MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 14
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=758

 
DR MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 14

ME YA FARU A KARBALA? 14 Me ya biyo bayan kashe Husaini?

Bayan da mutanen Kufa suka ga abinda ya faru a ranar Ashura sai suka hakikance sun ci amanar sayyidina Husaini tun da su suka gayyato shi amma kuma suka tozarta shi. Sun fito da shi daga amintaccen gari kuma sun yi biris da zuwansa har mai aukuwa ta auku. To, sannan ne fa suka fara tunanin yadda zasu kankare ma kansu wannan laifi. A nan ne wata kungiya ta bayyana mai suna ''Jaishut Tawwabin'' rundunar masu tuba.

Babbar manufar wannan kungiya tasu ita ce yin gangami don fada da gwamnatin Banu Umayyah da ta zama gwamnatin 'yan ta'adda wadda ba ta kiyaye alfarmar jinin gidan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ba. Manufa ta biyu ita ce daukar fansar jinin 'ya'yan gidan Manzon Allah da aka kashe. To, sai dai wannan fargar jaji da 'yan Shi'ah suka yi ba ta yi wani tasiri na azo a gani ba. A maimakon haka sai ta ida dagula lamurra, ta kara auka al'ummar musulmi cikin rikici. Duk abinda 'ya'yan wannan kungiya ta 'yan tuba suka yi bai wuce kamfe ne da furofaganda ba ta batunci ga gwamnatin Yazid da kokarin wanke hannun 'yan Shi'ah daga wannan ta'asa. A cikin wannan kungiyar ne aka samu wani dan ta'adda mai suna Mukhtar bin Abi Ubaid Ath Thaqafi wanda ya lashi takobin sai ya ga bayan duk masu hannu ga kisan Husaini.
A cikin haka kuwa ya halaka mutane masu dinbin yawa wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, tare da cewa kuma lalle ya kashe da dama daga cikin mutanen waccan la'anannar runduna ta Bin Ziyad. Daga karshe dai Mukhtar ya yi da'awar cewa, yana haduwa da mala'ika Jibrilu a kullum don tattauna matakan da yake dauka a cikin wannan Jan aiki da ya dora ma kansa. Ya dai zamo wani dan karamin annabi kenan. Daga cikin babban tasirin da kungiyar Tawwabuna ta yi ta shigar da mutanen Makka da Madina cikin wannan rikici. Ina nufin yunkurin juya gwamnati mai ci ta Yazidu. Kodayake ba lalle ne a dora masu dukan alhakin abinda ya faru ba. A Makka tun da labarin Karbala ya je ma su sai Abdullahi bin Zubair ya nemi goyon bayan jama'a a kan zama khalifa, kuma ya samu nan take. Kamar dai mutanen Makka na ganin duk gwamnatin da ta iya tafka wannan danyen aiki to, tawaye a kanta ya zama wajibi.

A Madina birni Manzo kuwa, jama'a sun tashi haikan don nuna alhininsu game da abinda ya faru. Tuni suka tsige gwamnansu Usman bin Muhammad bin Abi Sufyan, suka kuma gargada duk dangin Banu Umayya da ke zaune a Madina suka fitar da su daga cikinta a mtasayin wani gargadi na yin tawaye ga gwamnatin Yazidu.

Wannan ya faru bayan an tattara su a cikin gidan Marwan bin Al Hakam inda suka yi fursuna na wani dan lokaci. Kuma an ruwaito cewa adadinsu na da yawan gaske. Bayan sama da watanni goma da aka yi ana famar sasanta wannan lamari, mutanen Madina sai kara cijewa a kan matsayinsu suke yi. A nan ne Yazid ya tashi wata runduna da ya yi mata izinin yakar gari mai alfarma bayan gargadi na kwana uku da ya amince a ba su na su dawo ma doka.

Wanda ya jagoranci wannan runduna shine Muslim bin Uqbah. A nan ne fa Yazid ya iyar da kife sauran kimar da yake da ita a idon jama'ar musulmi na duniya ta wancan lokaci.

Domin kuwa duk kokarin da rundunar Muslim ta yi na shawo kan mutanen Madina su koma ga da'a cin tura ya yi. Masu shiga tsakani duk suka hakura. Daga karshe kaddarar Allah ta gudana da ayi ta'addancin halasta wannan birni da Manzon Allah ya haramta. An yi hasarar rayuka da dama na mutanen kirki masu ibada da matasa da malamai har da wasu daga cikin 'ya'yan sahabbai. Bayan da Muslim ya tarwatsa rundunar mutanen Madina, ya karya karfin mayakansu sai ya nada masu sabon gwamna shine Ruhu bin Zinba'u.

Wannan kuwa ya faru a farkon watan Dhul Hajji na shekara ta 53H. Da Muslim ya gama wannan barna sai ya tasar ma birnin Makka mai alfarma bisa ga umurnin sarki Yazid. To, amma Allah bai yi masa jinkiri ba tunda rai ya yi halinsa tun yana kan hanya. Wanda ya karasa tafiya da rundunar shi ne Husaini bin Numair.

Sun isa Makka daidai lokacin aikin hajji, suka je Minna da Arafat, suka yi hadaya tare da jifar Shedan. Amma fa ba hanyar shiga Makka balle ayi dawafi da sa'ayi tunda rundunar Ibnuz Zubair ta yi zobe ta cikin garin Makka.

Haka su kuma Ibnuz Zubair da jama'arsa sun yi dawafi da sa'ayi amma ba zancen tsayin Arafat tunda ba su iya fita gari. Sai aka yi canzaras; ba wanda hajjinsa ya inganta a wannan shekarar. La haula wala kuwwata Illa billah. Watanni hudu rundunar Yazid na fake da Makka, bayin Allah na ciki suna shan azabar rayuwa, ba a shiga ba a fita, sai ga ikon ubangiji ya bayyana, labari ya iso cewa sarki Yazidu ya gama da duniya. To, ko ya wannan kunyatattar runduna ta karasa da Ibnuz Zubair da mutanen Makka? Zamu ci gaba in sha Allah.Batun: Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi