SALLAH MAFIFICIYAR IBADA !!! FITOWA TA 6
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=740

 
SALLAH MAFIFICIYAR IBADA !!! FITOWA TA 6

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

CIGABA GAME DA WASA DA SALLAH !!!

A rubutun da ya gabata mun fara bayani game da mai wasa da sallah kamar yadda yazo daga ayoyin ALLAH da Hadisai da kuma maganganun magabata.

Manzon ALLAH (sallahu alaihi wasallam)
Yace: "Alqawarin da ke tsakanin mu da sauran bayin ALLAH sallah ne, wanda ya barta yaqi yi gaba daya ya zama kafiri" .

[Ingantacce ne Ahmad ya fitar dashi 5/346 da Tirmizi (2621) da Nasa'I (464)] .

Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi wasallam)
Yace: "Duk wanda ya bari sallar la'asar ta kubce masa (da ganganci) to ayyukansa sun lalace" .

[Ingantacce ne Bukhari fitar dashi (553) da Nasa'I (1/236] .
Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi wasallam)
Yace: "Abunda ke tsakanin bawa da shirka ita ce sallah" .

[Ingantacce ne, Muslim ya fitar dashi (82/134) da Tirmizi (2619)
Manzon ALLAH (sallallahu Alaihi wasallam)
Yace: "Duk wanda yabar sallah da gaganci, haqiqa alqawarin da ALLAH ya dauka na taimako akan shi ya warware" .

[Ingantacce ne Bukhari ya fitar dashi cikin Adabul Mufrad (18) da Ibn Majah (4034)] .

Umar dan Khattab (ALLAH Ya qara masa Yarda) Yace: "Yadda al'amari yake dukkan wanda ya tozarta sallah to bayi da kaso acikin musulunci" .

[Ingantacce ne Muhammad dan Nasr ya fitar dashi acikin Ta'azimu Qadarus swalat (925)] .

Ibrahimun Nakha'iy (Almajiri ne daga Almajiran Abdullahi dan Abbas ALLAH Ya qara masa Yarda) Yace: wanda ya bar sallah da ganganci ya kafirta" .

Ayuba Assakhityani shima abunda ya fada misalin hakan ne.

[Ingantacce ne Dan Nasr ya fitar dashi acikin Ta'azimu Qadarus swalaat (978) da sanadi ingantacce] .

Jareer Ya ruwaito daga Abdullahi dan shaqeeq, daga Abu-hurayrah (ALLAH Ya qara musu Yarda) Yace: "Sahabban Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi wasallam) sun kasance basa ganin wani aiki wanda barinsa yake mai da mutum kafiri idan ba sallah ba" .

[Ingantacce ne Hakeem ya fitar dashi (1/8)
da sanadi mai rauni, sai yace: Tirmizi ya fitar dashi (2622) da sanadi ingantacce wa lahu shaahid] .

Ya ALLAH Ka sanya mu cikin bayinka salihai masu tsayar da sallah (Ameen)
Mu hadu a Fitowa ta 7 inshaa ALLAH.

YAR'UWARKU:

Faridah Bintu Salis (Bintus~sunnah)
Batun: Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin