ARBA'UNA HADITH NA (18) HADISI NA SHA TAKWAS
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=709

 
ARBA'UNA HADITH NA (18) HADISI NA SHA TAKWAS

An karbo daga Abu Zarri, shine Jundubu Bin Junada, da Abu Abdurrahman shi ne mu'azu dan Jabal R.A, yace manzon Allah s.a.w yace, kaji tsoran Allah, a duk inda kake, kabi mummunan aikin da kayi da kyakykyawan aiki,) ya shafe mummunan ka dabi'anci mutane da kyakykywar dabi'a Tirmizi 1987 ya rawaito yace: hadisi ne hasanun a wani bugun yace, hasanun sahihun.

Dangane da fadin manzon Allah s.a.w cewa kaji tsoran Allah a duk in da kake.........mun riga mun san menene takawa itace abin da duks aka dora maka, kayi abin da duk aka hana ka ka bari, wannan shi ne takawa, kuma takawa mafi tsadar abu kenan, da Allah ya umarci mutanen farko da mutanen karshe, suyi Allah y ace Munyi wasiyya ga wadanda muka bawa liffafi gabaninku da ku da kuji tsoran Allah.

Na farko da na karshe duk an umarce su da takawa a wani lokaci za a ce kaji tsoran Allah sai aces tsoran wuta, wani lokacin sai ace kaji tsoran yinin tashin tashin kiyama Ayoyin da suke nuna haka duk abu daya ne, ma'anarsu dai tana komawa zuwa ga abu daya; kaji tsoran Allah fushin Allah kaji tsoran Ukubar Allah kuw it ace wuta.
Wannan wutar din yaushe ne ranar shigar ta ranar tashin alkiyama; ayoyin da suke nuna haka, duk abu daya ne, ma'anarsu dai tana komawa zuwa ga abu daya, kaji tsoran fushin Allah kaji tsoran ukubar Allah ukubar Allah kuwa it ace wuta. Wannan wutar din yaushe ne ranar shigar ta ranar tashin kiyama don haka idan ance kaji tsoran wunin, ba wai wunin ba'a a'a abin da zai faru cikins. In an ce da Allah ya tanada don kar ya ya yi fushi da kai, ya tilasta ma shiga cikinta. Saboda haka dai duk abu dayane, kaji tsoran Allah a duk inda kake, kaji tsoran Allah a gida a waje a ko inas, ka kiyaye dokar Allah a boye, kamar yadda zaka kiyaye ta a fili haka ake bukata.

A gaba sai manzon Allah s.a.w yace, in kayi mummunan aiki, sai ka bi biyansa da kyakykyawa shi wannnan kyakykyawan zai goge mummunan aiki da kayi. Dangin abubuwn da suke goge zunubi yana ibnul kayyim ya ambace su a cikin littafinsa akwai tuba idan mutum ya tuba, yana kankare zunubin day a biyo baya. Allah yana cewa.

ﺍﻻ ﻣﻦ ﺗﺒﺎ ﻭﺀﺍﻣﻦ ﻭ ﻋﻤﻞ ﻋﻤﻼ ﺻﻠﺤﺎ ﻓﺄﻟﺌﻚ ﻳﺒﺪﻝ ﺍﻟﻠﻪ
(Sai wanda ya tuba ya yi imani yayi aiki na gari to wadannan allah yana caja ayyukansu zuwa kyawawa, Allah ya kasance mai yawan gafara da jin kai. (alfurkan)
Akwai yawan istigfari, shi ma yana taimakawa wajen kankare zunubi ko da yaka da tuba da istigfari suna haduwa wuri guda; sannan kuma akwai aikata kyakyawan aiki mai yawa, wanda har yawansa zai sa a manta da zunubin da kayi akwai ceton masu ceto akwai tsayar da haddi a kan mutum in kayi laifi sai aka tsayar da haddi a kanka, shi kenan an kankare maka wannan zunubin.

Daga karshe hadisin sai manzon Allah s.a.w yace ka dabi'anci mutane da kyakykyawar dabi'a da hakuri da juriya Da sauran al'amura da ake son mutum ya dabi'antu da su.
Batun: Al'Adun Musulmi Da Darajoji