MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 17
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=761

 
DR MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 17

MEYA FARU A KARBALA? 17 Mu Koma Kan Yazid Nuni ya gabata a can baya zuwa ga irin sabanin mawallafa a game da Yazid. Bisa ga wannan ne mutane suka kasu kashi uku a kan shi. Wasu na zagi har ma da la'antar sa, wasu na yabon sa da gwarzanta shi. Kashi na uku su ne wadanda suka tsaya a tsakani suna neman ayi masa adalci a ajiye shi a matsayin sauran ire- irensa daga cikin sarakunan musulunci masu rauni wadanda suka tafka kurakurai a cikin mulkinsu. A sa su a cikin ayar da madaukakin sarki yake cewa (ﻭﺁﺧﺮﻭﻥ ﺍﻋﺘﺮﻓﻮﺍ ﺑﺬﻧﻮﺑﻬﻢ ﺧﻠﻄﻮﺍ ﻋﻤﻼ ﺻﺎﻟﺤﺎ ﻭﺁﺧﺮ ﺳﻴﺌﺎ ﻋﺴﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻥ ﻳﺘﻮﺏ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻏﻔﻮﺭ ﺭﺣﻴﻢ ( ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺘﻮﺑﺔ: ١٠٢ ''Kuma wadansu sun yi ikirari da laifukansu, sun gauraya aiki na kwarai da wani maras kyawo, yana yiwuwa Allah ya yi tuba a kan su, lalle Allah Mai yawan gafara ne, mai gamammen jinkai''.

Suratut Taubah: 102 Mu saurari wani daga cikin malamai masu irin wannan matsakaicin ra'ayi, shi ne Imam Abu Abdillahi Adh Dhahabi.

Ga abinda ya ce a cikin tarihin Yazid a littafinsa SIYAR A'LAM AN NUBALA (7/36):

ﻟﻪ ﻋﻠﻰ ﻫﻨﺎﺗﻪ ﺣﺴﻨﺔ ﻭﻫﻲ ﻏﺰﻭ ﺍﻟﻘﺴﻄﻨﻄﻴﻨﻴﺔ، ﻭﻛﺎﻥ ﺍﻣﻴﺮ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﺠﻴﺶ، ﻭﻓﻴﻬﻢ ﻣﺜﻞ ﺍﺑﻲ ﺍﻳﻮﺏ ﺍﻻﻧﺼﺎﺭﻱ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ.... ﺍﻟﻰ ﺍﻥ ﻗﺎﻝ :

ﻭﻳﺰﻳﺪ ﻣﻤﻦ ﻻ ﻧﺴﺒﻪ ﻭﻻ ﻧﺤﺒﻪ، ﻭﻟﻪ ﻧﻈﺮﺍﺀ ﻣﻦ ﺧﻠﻔﺎﺀ ﺍﻟﺪﻭﻟﺘﻴﻦ، ﻭﻛﺬﻟﻚ ﻓﻲ ﻣﻠﻮﻙ ﺍﻟﻨﻮﺍﺣﻲ، ﺑﻞ ﻓﻴﻬﻢ ﻣﻦ ﻫﻮ ﺷﺮ ﻣﻨﻪ ..

Tare da tubatubansa yana da alheri guda daya, shine yakar Qustantiniyah. Kuma shi ya jagoranci yakin, alhali a cikin rundunar akwai manya irin su Abu Ayyub Al Ansari mai masaukin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam.. Har dai inda Dhahabi ya kai ga cewa, ''Yazidu na cikin wadanda ba ma zagin su, ba ma kuma kaunar su. An yi ire-irensa da dama daga cikin halifofin daulolin guda biyu (yana nufin Umawiyyawa da Abbasiyyawa), haka ma a cikin gwamnoni an yi ire-irensa da ma wadanda shi ya dara su dama.
A baya mun kawo hadisin da ya nuna falalar wannan jihadi da su Yazidu suka yi wanda Bukhari ya ruwaito shi – hadisi na 2924 – daga Ummu Haram Al Ansariyyah matar sayyidina Ubada bin Samit wadda ta ce, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya ce ''runduna ta farko daga al'ummata wadanda zasu yi yaki a kan teku an gafarta masu. Sai na ce, ya Manzon Allah, ni ina cikinsu? Ya ce, eh, kina cikinsu. Sannan ya ce, kuma runduna ta farko daga al'ummata da zasu yaki birnin Qaisar – Qustantiniyah – su ma an gafarta masu. Na ce, Manzon Allah ina cikinsu? Sai ya ce, a'a.

Kuma mun fadi ba ta ga wannan yakin da Yazidu ya jagoranta ba don ta cika bayan gama wancan yaki wanda babansa Mu'awiyah ya jagoranta kai tsaye.

Kamar yadda bakin da ba ya karya ya fada mata.

Game da la'antar Yazid kuwa da ma la'antar kowane irin musulmi – kai har da kafiri – ba aikin mutanen kirki ba ne. Domin kuwa manzonmu Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya ce a hadisin Abdullahi bin Mas'ud Radiyallahu Anhu: ''Musulmi ba mai yawan suka ne ba, ba mai yawan la'anta ne ba, ba kuma mai fadin kazamar magana ne ko kalmar alfasha ba''.

Imam Al Bukhari ya ruwaito shi a cikin AL ADABUL MUFRAD, Hadisi na 312, haka ma Ibnu Hibban a cikin Sahihin littafensa (1/421) Hadisi na 192, haka ma Imam Ahmad a cikin MUSNAD (1/404) da kuma Tirmidhi a cikin SUNAN (4/350), Hadisi na 1977.

Albani da Arna'ut sun inganta shi.

Magabata da dama sun kasance suna kame bakinsu daga la'antar ko da dabba ce, domin watarana a cikin tafiye tafiyen Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya ji wata mata ta la'anci rakumarta don ta kusa kayar da ita, sai ya yi umurni a dauke kayan da ke kan rakumar a sake ta. Ya ce, ''An riga an la'ance ta''. Imran bin Husain da ya ruwaito Hadisin ya ce, yanzu haka kamar ina ganin ta tana tafiyarta kowa ya fita batunta. Duba SAHIH MUSLIM (8/23), Hadisi na 6769.

Wani muhimmin al'amari da ya kamata mu yi nuni gare shi a nan shi ne tasirin farfagandar JAISHUT TAWWABIN da muka ambata a baya na karin gishiri ga mafi yawan labaran abubuwan da suka faru.

Misali, masu tantance ruwayoyi sun yi suka ainun ga riwayoyin da suka ce, an je da kan sayyidina Husaini har birnin Sham wurin Yazid, ballantana sauran almarar da aka hikaito ta cewa ya fashe haushi, da nuna murna har da wasu baitoci na rashin kunya. Haka kuma game da iyalansa bai inganta cewa, an yi masu wulakanci ko dan kadan ba. Maimakon haka ma da aka zo da su wurin Yazidu ya mutunta su, kuma ya yi masu rantsuwa cewa bai yi umurni da haka ba, bai kuma ji dadi ba.

Juyayi da makokin Husaini dai babu shakka wata bidi'a ce babba da take da manufar ci gaba da tona mikin da tuni wadanda suka yi shi sun gamu da Allah ya hukunta su. Da yana cikin addini a yi makokin wani ai kuwa da an shar'anta ayi na kakan Husaini wanda shine fiyayyen talikai. In kuma sun ce ai saboda an zalunce shi ne, to da shi da mahaifinsa wa aka fi zalunta? Shi ya yi fito na fito har ya samu sa'ar halaka mutane 88 a cikinsu ya aika su zuwa Jahannama a wurin kokarinsu na kama shi, sannan shi ma suka samu kashe shi bayan kama shi din ya faskara.

Amma shi mahaifinsa kwanton bauna aka yi masa yana hanyar tafiya masallaci cikin duhun asuba aka kashe shi. To, don Allah a tsakanin su biyun wa aka fi zalunta? Kuma in wannan ne dalilin yin makoki don me da ba a yin na babansa? Haka su ma Halifofi biyu da suka gabaci Ali kowanensu yana matsayin shugaban musulmi aka kashe shi kuma a cikin birnin manzon Allah mai alfarma. Idan kuma sun ce don ya yi shahada ne wajen kare addini, sai mu ce wannan kam ai abin buki ne, da Shari'a ta amince da yin bukin.

Wane ne ba ya son ya samu shahada? Sai a zauna ayi ta kururuwa ana yanka jiki don wani masoyinmu ya tafi aljanna? Kuma da haka ne da shugaban Shahidai Hamza baffan Manzon Allah ya fi Husaini cancanta. In sun ce ai kisan na wulakanci ne, to, ai kowa ya san irin wulakancin da aka yi ma gawar sayyidina Hamza, abinda ya bakanta ran Manzon Allah matuka. Amma duk da haka, masu hannu ga wannan lamari duk sun tuba, kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya karbi tubansu, ya bar su da Allah idan tuba na gari suka yi Allah ya sani. In ma ba haka ba to, can su da Allah masanin gaibi.

Alkur'ani ya fada mana cewa, Banu Isra'ila sun yi ta kisan Annabawan Allah. (Duba misali, Suratul Baqara: 87 da kuma 91). In da makoki Ibada ne don me da ba a umurci Manzo Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya yi masu makoki ba?

Allah ya jikan babban malamin Tabi'una; Rabi'u bin Khuthaim, a lokacin da aka gaya masa an kashe Husaini sai ya ce, sun kashe shi? Aka ce masa eh. Ya ce INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN.

Sannan ya karanta aya ta 46 a Suratuz Zumar inda Allah ke cewa: ''Ka ce, Ya Allah! Mai kaga halittar sammai da kasa, masanin fili da boye, Kai ne ke hukunci a tsakanin bayinka a cikin abinda suka kasance suna saba wa juna a cikinsa''. Bayan haka Malam Rabi'u bai sake cewa uffan ba.

Duba AL AWASIM MINAL QAWASIM na Al Qadi Abubakar Ibnul Arabi Al Ishbili, shafi 131.

Ranar Ashura kafin ta zama ranar shahadar Husain ta kasance rana mai tarihi da ya sa Annabi Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam yana azumtar ta tun yana Makka kamar yadda mushrikai su ma suna yi. Da ya zo Madina kuma ya tarar Yahud su ma suna yi, ya umurci musulmi su ma su yi shi a matsayin farali har sai da aka saukar da azumin Ramadhan sannan aka dauke faralci aka bar shi a matsayin Sunnah. Duk abinda ya faru bayan wucewar Manzon rahama ba zai canza shari'ar da shi Manzon ya bar mu a kanta ba.

Alhamdu Lillah.Batun: Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi