SALLAH MAFIFICIYAR IBADA !!! FITOWA TA 4
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=738

 
SALLAH MAFIFICIYAR IBADA !!! FITOWA TA 4

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

Kamar yadda muka yi bayanin falalar sallah da irin rabautar da bawa zai samu idan ya kasance ma'abocin kulawa da ita.

Kamar yadda muka yi bayani lallai ita sallah tana da salloli na kwadaitarwa musamman kasancewa ALLAH Ta'ala yana son bawa mai yawan sujjada.

Sujjada yana daya daga cikin abubuwanda ALLAH Ta'ala yake so, saboda girman sallah da darajarta sai sujjada ya kasance wani 6angare ne daga cikin sallah, saboda kuma girman sujjada har ta zamanto hanyar shiga aljannah ga mai yawan yinta.

Sai dai kash !!! Mafi yawan bil'adama a wannan zamanin ba kowa bane yake jajircewa wajen aikata salloli na kwadaitarwa wanda zai bashi damar yawaita yin sujjadar.

Yan'uwa dole ne sai mun jajirce mun kori shaidan kafin mu samu mu cimma burinmu na son kasancewa cikin ni'imar ALLAH Ta'ala.
Haqiqa masoyinmu fiyayyen halitta Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wasallam) Ya kwadaitar damu yawan sujjada ya kuma sanar damu girman falalarta da soyuwarta ga ALLAH Ta'ala.

Kamar yadda hadithai suka zo daban daban zamu kawo wasu daga ciki kamar haka:

• Daga Abu Firas Rabi'ata bn ka'abu al'aslamy (Radiyallahu anhu) Hadimin Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi wasallam kuma daya daga Ahlussufah yace: Na kasance ina kwana tare da Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi wasallam) sai na kawo masa ruwan alwalarsa da abun buqatarsa, sai Yace dani: "tambayi abunda kake buqata" sai nace ina roqon kasancewa tare da kai a Aljannah, sai yace: "kodai wani abun ba wannan ba" sai nace: Ni dai wannan nake roqo, sai yace to ka taimaka min da yawan sujjada" .

[Muslim ya ruwaito] .

• Daga Abi-Abdillah, Thauban (Radiyallahu anhu) 'Yantaccen Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi wasallam) yace naji Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi wasallam) yana cewa: "ka kula da yawan sujjada, domin duk lokacin da kayi Sujjada daya saboda ALLAH, Sai ALLAH Ya daukaka darajarka kuma ya shafe maka zunubi daya saboda ita" .

[Muslim ne ya ruwaito shi] .

• Daga Jabir (Radiyallahu anhu) yace: Naji Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi wasallam)
yana cewa: "lallai acikin dare akwai wani lokaci, wanda matuqar musulmi ya dace yana roqon ALLAH wani abu na alkhayri acikinsa, wanda ya shafi lamarin duniya dana lahira, tabbas ALLAH zai bashi, wannan kuwa yana kasancewa ne cikin ko wani dare" .

[Muslim ne ya ruwaito shi] .

• Daga Mughira dan shu'abah (Radiyallahu anhu) yace : Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yayi qiyamullaili har sai da qafafuwansa suka kumbura, da akace dashi ai ALLAH Ya gafarta maka abunda ya gabata da wanda ya jinqirta daga zunubinka sai Yace: "Ashe bazan kasance bawa mai godia ba?" .

[Bukhari da Muslim da Nasa'e ne suka ruwaito shi] .

• Hadith yazo daga dan Abbas (Radiyallahu anhu) yace Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi wasallam) ya umurce mu da yin salkah cikin dare, ya kwadaitar game da haka, har ta kai yana cewa: "ku kula yin sallah cikin dare koda kuwa raka'a daya ne tak zaku sallata" .

[Dabarani Ya ruwaito] .

• Dabarani ya ruwaito acikin Alkabir, daga Abu-malik al'ash'ari (Radiyallahu anhu) yace:

Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi wasallam)
yace: duk mutumin da ya farka cikin dare, ya tashi matarsa, idan kuma bacci ya rinjayeta ya yayyafa mata ruwa a fuska, suka ambaci ALLAH mai girma da buwaya, tsawon wani lokaci acikin dare to tabbas za'ayi musu gafara" .

Dan'uwa mai iyali sai ka tambayi kanka sau nawa ka tashi cikin dare har ka tashi iyalinka domin qiyamullaili ???

Mu ma masu karatu sai mu tambayi kanmu shin sau nawa muka aikata hakan???

Lallai sai mun jajirce dai mun fafari shaidan kafin mu samu damar aikata ayyukan ibada.

Muna roqon ALLAH Ya bamu iko Ya gafarta mana Ya sanya mu cikin bayinsa masu tsaida sallah dayin sallolin kwadaitarwa.

(Ameen)
Mu hadu Fitowa ta 5 Inshaa ALLAH.

Daga Yar'uwarku:

Faridah Bintu Salis (Bintus~sunnah)Batun: Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin