ARBA'UNA HADITH (12) HADISI NA SHA BIYU
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=703

 
ARBA'UNA HADITH (12) HADISI NA SHA BIYU

An karbo daga Abu Hurairata yace, Manzon Allah (S.A.W) yace, yana daga kyawun musulunci mutum barin abinda baya da mahimmanci, a gare shi tirmizi da Ibnu Majah ( 2318) ( 3976).

SHARHI; Fadin manzon Allah (S.A.W) cewa yana daga mahimmancin kyawun musuluncin mutum barin abinda baya da mahimmanci a gareshi ke nuna kyautatuwar to a rabu da shi wannan shi ke nuna kyautatuwar musulunci ka wannan muhimmancin ta fuskar addini ne amma ta fuskar duniya, duk abin da bashi da mahimmanci a duniyance to kyawun musuluncinka shi ne barin wannan al'amarin amma duk abin da yake mahimmanci o ta fuskar addini ko ta fuskar duniya to wannan ana bukatar ka neme shi, dama an halicce ka ne domin ibada Allah yanace wa ﻭ ﻣﺎ ﺧﻠﻘﺖ ﺍﻟﺠﻦ ﻭ ﺍﻻ ﻧﺲ ﺍﻻ ﻟﻴﻌﺒﺪﻭﻥ ( ) ﺍﻟﺬﺍ ﺭﻳﺔ :

(ban halicci mutum da Aljan ba sai don su bauta mini) (Azzariyat)
In ta fuskar duniya ne, Allah yace, ﻻ ﺗﻨﺲ ﻧﺼﺒﻚ ﻣﻦ ﺍﻟﺪ ﻧﻴﺎ ( ﺍﻟﻘﺼﺺ88 : )
(Kada ka manta da rabonka daga duniya )
Alkasaas 77)
Amma duk abin da baya da mahimmanci a dunia ko layhiya to yana daga kyautatar imani mutum ya bar wannan shirmen ya kama abin da zai amfane shi ko a duniyarsa ko a lahirarsa wadansu suna kafa hujja da wannan hadisin cewa idan muna tattaunawa ni da wani ta addini sai wani yazo ya tsoma baki sai mucew ai Annabi (S.A.W) yace, yana cikin kyawun musulunci mutum ya bar abin da bai shafe shi ba don haka bad a kai muke Magana ba, don me zaka tsoma baki ?

Ba haka hadisin yake nufi baa bin da hadisin yake nufi shine lallai mutmu ya bar abinda bashi da mahimmanci ba wai abin da bai shafe shi ba domin tattaunawar da kuke yi ko dai ta zamanto tana da alaka da ibada, to ta shafe ni don ni ma musulmi ne ina dangatuwa zuwa ga wannan addini ko zamanto tana da alaka da duniya in na sani dole in tsoma baki a ciki ko ya zamanto a aikin sabo kuke, ya wajaba a gareni in hani daga mummunan aiki to don me za kaec bat a shafe nib a?

Ta kowacce fuska maganr ta shafeni sai dai idan asabo kuke na yi umarni kuka ki bari sai in bar wajen, wannan hadisin Imamu Tirmizi ya waito shi da sauran wadansu malaami kamar Ibnu Majah da Imamu Ahmad acikin Musnad,amma shi ya rawaito shi ya bata fuskar Abu Hurairata bat a fuskar hasan Bin Aliyyu Bin Abi Dalib ya rawaitos hi Hadisi ne ingantacce.
Batun: Al'Adun Musulmi Da Darajoji