ARBA'UNA HAADITH (28) HADISI NA ASHIRIN DA TAKWAS
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=719

 
ARBA'UNA HAADITH (28) HADISI NA ASHIRIN DA TAKWAS

An karbo daga Abu Najih, shi ne irbadu dan sariya R.A y ace Manzon Allah s.a.w yayi mana wa'azi wa'azi mai isarwa zukata suka tsorata, idanu suka zubar da hawaye. Sai muka ce dashi, ya manzon Allah s.a.w kamar wa'azin mai bankwana to kayi mana wasici da jin tsoran Allah s.a.w kamar wa'azin bankwana to kayi mana wasici sai yace, ina muku wasici da jin tsoran Allah da kuma ji dabi, ko da bawa ne ya zama shugaba a gare ku lallai wanda ya rayu a cikinku da sannu zai ga sabani mai yawa, na umarce ku ku rike sunnata, da sunnonin halifofi shiryayyu. Ku rike tad a hakoranku (Fika), ku kiyaya fararrun ala'mura domin kowacce, bidi'a bat ace. Abu dawud 4607 da Timizi yace wannan hadisi ne mai kyau.ingantacce.

SHSRHI Annabi s.a.w ya kasance yakan yi wa sahabbai wa'azi daga lokaci zuwa lokaci idan hakan ta kama awata rayuwar ta hadisin a kanuna wa'azi Annabi s.a.w yayi musu shine bayan sallar Asuba an kamala sallar sai yayi wa'azi wani lokacin idan ya so yayi musu wannan wa'azin yaka hau minbarin juma'a ya fadakar dasu, don a nuna maka ba wai sai juma'a ne kawai zaka fadakars da al'aumma ka hau mumbarins kayi innal hamdu lillahi dinka yayi iradu dan sariya yace, manzon Allah s.a.w yayi mana wa;azi mai isarwa zukata suka tsorata idanu suka zubar da hawaye a sakamakonwanan wa'azi wato wa'azi mai tasiri kenan wanda yake ratsa zuciya ya sa suna kuna zuci suna kukan idanu ina muku wa'azin ya ratsa su sun kamar kalma ce ta mai ban kwana don haka sai suka ce to kayi mana wasici sai ya ec in amutu wasici da jin tsoran Allah tsoran Allah kuwa shine kiyaye dokokin Allah ta'ala kuma ina muku umarni da ji da bi kuji ku bi ko da bawa ne ya zama shugaba a gerku lallai kuji abin day a fada kuyi biyayya dangane d aumarninsa matukar bai saba wa Allah da manzonsa ba, wannan tsari kena na shugabantar al'umma a musulunci wajibi ne al'umma suyi masa da'a sai fa idan yayi umarni da sabon Allah ne to sai su kyale shi ba zasu bishi ba a cikin abin day a umarni da shi na sabon Allah.
ma idan ya yi umarni da sabon Allah. Sai a kyale shi. Halifofin Annabi sune Abubakar da Umar bin Khaddab da Usman bin Affan da kuma Aliyu bin Abi Dalib wadannan sune halifofin Annabi s.a.w duk mulkin day a biyo baya wannan sunansa mulki ba a kiransa halifanci don su halifofi halifantar Annabi s.a.w sukye yi. Idan ka lissafa shekarun da halifofi halifantar Annabi s,a,w sukeyi. Idan ka lissafa suka yi to sukayi gaba dayansu. Zaka ga shekaru talatin din Annabi s.a.w yac shi ne lokacin halifantar Annabta daga baya kuma sai Allah ya mayar da abin daya zama mulki ga wanda ya ga dama. A tarihance sai aka samu wadannan halifofi guda hudu su suk mamaye shekarun wadansu malamai suka ce a'a wadannna sahabbai guda hudu sun mamaye shekaru ashirn da tara ne da wata shida ko wata takwas alhasan bin Aliyu bayan aliyu yayi shahada shi ya zama halifa shi kuma yayi wata shida ne ko wata hudu cikon wadannan shekaru talatin din da yaga rigima ta yi yawa sai ya sauka daga kan shugabancin ya bar wa mu'awiya yace masa yaje ya rike don a zauna lafiya. Saboda haka idan aka hada wadannan watanni da Hasan bin Aliyu yayi wata shida ko hudu ne zaka samu shekaru talatin kenan shi ma ya zamanto cikin hadisan da suke nuna wajabcins bin sunnar Annab s.a.w sai dai mai tambaya zai iya cewa shin akwai bambaci tsakanin sunnar Annabi s.a.w da kuma sunnar halifofi masu shiryarwas ko duk daya ne ? abin da ake nufi, wadannan sahabbai guda hudu idan kansu ya hadu a kan mas'ala ta addini to baz aka ga sun saba wa abin da Alkur'ani ko hadisin Annabi s.a.wf suka zo dahi shi yasa akce a bi sunnarsa bayan ta annabi s.a.wf to amma idan Abubakar ne R.T.A ya bada fatawa, ko Usman R.T.A ko Aliyu R.T.A kadai ya bada fatawa wannan dolenef sai an gwada idan ta dace da alkur'ani da hadisi to shikenan, amma idan kansu ya hadu akan wata mas'ala to da wuya kaga sun saba wa nassin Annabi (SAW).Batun: Al'Adun Musulmi Da Darajoji