ARBA'UNA HAADITH (30) HADISI NA TALATIN
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=721

 
ARBA'UNA HAADITH (30) HADISI NA TALATIN

An karbo daga Abu Sa'alaba shi ne Jursumu dan Nasihib (R.A). y ace, ''Lallai Allah Ta'ala ya farlanta farilla, kar ku tozarta su, ya sanya iyakokin, kar ku ketare su, ya haramta wasu abubuwa, kada ku keta alfarmarsu, ya yi shiru game da wadansu al'amura don jin kan ku, ba don mantuwa ba, kar ku bincike su. Darakuduni littafinsa sunan (j 4/sh 184 da waninsa.)'' Fadin Manzon Allah (S.W.T) cewa ''......Allah Ta'ala ya farlanta farilla, kar ku tozarta su....'' yana nufin lallai ku tsayar da wannan farilla yadda Allah ya dora muku su. Cewar, ''...... ya sanya iyakoki, kar ku ketare....'' wadannan iyakokin, yana nufin dangogin haram, ko kuma abubuwan da suke na haddi, idan mutum ya yi su, za'a yi masa haddi kaza, duk wanda ya yi ku, tsayar da haddin kansa.
Sai kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ci gaba da cewa ''........ ya haramta wasu abubuwa, kada ku keta alfarma......'' wadannan al'amuran da aka haramta su. Sannan sai y ace, Ubangiji, ''..... Ya yi shiru game da wadansu al'amura don jin-kan ku.....'' Ya yi shiru bai haramta sub a, ya kyale ku, ya yi shiru, ba don ya manta ba, don haka kar ku ce sai kun gao hukuncinsu, ku kyale in kuma son ku yi amfani da su, ku yi, ib ba kwa so, ku kyale, kar ku ce sai kun gano haram ne ko halal, an kyale muku sune, don rahama, ba don Allah ya manta ba. Da dama daga cikin malaman hadisi sun raunana wannan dahidi, abin d azan iya tunawa daga ciki akwai Ibnu Rajab Alhambali a cikin littafinsa, Jami'ul Ulum Wal-Hikam in ban manta bay a raunana wannan hadisi.Batun: Al'Adun Musulmi Da Darajoji