ARBA'UNA HADITH (16) HADISI NA SHA SHIDA
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=707

 
ARBA'UNA HADITH (16) HADISI NA SHA SHIDA

An karbo daga Abu hurairata R.A yace, wani mutum yazo, yace da Annabi kayi min wasiyya saihhi yace dashi kada kai fushi sai kayi fushi sai yayi ta maimaita bukatarsa, si (Annabi) yace, kada kai fushi Bukhari (6116) ya rawaito.

SHARHI; Dangane da lafizin ''Wasiyya'' day a zo a cikin jumlar, ''Ku yi min wasiyya.'' Abin daake nufi da 'wasiyya', shi ne wata kalma takaitacciya d azan dade ina amfani da ita a cikin rayuwata a duniya, wadda za ta dora ni a kan tafarki madaidaci. Da y ace ''ka yi min wasiyya.'' Tsammaninsa Annabi (S.A.W).

zai rubuta masa lattafi guda, amma sai y ace masa ''kada ka yi fushi'' sai yayi ta maimata bukatarsa ta dazu, ''...... yi min wasiyya.'' Annabi (S.A.W). ya tsaya bai ce komai ba, ya kyale shi. To da aka ce, ''Kada ka yi fushi!'' ai fushi ba ikonka ban e, zuwa yake yi, ba ka san ya zo ba, ka duba Annabin Allah aka ba shi attura, aka ce da shi ''..... Rike tada karfi'' amma day a zo ya sami kansa a cikin fushi, ya jefar da attaura gaba-daya. Yayin day a huce, sai ya dauke ta. To yaya za ka yi, ba za ka yi fushi ba? Ai ba zai yiwu ba a hana ka abin dab a ya yiwuwa. Don haka sai dai a ce , cewar ''Kada ka yi fushi!'' yana da ma'ana guda biyu: wadansu suke ce ma'anar da za mu iya bayarwa wajen, ''kada ka yi fushi!'' shi ne sifanta da hallaye nagari, kamar karamci, da afuwa da yawan hakuri, da yawan kyauta, kar ka zamanto marowaci.
To idan ka siffantu da wannan siffofi, su ne za su taimaka maka, su rika rage maka yawan fushi. In ba ka da su kuwa, dole ka yi fushi. Saboda Annabi (S.A.W). y ace ''Kada ka yi fushi!'' kamar yana nfin ka siffantu da dabi'u nagari, irin dabi'un da suke rage fushin.

Ma'ana ta biyu suka ce, abin da ake nufi da ''kada ka yi fushi!'' shi ne, kada ka yi aiki da fushi in ya zo maka, kar ka zartar da hukunci kana cikin fushi. Domin indan fushi ya yi yawa, kila ka zo ka cewa matarka, ka sake ta saki uku! Daga baya ka zo kana ta bin malamai kana fatwa. Don haka duk abin da fushi ya shawarce ka, ka yi, kar ka yi aiki da wannan abin, ka nisanc shi, ka zamto mai hakuri, mai juriya. {Don ganin Karin bayani duba: Jami'ul Ulum walHikam Na Ibnu Rajab 1/373-374}.

Wannan wasiyya ta Annabi (S.A.W). ta shafi dukan dangogin ayyuka na alheri, kamar yadda malamai suke ce, wannan yana cikin jawami'ul Kalim da aka ba wa Annabi (S.A.W). Wato jumla guda daya, amma za ta dauki ma'ana mai dinbin yawa, domin za ta shiga cikin kowanne bangare na rayuwa.

Domin fushi yana iya sa ka yi abu ba dan Allah ba, sai ya zamanto ba ka samu lada ba wajen Allah.

An rawaito daga Aliyyu bin Abi Dalib wata rana ya fito wajen yaki ya dauki takobinsa, ya fuskanci wani kafiri gadan-gadan zai immasa, sai wannan kafiri ya tafa masa yawu, sai Aliyyu bin Abi Dalib ya fasa kashe shi, ya ja baya, ya ba shi wuri. Sai abi nya ba wa wannan kafirinm mamaki, y ace, ''Abul- Hasan! Da ka biyo ni kamar za ka kasheni, ni,m ga shi kuma ka samu damar ka kashe ni, amma da na taho maka yawu, sai ka fasa, Ya ce ''IE! Lokacin da na taho a karon farko, na z one da niya zan yake ka, don kai kafiri n, don daukaka kalmar Allah, in gama da kai musulunci ya ci gaba, amma da ka tofa min yawu, sai na ji haushi, sai na ji tsoron kai in kashe ka, ka dauka don ka tofa min yawu ne, ba don kasancewarka kafiri ba. Don haka sai na fasa.'' To ka ga a nan wurin fusihn da Annabi (S.A.W). yake hanawa, shi ne fushi don don kanka, kar ka yi fushi don ba da kariya ga kanka, ko ba kariba ga 'yan uwanka ko 'yan gidanku, don an take mutuncinsu. Kar ka yi fushi don wannan! Shi ne ma''anar ''Kada ka yi fushi!'' Share Sign out Notify me Comment as:

Publish Preview 1 comment:

Alhassan December 20, 2011 at 12:39 PM Wane mutum ne yazo wurin manzon Allah (SAW) don niman wasiya?
Batun: Al'Adun Musulmi Da Darajoji