GAISHE DA MARA LAFIYA
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=730

 
Sheikh Isa Ali Pantami

GAISHE DA MARA LAFIYA

ZUWA GAISUWAR MARAR LAFIYA BABBAR IBADA NE!

Allah ya mana karin LAFIYA da IMANI,.... Imam Bukhari, Shaykhul Islam da Ibn Uthaymeen (Rahimahumul Laah)
dukkansu sun tabbatar da cewa zuwa gai da majinyaci wajibi ne.

Amma Bn Uthaymeen (RH) yana ganin cewa yana halatta wani ya wakilci wani a gaisuwa ko kuma zuwan wasu yasa wajibcin ya sauka kan wasu ''Fardhu Kifaayah.'' Annabi (SAW) yana cewa: ku ciyar da Mai Jin Yunwa, ku ziyarci MARAR LAFIYA, sannan ku yanta Fursunoninku (Bukhari).
FALALAR ZUWA GAISUWAN: Annabi (SAW) yana cewa: Duk wanda yaje gaisuwa ga marar lafiya da SAFE, Mala'iku dubu saba'in zasu masa Addu'ah har zuwa yamma. Idan yaje da Yamma Mala'iku dubu saba'in zasu masa Addu'ah har gari ya Waye. Kuma ana masa TANADIN LAMBU a ALJANNAH. (Tirmithiy, Sahihun ne a cikin Sahih Tirmithiy).

Annabi (SAW) ya kara da cewa: Lalle Musulmi Idan ya ziyarci Marar Lafiya to yana tafiya ne a cikin inuwar Aljannah har sai ya dawo.

(Muslim).

Yaa Allah ka bamu ikon zuwa gaisuwa ga marassa lafiya,.... Batun: Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen