa day a shimfida mayafinsa Annabi(S.A.W)
yace daga yai din na duk abin da kaji daga bakina ka haddace shi ken an dauki mayafinka ka tafi ya dauki mayafinsa ya yafa a jikinsa tun daga ran nan yace, duk abin day a fito daga bakin Annabi (S.A.W) na haddace shi (duba bukhari 118 ) da muslim 2492) shi Abu Huraira ba ya noma baya kasuwanci yace yana nan duk abin da Annabi (S.A.W) ya fada ya rike ba don komai ba si don saboda ya sanar da Al'umma wannan abin yace, sau da dama mutum zai fito daga masallaci, sai in bishi ina tambayarsa fassarar wata aya in bishi ina tambayar sa wani hadisi ba wai don ban sna aya ko hadisin ba, kila ma naïf shisani ammadon saboda ko yayi mi tayi yace, zo muje gidana mu ci abinci shi dai ba zai ce masa in zo gidanka in ci abinci ba (duba bukhari 6452)
Dangane da fadin manzon Allah (S.A.W)

cewa ,duk abinda na hane ku (da bari) to ku nisance shi wannan da ma duk abin da shari'a tayi umarni iri biyu ne ko abin da yake umarni ne k abin da yakie hani ne tosai dai malamai sukace aikata abinda aka hana yafi girman laifi sama da kayi sakaci aikata abin da aka yi umarni sukace hani da sassauci tunda Annabi (S.A.W) yace duk abin da na hane ku ku nisance shi ba ma ku nisanci wurin abin ba .amma a wajen umarni si yace to kuzo da wannan abin gwargwadon iko duba Jami'ul walhikam na ibnu Rajab 1/246 Asalin sallah kayi a tsaye idan baka da lafiya sai kayi a zaune ya halatta in rashin lafiar yayi tsanani sai a kwance zaka iya yi sai kayi kwancen ya halatta. A salin sallah shine ka fiskanci Alkibla amma sai kazo bakunta wani garin da nbaka san alkibla ba kuma baka samu wanda zaka tambaya ba, to duk inda ka ga dama kayi sallah ya halatta ko da yake akwai malamai da suke cewa kayi sallah hudu ka kalli nan ka kallai nan. Sai dai a nan, an tsananta da yawa! Abin da shari'a ta wajabta maka, shi ne ina ne inda ka nutsu cikin zuciyarka cewa nan ne alkibla ko da nan bane, kayi sallah ta wadatar ba si kayi sallah hudu ba haka nan lokacin sallah ya kusa fita, saura kadan ba kasami ruwa ba ko ruwan wanka ba kasami kasar da zaka yi taimama sai kayi sallah a haka, kada kace sai kaje neman ruwan har lokacci sallah ya fita ba kayi ba. Wannan kurkure ne Allah yana cewa ﺍﻥ ﺍﻟﺼﻠﻮﺓ ﻛﻨﺖ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﻮ ﻣﻨﻴﻦ ﻛﺘﺒﺎ ﻣﻮ ﻗﻮ ﺗﺎ )103 ( ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ:

(Hakika salllah ta kasane akan mumiminai farillam mai kayayyadan lokaci ) Annisa'I 103)

Da manzon allah (S.A.W) yace Abin da ya halakar da wanda suke kafin ku yawan tambayoyisu tambaya nan akwai wacce ta haltatta akwai wacce kake son fahimta wani abu na hukuncin shari'a musulumci wanda ka jahilce shi irin wannan tambayar wajibi ne kayi ta Allah yace, Ku tambayi ma'abota sani in baku sani ba)
(Al-anbiya 7)

In baka san abu ba, wajibi ne ka tambaya kafin ka aikata shi amma irin tabmayar da mutanene makkah suke yi wa Annabi (S.A.W) su tambayeshi abin d suka san ba zai iya sani bas u cew sai ya yi kamar yadda suka rika fada aya ta 90 cikin suratul Isra'I ﻭ ﻗﺎﻟﻮ ﻟﻦ ﻧﻮ ﻣﻦ ﻟﻠﻚ ﺣﺘﻰ ﻧﻔﺠﺮ ﻟﻨﺎ ﻣﻦ ﺍﻻ ﺭﺽ ﻳﻨﺒﻮ ﻋﺎ ) 90 ( ﺍﻻ ﺳﺮﺍﺀ 90 (suka cew ba zamu yi imani dakai ba har sia ka bubbugo mana da idaniyar ruwa daga sama ) (Isra'I )

Kaji abin da suka gindaya wai sai anfitar musu da maremarin ruwa daga sama a cikinta da kuma korama a cikin sahara inda ba a tsammann ganin ruwa ko kuma ya kasance ka rufto mana da sama kamar yadda kake fada: ko ka kasance kana da gida na koma zinare da azurfa bulo din da simintin da fentin da komai da komai na zinare ko kawai mug a na turo maka da wata matattakala, ka tatttaka kana hawa sama. Sukace, ko dam un ga kana tattakawa wa din nan fa ba zamuyi imani da hawan da kayi sama ba, har sai ka sauko da wani littafi ka bamu muna karantawa mun ga an cew kai manzo ne zuwa gare mu to irin wannan tambayar ita manzon Allah (S.A.W) yake nufi dayace, abin day a halakar da wadanda suke kafin ku shi ne yawan tambayoyinsu in kaji an zargitambaya a cikin nassin Alkur'ani ko nassin hadisi to irin wannan tambaya ake zargi, don ba tambaya ce ta neman fahimnta ba. Haka kuma yana cikin tambayar da malamai ke zargi shi ne al'amura da suka faru a baya wanda bayaninsu bai zo ba ko a bayaninsu dalla-dalla kamar alkaluman d aka yi takara lokain da aka kawo maryam wajen daliban zakariyya kan cewa waye zai riketa to si wani yazo ya tamnaye ka, wannan alkaluman na meye ? dan kara akayi su ?

karan gero ko dawa? Ko gamba ? ko menene farare ko bakake ne ? yanzu in ka san wannan, me zai kara maka kuma in ka jahilci wannan cewa lokacin da fir'auna yabi annabi mus da runduna dubu nawa ya tafi da ita? Sannan wane irin sirdi ya dora wa dokinsa ? sannan dokin baki ne ko fari ne jamne ko wamkan tarwada me zaka karu a cikin wannan in an sanar da kai, kuma me zakayi asara in ka jahilci wannan ?

Yana daga cikin tambayoyin dab a a so kayi tambaya akan abin da bai riga ya faru ba Haka kawai ka kirkiro in da abu kaza zai faru menene hukuncinsa wadananan tambayoyi Manzon Allah (S.A.W) yace, su suka halakar da wadanda suke gabaninmu.
Batun: Al'Adun Musulmi Da Darajoji