SALLAH MAFIFICIYAR IBADAH !!! FITOWA TA 8
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=742

 
SALLAH MAFIFICIYAR IBADAH !!! FITOWA TA 8

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

CIGABA GAME DA WASA DA SALLAH !!!

Kamar yadda muka fara haqalto abunda ya tabbata daga Qur'ani da hadisi da maganganun magabata dan gane da wasa da sallah, haqiqa addinin musulunci yayi bayani sosai ga matsayin sallah da hukuncin wasa da shi.

•Imam Ahmad Ya ruwaito cikin "isnadi" daga hadithin Abdullahi dan Amr (ALLAH Ya qara masa yarda) daga Annabi (sallallahu alaihi wasallam) Yace: "Wanda baya kiyaye sallah, bayi da wani haske bayi da hujja bayi da ku6uta, kuma zai kasance a ranar alqiyama tare da Qaruna da Fir'auna da Hamaana da ubayyu bin khalaf" .

"Sahih ne Ahmad ya fitar dashi 6576 da Daarimy 2/301-302] .
•KISSAR ANNABI MUSA (ALAIHISSALAM) DA WATA MATA DAGA BANI ISRA'ILA:

An ruwaito cewa wata mata daga cikin Bani isra'ela taje zuwa ga Annabi Musa (Amincin ALLAH su tabbata agare shi) tace: Ya Manzon ALLAH, Ni na aikata zunubi, zunubi mai girma, kuma haqiqa na tuba zuwa ga ALLAH (SWT) ka qirayi ALLAH Ya gafarta min.

Sai Annabi Musa (Alaihissalam) yace da ita:

menene zunubinki? Sai tace: Ya Annabin ALLAH, Ni na aikata zina kuma na haifi yaro kuma na kashe yaron !!!

Sai Annabi Musa (Alaihissalam) Yace: tashi ki fita Ya fajira kada a sauqar da wuta daga sama ya qona mu saboda shu'umcin ki, sai ta fita tana mai karaya a zuciyarta.

Sai Mala'ika Jibrilu (Alaihissalam) ya sauqa yace: Ya Musa, Ubangijinka madaukaki Yace a fada maka, Me yasa ka kori wacce take neman tuba Ya Musa, shin baka san akwai abunda yafi wannan sharri ba ???

Sai Annabi Musa (Alaihissalam) Yace:

menene abunda yafi wannan sharri? Sai Jibrilu (Alaihissalam) Yace: "BARIN SALLAH DA GANGANCI".

•MU HANKALTA: wannan kissar tana mana hannunka mai sanda wajen nuna mana cewa Barin sallah da ganganci zunubinsa yafi muni sama da wanda ya aikata zina wa'iyazubillahi.

Ya ALLAH Ka gafarta mana zunubanmu kuma ka kar6i kyawawan ayyukanmu kuma ka sanya mu masu tsaida sallah tare da bayinka salihai (Ameen)
Mu hadu a Fitowa ta 9 inshaa ALLAH.

YAR'UWARKU:

Faridah Bintu Salis (Bintus~sunnah)Batun: Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin