MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 8
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=752

 
DR. MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 8

ME YA FARU A KARBALA? 8 Yarima Ya Zama Sarki Tun daga hudubar farko da Yazid ya yi ya fara sauya siyasar mulki daga ta babansa kamar yadda hausawa suka ce Sarki Goma Zamani Goma. Yazid ya soma da jajanta ma jama'a game da mutuwar sarkin musulmi Mu'awiyah, Sannan ya bada sanarawar game ma mutane albashin wata uku (a wancan lokaci talaka albashi gwamnati ke masa, sunnar da sarkin musulmi Umar Dan Haddabi ya fara), Sannan Yazidu ya ce ya jinkirta yaki a bangaren teku saboda shigowar lokacin sanyi. Daga juyayi sai mutane suka koma murna.

Ba a Sham kadai aka yi wa Yazidu mubaya'a ba, a'a har da Makka da Madina da sauran garuruwan musulmi.

Amma mutum biyu da muka sani cewa ba su yi mubaya'a ba suna nan a kan matsayinsu.

Kuma ganin kamar gwamnan Madina Al Walid bin Utbah zai yi yunkurin tilasta su sai suka sauya mazauni su biyun suka koma Makka.
Hussaini Radiyallahu Anhu ya kwashe duk iyalansa ya tafi da su, in ban da kanensa Muhammad bin Ali (Ibnul Hanafiyyah) shi kam daman ya yi mubaya'a kuma ya shawarci Husaini da ya canza ra'ayi shi ma ya yi.

Yin wannan hijira da sayyidina Husaini ya yi sai ta ba mutanen Iraqi irin damar da suke nema. Take kuwa suka fara aike masa sakonni suna nuna masa cancantar ya dawo garinsu. Wasa wasa sai magana ta girma, Iraqawa sun dau alkawalin tumbuke gwamnatin Yazidu da kafa sabuwa da sabon sarki shi ne Husaini.

Masu lura da al'amurra sun ga abinda ke kai da komo, kuma sun bada shawarwarin da ya kamata. Abdullahi bin Abbas cewa ya yi, a ra'ayina ya kamata mutanen Iraqi su fara cire gwamnansu su damka maka kujerarsa idan har da gaske suke yi. In ya so sai ka fara daga can. In ba haka ba ba na ganin ya kamata ka bar Makka saboda wadannan mutane mayaudara ne.

HUSAINI ya aiki kanensa Muslim bin Aqil bin Abi Talib don ya bincika masa gaskiyar mutanen. Da tafiya ta yi tafiya ya aiko a fada ma Husaini tafiyar tana da wahala sosai yana rokon ya bar shi ya koma Makka sai Husaini ya roke shi ya hakura ya ci gaba da tafiya. Isar sa Kufa ke da wuya sai yan Shi'ah suka kewaye shi, suka jaddada mubaya'arsu ga Husaini ta hannunsa. Kimanin mutane 18,000 ne suka dau alkawari ga Allah na kare HUSAINI. Ganin haka sai Muslim ya tayar da manzo na musamman don ya sanar da shi abinda ake ciki, alabashi shi kuma ya kama hanya ya iso.

Sai dai kamar yadda zamu gani nan gaba duk wannan yaudara ce kawai ba maganar arziki ba. Shi kansa Muslim za a kashe shi a fili ko dangwara fuskar wani ba ayi ba.

A Makka dai mutane masu dinbin yawa ne suka shawarci Husaini da kada ya dauki wannan mataki. Cikinsu har da sahabbai irin su Jabir Dan Abdullah da Abu Sa'id Al Khudri da Abu Waqid Al Laithi da Umar bin Abdirrahman bin Al Harith da Ibnu Abbas dai sauran su.

Anya kuwa wadannan shawarwari da nasihu sun yi amfani? Babu shakka HUSAINI ya saurari wadannan shawarwari da zuciya wankakka sai dai Kaddara ta Riga fata!

Zamu ci gaba gobe in sha Allah.Batun: Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi