ARBA'UNA HAADITH (34) HADISI NA TALATIN DA HUDU
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=725

 
ARBA'UNA HAADITH (34) HADISI NA TALATIN DA HUDU

An karbo daga Abu Sa'id Al-Khuduriy (R.A) y ace ''Na ji Manzon Allah Annabi (S.A.W).'' yana cewa ''Duk wanda ya ga abin ki, to ya gusar da shi da hannunsa, in ba shi da iko, ya gusar da shi da harshensa, in ba iko, to ya ki abin a zuci, wannan shi ne mafi raunin imani.(1)'' Muslim ne ya rawaito shi (#49).

SHARHI; Malamai suke ce, wannan hadisi yana cikin nassosin da ke nuna wajabcin umarni da kyakykyawan aiki, da hani ga mummuna.

Wannan kuma shi ne tabbatacce cikin ayiyon Alkur'ani da dama. Don haka wannan hadisi yana abin ayoyin da suke nuna wajabcin cewa, duk inda aka ga mummunan abu, to a ki shi, duk kuma in da aka ga mai kyau, a ja hankalin mutane su bi shi.

Cewa ka gusar da shi da hannunka ko ka gusar da shi da harshenka, wannan ba wajabci ban ea kan daidaikun al'umma. A'a!
wajibi ne a kan wadanda suke da ikon yin hakan a cikin al'umma. Za ka iya ganin abi nki yana faruwa, kana son ka haka su da harshenka, amma ba ka za dalilai na shari'a da za ka gamsar da wanda yake aikata wannan barnanr a kan ya bari. Ka ga, ba kai ne wanda wajibin yake kanka ba, sai dai ka yi kokarin ka sanar da wanda kake ganin zai iya wa'azantarwa da shi, ya fuskantar da shi, ya ba shi dalili, don ya sanar da shi, ba kai ba. Kai din ka fara, ba za ka iya kaiwa ko'ina ba, saboda ba ka da dalili, ba ka da abin da za ka gamsar da shi din. Wajen ture abin ko ko barna da hannu kuwa, da ma wannan, sai dai ko a kwaryar gidanku ne, za ka iya hanawa da hannunka. Amma idan ya zo titi, wadansu suka zo suna sayar da barasa a unguwarku, suka bude shagon sayar da barasa, ai ba za ka taho da sanda ka ture sub a, ko ka ce za ka fasa kwalbar barasar, ka yi tafiyarka ne, in ka yi haka, sai ka gan ka a Police Station, ana cewa sai ka biya kudin giyar da duk ka zubar. Ka ga ai t abaci! Haka kuma ko da wani lokaci in za ka gusar da barna, sai ka ga menene abin da zai biyo baya? In ka san in ka ture barna alheri ne zao biyo baya, to wajibi ne ture wannan barna. In kuwa ka san wannan barna ba za ka iya tura ta b gaba daya ba, amma dai ka rage mata kaifi, za ka iya kokarin ture wannan barna. Idan ka san in ka ture barna, wata barn ace makamanciyarta, za ta zo a cike gurbin wannan, to sai malamai suka yi sabani:

wadansu suke ce ka bar wannan , waccan ai ba kai ka janyo ta ba. In kuma ka san, in ka ture barna wata barna da ta fit a girma ita za ta maye gurbinta, to ta ci gaba da faruwa, ita karama ce, a maimakon ka jes ka ture wanna babbar barna ta zo. Wannan yana cikin fikihun da malamai suka yi Magana a kansa musamman Ibnul Kayyim a cikin Littafinsa I'ilamul Muwaki'in.

(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA'AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).Batun: Al'Adun Musulmi Da Darajoji