SALLAH MAFIFICIYAR IBADA !!! FITOWA TA 2
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=736

 
SALLAH MAFIFICIYAR IBADA !!! FITOWA TA 2

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

FALALAR SALLAH !!!

Haqiqa idan muka duba zamu ga sallah hanyace babba a gare mu bisa hanyar samun ni'ima da nitsuwa domin duk wanda ya tsaida ita zai samu sauqi ga dukkan al'amuransa, wanda kuma ya sa6a gareta to zaiga ba daidai ba acikin al'amarinsa.

SALLAH ita ce ke banbanta tsakanin kafiri da musulmi, saboda falalarta yasa ta zama haske dake haskaka musulmi da tabbatar da musulunci a tare dashi.

Annabi (SAW) Yace: "Banbancin dake tsakaninmu dasu (kafirai) shine yin sallah" .

[Abu-dawud da Nasa'I] .
Saboda Falalar sallah da darajarta sai da akayi tafiyar dare da masoyinmu Muhammad (SAW) sannan aka wajabta ta akan bayi.

Hadith yazo daga Anas (R.A) yace: An farlanta salloli 50 ga Annabi (SAW) a daren da akayi Isra'i dashi, sannan aka ringa rageta sai fa ta kona 5, sannan aka qira shi da cewa: Ya Muhammad Lallai ba a sauya magana a wajena, kaje za'a baka ladan sallah 50 a maimakon 5 din" .

[Maruwaita Hadith 5 suka ruwaito banda Abu-dawud] .

Shin wannan ba falala bane? Ladan sallah 50 a baka ita a guda 5.

Sallah tana kankare zunubi, tana haskaka fuskar wanda ya kyautata, tana kawar da baqin ciki da damuwa tana sada bawa ga ubangijinsa, dukkaninta addu'a ce, ttana kawar da sharri ga wanda ya kyautata, tana tabbatar da alkhayri ga wanda ya kiyayeta.

Hakanan Sujjada yana daya da cikin abunda ALLAH (SWT) yake so ga bayinsa saboda darajar sallah sai sujjada ta kasance acikinta, duba kaga sujjada nawa kake samu acikin sallolin lokuta 5 ?

Annabi (SAW) yace: "Babu wani hali da ALLAH yafi son bawansa acikinsa, kamar ya ganshi a halin Sujjada yana mai sanya fuskarsa a qasa don qanqan da kai ga ALLAH" .

[Dabarani ya ruwaito] .

Annabi (SAW) yace: "Duk bawan da yayi sujjada guda 1 saboda ALLAH, ALLAH zai rubuta masa lada kuma ya shafe masa zunubansa, sannan ya daukaka darajarsa saboda ita, don haka ku yawaita yin Sujjada" .

[Ibn majah ya ruwaito shi da salsala ingantacce] .

Hakanan idan bawa ya karanta ayar farko a suratul fatihah acikin sallarsa sai ALLAH Yace (bawana ya gode min) idan ya karanta ta 2 sai ALLAH Yace (bawana ya yabe ni) idan ya karanta ta 3 sai ALLAH yace (bawana ya girmamani) idan yazo kanta 4 sai ALLAH Yace (wannan ayar tsakanina da bawana ne kuma bawana yana da abunda ya tambaya)
ma'ana za'a amsa masa addu'arsa.

Ya 'Yan uwana wani irin dimbin lada muke tsammani daga cikin wannan falala idan muka kyautata. Haqiqa ALLAH shine masani.

Mu hadu a Fitowa ta 3 inshaa ALLAH.

Daga: Yar'uwarku Faridah Bintu Salis (Bintus~sunnah)Batun: Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin