MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 3
 
Wannan Labari Ya fito Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
URL na Wannan Labari Shine:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=747

 
DR MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 3

ME YA FARU A KARBALA? 3 Rikicin mawallafa a game da YAZIDU Yana da wahala kwarai ka samu mutum a tarihi wanda aka yi ta takin saka a kansa, ruwayoyi kuma suka rinka cin karo da juna a kan sa kamar YAZIDU. Yawan masoyansa masu yabon sa, da makiyansa masu sukar sa na sanya mai karatun tarihi a cikin rudani ba na wasa ba. Zan bada wasu 'yan misalai don mu gane wannan.

Misali na Daya: A yayin da Ibnu Abdi Rabbihi ya ruwaito cewa, YAZIDU ya damu da nadin da aka yi masa a matsayin kwamanda wajen yakin Qustantiniyah kuma har ya zargi babansa da son halaka shi. Kai har ma wai zambo ya yi ma baban nasa! (Duba Al Iqdul Farid na Ibnu Abdi Rabbihi 4/367)
Shi kuma Ibnu Tolon cewa ya yi YAZIDUn ne ya nemi a ba shi wannan mukami.
Saurari ruwayarsa kamar haka:

Watarana Fakhitah matar Mu'awiyah ta zagi YAZIDU a gabansa sai ya ce mata, ai YAZIDU ya fi danki Abdullahi. Da ta gardamta ma sa sai ya aika aka kira Abdullahi a gaban ta don ya nuna mata banbancin su. Da Abdullahi ya zo sai ya tambaye shi in yana da wata bukata. Abdullahi sai ya kada baki ya ce, baba jaki nake so ka saya min! Mu'awiyah ya ce, to, kin ga irinta! Ai kai ma jaki ne. Tashi ka ba ni wuri. Nan take ya aika aka kira masu YAZIDU, sai ya yi masa irin tayin da ya yi ma dan uwansa. YAZIDU sai ya fadi ya yi sujada don godiya ga Allah. Da ya daga kansa sai ya taya babansa murna da Allah ya nuna masa wannan rana da ya amince ma dan cikinsa.

Sannan ya ce masa, bukatocin dan sarkin musulmi su ne kamar haka:

1. Ka shugabantar da ni a wajen Jihadi 2. Idan kwarewata ta bayyana sai ka yi mini Amirul hajji 3. Ka fada ma jama'a na nemi ayi masu karin albashi kuma ka aminta 4. Ka yanka ma marayu sabon tsarin albashi 5. Daga baya sai ka ayyana ni a matsayin yariman da zai gaje ka (Duba littafin Qaidus Sharid Min Akhbari Yazid na Ibnu Tolon, shafi na 25-26).

Duda irin banbancin da ke tsakanin wadannan ruwayoyi guda biyu. A ta farkon an nuna YAZIDU a matsayin wani wawa da bai san ciwon kansa ba, har zambo yake ma mahaifinsa a kan tura shi yaki. A ta biyun kuma sai ya fito wani sadauki, jarumi, mai tarin basira da hankali, ga nazari da iya siyasa.

To, wace riwaya zamu dauka?

Zamu ci gaba da kawo misalai irin wadannan don mu tabbatar da yadda marubuta suka sha banban wajen bayyana wannan dan taliki sannan daga bisani mu fadi ra'ayinmu a kan sa. Bayan haka sai mu koma maganar siyasa, ina nufin nadinsa da Abubuwan da suka haifu bayan sa.


 

Batu: Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi


Comments 💬 التعليقات