MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 6
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=750

 
DR MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 6

ME YA FARU A KARBALA? 6 Matsayin Sayyidina Hussaini game da gwamnatin Yazid Kafin mu je can, yana da kyau muyi waiwaye game da gwamnatin da ta kawo shi mulki, ina nufin gwamnatin babansa Mu'awiyah.

Abinda aka sani ne cewa, har zuwa lokacin wafatin sayyidina Ali ba wani nadadden sarkin musulmi in ba shi ba.

Babu kuma wanda yake da'awar son ya karbi wannan mukami daga wurinsa. Amma bayan da sayyidina Ali ya samu shahada ta hannun Abdurrahman bin Muljam (daya daga cikin 'yan Khawarij wadanda suka yi tawaye daga rundunarsa – Shi'arsa), sai mutanen Iraq suka nada dansa AlHasan, a yayin da mutanen Sham suka nada gwamnansu Mu'awiyah. Ba kuma wani bangaren da ya tuntubi wani a wajen aiwatar da muradinsa.
Wannan shi ne karo na farko a tarihin musulunci da aka samu sarkin musulmi biyu a lokaci guda. Don warware wannan takaddama ne Al Hasan Radiyallahu Anhu ya gayyaci Mu'awiyah da kansa don su sasanta, daga karshe kuma ya sauka ya gabatar da Mu'awiyah, ya kuma sanya mutanen Iraqi yin haka. Wannan shi ya tabbatar da busharar da Manzon rahama ya yi a kansa cewa, jikan nan nawa zai zama shugaba, kuma Allah zai kawo karshen wata tarzoma da zata barke a tsakanin manyan bangarori biyu na musulmi. Sahihul Bukhari (7/74) da Al Jami' na Tirmidhi, hadisi na 3775.

HUSAINI Radiyallahu Anhu ya Lizimci kawaici game da abinda wansa ya yi amma a zuciyarsa bai ji dadi ba kamar yadda akasarin mutanen Iraqi ba haka suka so ba amma dai ya daure ya yi mubaya'a tare da sauran jama'a.

Ba wani rahoto da ya nuna ko sau daya ya taba nuna ma Mu'awiyah rashin goyon bayansa ga gwamnatinsa kamar yadda shi ma Al Hassan din ya yi. Sukan karbi kyautarsa, suna mutunta shi tare da bin umurninsa. Kusan ma duk yakokan jihadi da aka yi a zamaninsa tare da su aka yi. HUSAINI ma yana cikin rundunar Yazidu wadda ta ci Qustantiniyah. Shekaru goma ne Al Hasan ya yi a karkashin mulkin sayyidina Mu'awiyah, Husaini kuma ya kara wasu goma bayan haka.

A cikin wasiyyar da Al Hasan ya bar ma kaninsa HUSAINI ya gargade shi da kada ya rudu da mutanen Iraqi.

Ya ce masa ka san wahalar da mahaifinmu ya sha a hannunsu, kuma ni ka ga irin tozartawar da na gani hannunsu wadda ta sa na yada mangoro na huta da kuda. Don haka, kada ka yarda su sake janka cikin wannan lamari. Ga dukkan alamu Allah ba zai hada Annabta da halifanci a gidanmu ba. Al Imam At Tabari ya kawo wannan wasiyyar a tarihinsa.

To, ko sayyidina Husaini ya rike wasicin yayansa? Amsa ita ce eh, ya rike wasicinsa amma sai dai akwai wasu abubuwa da suka biyo baya. Sai a ci gaba da biyo mu domin jin abinda ya faru.Batun: Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi