ARBA'UNA HAADITH (26) HADISI NA ASHIRIN DA SHIDA
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=717

 
ARBA'UNA HAADITH (26) HADISI NA ASHIRIN DA SHIDA

An karbo daga Abu hurairata R.A yace, dukkan gabbai na mutane akwai sadaka a ciki kowanne yini da rana ke hudowa cikinsa da zaka sasanta tsakanin mutane biyu dake rigima da juna sadaka ne, ka taimaki mutum game da dabbarsa, ka dora shi a akai sadaka ne ko kayansa ka dora masa akan dabbarsa sadaka ne, kalma daddada sadaka ce, dukkan taku da zaka yi tattaki zuwa sallah, sadaka ne, dauke wni abu mai cutarwa daga kan hanya sadaka ne, Bukhari (#2989) da Muslim(#1009)
suka rawaito shi.
SHARHI Wannan hadisin ya na nuna cewa dukkab gabbai wato dukkan wata mahada ta kashi kamar gwiwa wuyan hannu kafa, da dai sauransu akwai sadakar da mutum zai yi da ita haka kowanne yini, wanda a cikinsa da zaka sasanta tsakanin mutane biyu kayi adalci tsakanin mutane biyu da ke rigima da juna sadaka ne, ka wayi gari wane d awane na rigima wance ta yi yaji ka sasanta su ita da mijinta to wannan zai za abak ladan kayi sadaka haka su ita da mijinta to wannan za'a baka ladan kayi sadaka haka idan ka taimaki mutum game da dabbarsa dattijo neb a zai iya hawa kan dabbarsa ba. Sai ka dora shi akai ko ka zo wata tasha. Sai kaga wani dattijo zai hau mota da nauyin jiki ka kama ka dora shi a kan motar nan ko dukkan wani abin hawa ko ka dauki kayansa ka dora masa akan dabbarsa don shi ba zai iya hawa ba, ko ka kama masa ka taimaka masa kuka dora tare, to duk dai wannan sadaka ce. A wani hadisin sahabbai suke tambayar me zamu yi bamu da dukiyar da zamu yi sadaka, sai Annabi s.a.w yace kuyi tasbihi, kuyi hailalas in baku samu dammar wannan ba, kuyi umarni da kyakykyawan aiki kuyi hani da mummuna aiki in baku sami dammar wannan ba ku fadi daddar kalma ga 'yan uwanku musulmi sadaka ne. si yace in duk kun kasa yin wanann ka kamed bakinka kar ka fadi sharri.Batun: Al'Adun Musulmi Da Darajoji