MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 5
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=749

 
DR MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 5

MEYA FARU A KARBALA? 5 Har yanzu dai a kan Yazid Mun riga mun fadi cewa, akwai rikici mai yawa a tsakanin mawallafa game da sha'anin Yazidu har mun soma bada wasu 'yan misalai a kan haka.

Daga cikin abin da ke nuna haka zamu ga zancen wasiyyar da Mu'awiyah ya yi masa Dinawari da Ibnu Abdi Rabbihi duk sun ruwaito ta. Amma Dinawari cewa ya yi Mu'awiyah ya yi masa wannan wasici ne baka da baka, amma shi Ibnu Abdi Rabbihi sai ya ce Mu'awiyah ya rubuta ta ne a yayin da Yazidu yake can yana farauta da wasanni kuma bai dawo ba sai bayan mutuwar uban nasa.

Duba Al Iqdul Farid na Ibnu Abdi Rabbihi (4/372) da kuma Al Akhbarut Tiwal na Dinawari, shafi na 225.

To, wace ruwaya ce ta gaskiya a cikin wadannan?
Game da zancen kashe HUSAINI ma riwayoyin mutanen Kufa (Iraq)
sun karkata ga zargin Yazidu da bada umurnin a yi wannan danyen aiki.

Wasu riwayoyin kuma cewa suke ya barrantar da kansa har da rantsuwa cewa bai ce a kashe shi ba, ya dai ce a dakatar da shi ne daga yunkurinsa na juyin mulki.

Haka ma game da iyalansa, an ce ya wulakanta su, an kuma ce ya girmama su.

Akwai ma riwayoyin Abu mikhnaf da ire- irensa masu cewa ya dauki karen gamba ya rinka sokawa a cikin hancin Husaini lokacin da aka zo masa da kansa.

Yana wulakanta shi yana Jin dadi. Alhali akwai riwayoyi da suka ce kuka ya rinka yi har da la'antar gwamnan Kufa, yana cewa bai mutunta Manzon Allah ba ga iyalansa. Kuma duk wadannan akwai su a littafan tarihi irin na su Tabari da Ibnu Sa'ad da makamantansu. Zamu dawo ga wannan maganar idan mun zo zancen Karbala.

Amma kafin mu karkare magana kan Yazidu yana da kyau a san abubuwan da Ahlussunna ke la'akari da su wajen yanke hukunci a kan kowane mutum.

1. Musulmi duk yana da alfarmar da ya kamata a kiyaye masa. Ba ya halasta a shiga rigar mutuncinsa sai da dalili tabbatacce.

2. Kuskure a wajen kyautata ma musulmi zato ya fi alheri bisa yin daidai wajen cin zarafinsa. Domin a na farkon, Allah na iya yi ma uzuri, amma a na biyun mai alhaki zai ja alhakinsa.

3. Wanda bai gani da idonsa ba, ko ya ji da kunnensa, to idan ya ba da sheda, shedarsa ba kammalalliya ba ce, domin ba ta ginu a kan ilmi ba. Kamar yadda Allah ya ce: ﺍﻻ ﻣﻦ ﺷﻬﺪ ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻭﻫﻢ ﻳﻌﻠﻤﻮﻥ. ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺰﺧﺮﻑ: ٨٦ ''Sai dai wadanda suka yi shaida da gaskiya, kuma suna sane (da abin da suka yi sheda a kansa).

4. Maganar abokin gaba ba a karas da ita sai an tabbatar da tsarkin zuciyarsa da gaskiyar harshensa. Amma abokin gaba da aka san shi da shara ta to sai anyi nazari an duba sauran ruwayoyi sannan a yanke hukunci.

5. A kan kowane mutum akwai abinda yake yuwa a jingina masa. Ko a cikin abokanenka da zaran an ce wane ya yi kaza, zaka yi fararat ka ce a'a. Ba dai wane ba.

Wani kuma da zaran an fada zaka ce karamin aikinsa ne. Wannan fa tun baka bincika ba kenan, to ina ga ka tambaye shi ya karyata zargi? Wannan shi ya sa yake da kyau mu san cikakken tarihin mutum kafin mu dau matsayi a kan duk wani labari da aka jingina masa. Kuma wannan shi ya sa masu hankali ke sanya nazari kan almajiran Annabi Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam la'akari da dinbin yabon su da muke ta karantawa kullum a cikin maganar Allah. Wanda Allah ya saukar da dawwamammen littafi ana karantawa a kan yabon sa, zai yiwu ya zama shi ne abin zargi?

6. Mutum ya kan iya yin laifi kome girmansa amma ya kasance ya tuba daga bisani ko ya gamu da wani hukuncin Allah a nan duniya wanda zai shafe laifinsa, ko ladarsa ta rinjayi zunubinsa, ko ya samu gamon katar da ceton Manzon Allah, ko Allah ya dubi tsarkin zuciyarsa ya yafe kurensa ko ya yafe masa laifinsa. Don haka ya sa Ahlussunna ba su zagi, ba su la'anta domin ba su son shiga tsakanin mutum da mahaliccinsa.

Wadannan ka'idoji ne da suka shafi Kowa da Kowa. Ba ina nufin Yazidu ba. Amma maganar Yazidun da nasa laifi tana nan tafe.

Ku kara biyo mu.

Ma'assalam.
Batun: Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi