ARBA'UNA HADITH (10) HADISI NA GOMA
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=701

 
ARBA'UNA HADITH (10) HADISI NA GOMA

 An karbo daga Abu hurairata (R.A) yace, manzon Allah (S.A.W) yace, lallai Allah tsarkakke ne kuma baya karbar abu, sai tsarkakke, Allah ya umarci muminai da irin abin daya umarci manzanni da shi yace, yaku manzanni ku ci daga dadddan abubuwan kuma yi aiki nagari kuma (Allah)
 yafada lokacin da yake umartar muminai yaku wadanda suka yi imani ku ci daga dadadan abububawan da muka azurta ku da shi sannan Annabi (S.A.W) ya ambaci wani mutum da yake tsawaita tafiya gashin kansa yayi gizo yayi kura yana mika hannayensa zuwa sama yana cewa ya rabbi ya rabbi amma kuma abincinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, tufafinsa haramun ne an ciyar dashi haram tayaya za amsa masa (Addu'arsa) Muslim (1015).

 SHARHI; Abin da ake nufi da ''Allah ta'ala tsarkakakke ne shi nekamiline shi cikin siffofinsa babu tawaya ko nakasa tare dashi dukkan wani dangi n a tawaya Allah ya siffanta da wannan dukkan siffar dake nuna kamala, to Allah ya siffanta da wannan dukkani siffar dake nuna kamala to Allah shi k da mafi cikar wannna siffar: ilmi kamala ne to Allah shi yafi kowa ilmi karfi kamala ne to Allah yafi kowa karfi adalci kamala ne to Allah shi yafi kowa adalci a bayan kasa.

 Dangane da fadin manzon Allah (S.A.W) cewa kuma bay a karbar abu sai tsarkakke idan ance aiki tsarkakke to ana nufin abin day a cik sharudda wadanda shari'a ta gindaya a kansa, aikin da aka dora da Alku'rani da hadisi dangane da tabbatuwarsa.

Dangane kuwa da fadinsa cea ''Allah ya umarci muminai da irin abin day a umarci manzanni dashi a nan wurin kaga Allah yace wa manzanni kuci daga dadadan abubuwa da muka azurta ku dashi irin abin da Allah ya kallawa Manzanni yace lallai su yi haka ya dora wa bayinsa muminai wannan yana nuna mana dukkan abin da mutum zai Allah ya karba to ya zamanto wannan abin tsarkakke ne ,halattace ne, ya cika sharuddan da shari'a take bukata kowace irin ibada sai ta cika sharuddan da shari'a take bukata idan ibadaza a yi tad a dukiya to ya zamanto dukiyar da akayi wannan ibada za a yi ta zamto ta halal ba dukiya ce da akasame ta ta hanyar magudi ba in zaka yi masallaci, in zaka yi makaranta in zaka je hajji ko umara ko zaka biya wa wani yaje, to ya zamanto dukiya ce ta halal da guminka aka yi aka bar ta a gidanku sai a sarrafata, wannan tasarrafin to wannan ya halatta kuma kana da lada a kai amma in ta kasancew ta magudi ko haram ce ko ta kwace ko ta sata ko ta sama da fadi ka same ta to ko ka bayar da kujera dari ko miliyan ba ka da lada a wajen Allah ko ka dauki kudinsata kaje hajji ko kaje umara, ba zaa karba maka ba domin Allah tsarkakekke neb a ya kuma karbar abu sai tsarkakekke saboda haka wajibi ne bayar da dukiya ta halal. Haka kuma, ta siya yiyuwa abin naka na halal ne, sai dai bay a da nagarta, sai ka dauka ka bayar sadaka, to Allah bay a son irin wannan sadakar. Kamar abinci ya lalace, sai ka dauka ka bayar sakada, ko ka taskance shinkafa ko masara ko gero a store, har ya fara lalacewa, ta yadda ko ka kai shi kasuwa ba zai yi kima ba, ba zai yi daraja ba, wannan Allah ba zai saurare ka ba, saboda Allah Ta'ala mai tsarki ne, kuma bay a karbar aiki sai mai tsarki. Kuma Allah yana cewa, (ﻳﺄﻳﻬﺎ ﺍﻟﻠﺬﻳﻦ ﺀﺍﻣﻨﻮﺍ ﺃﻧﻔﻘﻮ ﻣﻦ ﻃﻴﺒﺂﺕ ﻣﺎ ﻛﺴﺒﺘﻢ ﻭﻣﻤﺎ ﺃﺧﺮﺟﻨﺎ ﻟﻜﻢ ﻣﻦ ﺍﻷﺭﺽ ﻭﻻﺗﻴﻤﻤﻮ ﺍﻟﺨﺒﻴﺚ ﻣﻨﻪ ﺗﻨﻔﻘﻮﻥ ﻭﻟﺴﺘﻢ ﺑﺌﺎﺟﺬﻳﻪ ﺇﻷ ﺃﻥ ﺗﻐﻤﻀﻮﺍ ﻓﻴﻪ ﻭﺍﻋﻠﻤﻮ ﺃﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻏﻨﻲ ﺣﻤﻴﺪ ( )ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ267 : ).

(Ya ku wadanda kuka yi imani! Ku ciyar daga dadadan abubuwan da kuka tsururuta, da abin da muka fitar muku daga cikin kasa, kada ku nufaci lalatacce ku ce dga shi za ku ciyar alhali ku kba za ku karbe shi ba, sai kun runtse idanu. Ku sani kahika Allah mawadaci ne abin godiya). {Al- Bakara:267}.

Sannan Annibi (S.A.W) ya anbaci wani mutum da yake tsawaita tafiya. Wasu malamai sun ce tafiyar aikin hajji ce, wasu kuma sun ce tafiyar umara ce, wasu kuma sun ce a'a! yana cikin tafiya da take ta da'a ce, ma'ana dai wannan mutum yana cikin tafiya, kuma tafiyar da'a ga Allah Ta'ala, ga gashin kansa duk ya cure da juna bai nma samu ya taje gashin kansa ba, duk ya kukkulle saboda halin tafiya, sannan kuma, duk ya yi datti, ya yi kura. Manzon Allah (S.A.W) ya ambaci wannan mutum y ace, ''......

yana mika hannayensa biyu biyu zuwa sama, yana cewa ''Ya Rabbi! Ya Rabbi!!'' amma kuma abincsa haramun ne, abin shansa harammun ne, tufafinsa haramun ne, an ciyar da shi haram (tun yana yaro). Ta yaya za'a amsa masa (Addu'arsa)?'' Ma'ana, ai ba za'a amsa masa ba, sharadin da ake bukata ga addu'a a yi ta, a karba, ya cika. Ga shi matafiyi ne, ana amsa addu'ar mutumin da yake matafiyi. Saboda haka lokacin tafiya, hali ne na amsa addu'ar mutum. Ga shi kuma ''...... gashin kasna ya cakude, ya yi kura....'' wanda yake nuna yana cikin wahala. Duk mutumn da yake cikin halin tsanani, ana sa ran a karba masa addu'arsa, don Allah y ace, ( ﻓﺈﻥ ﻣﻊ ﺍﻟﻌﺴﺮ ﻳﺴﺮ )1 ( ﺇﻥ ﻣﻊ ﺍﻟﻌﺴﺮ ﻳﺴﺮ )
(Lallai a tare da tsananin akwai sauki. Lallai a tare da tsananin akwai sauki) {Sharah:

5-6}.

A nan wurin sauki biyu ne, tsanakin daya, waye zai rinjayi wani? Mutumin da ke cikin tsanani, ana sa ran sauki zai zo masa da wuri. Sannan kuma shi wannan mutumin da Manzon Allah (S.A.W) yake Magana a kansa, shi yayi riko da wani ladabi cikin ladubban addu;a shine mutum ya daga hannayensa sama.Annabi (S.A.W) in yana addu'a yana daga hannayensa sama in yagama addua kuma saukewa yake, bay a shafa fuska gashi kuma mutumin ya tabbatar wa Allah rububiyarsa, bai hada Allah da kowa ba, don yana cewa ya Rabbi Ya rabbi !! wato yana tabbatar wa Allah rububiyarsa imani da cewa ba wanda zai cire shi daga wannan abun, sai Allah.

Tsabar tauhidi duk ya kankama, amma me ya kawo cikas aka ki karbar Addu'ar sa ?

abin day a biyo baya shine , abincinsa haramun ne tufafinsa haramun ne an ciyar da shi haram , ta yaya za amsa masa (Addu;arsa) ? ba wai addu'ar ce ai karanta daidai ba ya karanta daidai ba wai don bai daga hannu, bay a daga hannu, ba wai don ba cancanta ba, ya cancanta tunda yana cikin tsanani amma me yakawo masa cikas ? sharuddaisun cika amma sai sai aka samu wani abu da ka hanawa. Kamar mutum ne ya cancanci ci ngado ta kowacce fuska, saiwani abu yazo ya hana shi cin gado misali akwai dangantaka taskaninsa da mamaci kuma lallai mamacin ya mutu wannan yana da rai ka gga dukkan sharuddai da ake bukaata sun cika wannan musulmi ne sai muka bincika muka ga wannan hadisin yana nuna mana yunkurin neman halal a cii dukkanin al'amura in za mu yi tufafi ya zamanto halal ne, haka in za mu ci ya zamnto halal ne, domin duk inda haramun take, bat a da albarka halal itace mai albarka, halal zaka ci ka kwanta lafiya, haram kuwa idan kaci ko bat a tashi anan ba to zatashi a can saboda haka, ya kamata mutum ya kiyaye wannan Allah yanacewa ﻗﻞ ﻻ ﻳﺴﺘﻮ ﺍﻟﺨﺒﻴﺚ ﻭ ﺍﻟﻄﻴﺐ ﻭ ﻟﻮ ﺍ ﻋﺠﺒﻚ ﻛﺜﺮﺓ ﺍﻟﺨﺒﻴﺚ ) ﺍﻟﻤﺎ ﺀﺩﺓ Kace halal da haram basu zama daya ba, ko da yawan haramun din ya burge ka,)Batun: Al'Adun Musulmi Da Darajoji