ALAMOMIN KYAKYKYAWAN K'ARSHE!
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=731

 
Sheikh Isa Ali Pantami

ALAMOMIN KYAKYKYAWAN K'ARSHE!

Allah ya sa mu cika da IMANI,..

Annabi (SAW) yana cewa: Idan Allah yana nufin BAWANSA da ALHERI, sai yayi aiki da shi. Sai aka tamabayi Annabi (SAW) ta yaya Allah zai yi aiki da shi?

Sai yace:Allah zai shiryar da shi zuwa ga ayyuka na kwarai gabannin rasuwarsa (Imam Ahmad, 11625; al- Tirmidhi, 2142; saheeh by Al-Albaani ya inganta shi Saheehah, 1334).

ALAMOMIN CIKAWA DA MUTUWAR SHAAHADA:

Akwai wasu alamomi duk wanda ya rasu ya samu dacewa da daya daga cikinsu akwai alamar ya samu mutuwa mai nagarta, kuma akwai alamun yayi mutuwar SHAHAADA.
1) RASUWA DA KALMAR SHAHADA: Annabi (SAW) yana cewa: Duk wanda kalmar karshensa ya zama LA'ILA ILLA LAAH, zai shiga ALJANNAH (Abu Dawood, 3116; Saheeh Abi Dawood, 2673).

2) RASUWA TA HANYAR MATSANANCIYAR JINYA: Annabi (SAW)
yana cewa: MUMINI yana rasuwa da JIBIN GOSHI. (Ahmad, 22513; Tirmidhi, 980; Nasaa'i, 1828).

3) RASUWA DALILIN NAK'UDA ko RASUWA DALILIN KOWACE CUTA ALHALI MACE NA DA JUNA: Annabi (SAW)
yace MATAR da ta rasu tana da juna to tayi SHAHADA. Duba (Abu Dawood 3111).

4)RASUWA DALILIN CUTAR ANNOBA: Duba (Bukhaari, 2830; Muslim, 1916).

5) RASUWA RANAR JUMU'AH KO DARENTA:

Duba hadisin Ahmad, 6546; al-Tirmidhi, 1074.

al-Albaani.

6) RASUWA A TAFARKIN ALLAH: Duba Al-Qur'an Suratu Al-'Imraan 3:169.

7) RASUWA DALILIN CIWON CIKI: Duba Sahihu Muslim, 1915.

8)RASUWA DALILIN RUSHEWAR GINI KO KUMA A RUWA: Duba littafin Bukhaari, 2829; Muslim, 1915.

9) RASUWA DALILIN WUTA. Duba cikin littafin Saheeh al- Targheeb wa'l- Tarheeb, 1396.

10)RASUWA DALILIN KARE ADDINI KO DUKIYA KO RAI: Duba littafin Tirmidhi, 1421.

11) RASUWA A CIKIN KYAKYKYAWAN AIKI:

Duba littafin Imam Ahmad, 22813.

Yaa Allah ka mana baiwa da kyakykyawan karshe, sannan ka sa mu yi MUTUWAR SHAHADAH,....Batun: Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai