MARAR LAFIYA SUNNAH NE: YAA ALLAH KA BAMU KARIN LAFIYA DA IMANI,....
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=732

 
SHEIKH ISA ALI PANTAMI

MARAR LAFIYA SUNNAH NE: YAA ALLAH KA BAMU KARIN LAFIYA DA IMANI,....

SADAKA A LOKACIN JINYAN MARAR LAFIYA SUNNAH NE: Yaa Allah ka bamu karin lafiya da Imani,.... Annabi (SAW) yana cewa: Kuyi jinyar MARASSA LAFIYANKU da bada sadaka.

(Abu-Daud ya ruwaito, Shaykh Albani ya inganta shi a Sahihul- Jamiy 3358).

Yana daga karantarwar Sunnah, Idan muna jinyar iyaye ko Iyalai ko yan'uwa, mu yawaita bada Sadaqa, Domin Allah yana bada lafiya ta wannan hanyar. Yaa Allah ka amsa mana addu'o'in mu da bukatunmu,....
TAMBAYOYIN JARRABAWAN DA DOLE SAI MUN AMSA(SHEIKH ISA ALI PANTAMI)

Annabi (SAW) Yace Idan mutum ya mutu, Mala'iku biyu zasu zo masa sannan su masa tambayoyi Hudu a 'Kabarinsa. Wadannan tambayoyi sune:

1) Waye Mahaliccinka? Amsa:

ALLAH.

2) Menene addininka? Amsa:

Addini na shine Musulunci 3) Me zaka ce akan wannan da aka aiko muku? Amsa:

Muhammad, Manzon Allah 4) Menene ilminka? Amsa: Na karanta littafin Allah, kuma nayi Imani da shi. Annabi (SAW) Yace duk wanda ya amsa ko ta amsa tambayoyin nan dai dai a 'Kabari, za a rubuta sunansa/ta a cikin ''ILLIYUN'' wanda shine register ta sunayen 'yan Aljannah. (Abu Daud, 4753; Ahmad, 18063; Saheehul'Jamiy, 1676) Yaa Allah ka bamu ikon amsawa dai dai da SHIGA wannan register Mai darajaBatun: Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi