ARBA'UNA HAADITH (33) HADISI NA TALATIN DA UKU
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=724

 
ARBA'UNA HAADITH (33) HADISI NA TALATIN DA UKU

An karbo daga Abdullahi dan Abbas (R.A) ya ce, Manzon Allah Annabi (S.A.W). ya ce, ''Da za'a bai wa mutune dukkan da'awarsu, da wadansu sun yi da'awar dukiyar wadansu da jininsu' sai dai hujja tana kan mai da'awa, rantsuwa kuma a kan wanda ya yi musu.''(1) Baihaki ne ya rawito shi a cikin litaffinsa sunan (J 10/sh 252). Wani sashi na hadisin yana cikin Bukhari da Muslim.

SHARHI; Ma'ana, da duk da'awar da mutane za su yi, za'a dauka a ba su wannan abin da suka yi da'awa, misali in sun ce kaza namu ne, a ba su, ba tare da shaida ba, ba tare da an bincike ba, ''...... da wadansu sun yi da'awar dukiyar wadansu.....'' Da sun yi da'awar jinin wasu, sai Annabi (S.A.W). y ace ''...... sai dai hujja tana kan mai da'awa.....'' 
Ma'ana, ana neman mai da'awa da ita, wanda kuma ake nema day a yi rantsuwa, shi ne wanda ya yi musu, abin nufi idan na zo n ace motar da wane yake kawa tawa ce, to a shari'ance kafin ya hana ni, wannan abin da na kawo shaida. Idan na kawo shaidu suka tabbatar da wannan taw ace, dole a karbe wannan mota a ba ni, a shari'ance. Shi kuma in ya yi nikari, y ace sam! Duk da shaidar nan da na zio da ita bai yarda ba, to sai ya yi rantsuwa, don a tabbatar da haka ne. wato dai kullum mai da'awa shi ne ake bin bashin dalili idan mutum ya yi da'awar kaza haramun ne, shi za'a ce ya kawo dalilinsa, idan mutum ya yi da'awar halacci a cikin abin da asalinsa haramci ne, to wannan shi za a nemi ya kawo dalili.

Wannan hadisi asalinsa mai girma nes kwarai da gaske, yana shiga babuka da dama, musamman ma babin day a shafi hadddi, babin day a shafi rigingimu a tsakanin mutane da rigimar dukiya. Hadisi dai yana shiga babi da daman a fikihu da babin ma'amaloli.

(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA'AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).Batun: Al'Adun Musulmi Da Darajoji