AL KITABU WAL ''ITRA'' KO AL KITABU WAS ''SUNNAH&#
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=763

 
DR MANSUR SOKOTO

AL KITABU WAL ''ITRA'' KO AL KITABU WAS ''SUNNAH''? 2

kashi na Uku shi ne hadisan da malamanmu suka yi sabani a kan ingancinsu ko rauninsu.

Ka'idarmu a nan ita ce hujja, ba Malam wane ya fada ba. Amma da zaran an samu haka sai su yi fararat su ce, ai Malaminku wane ya inganta shi. Daga nan sai su gina abinda shi malamin da an tambaye shi zai ce ba haka ne ba.

Idan mun zo fitar da Hadisin ''ITRA'' zamu ga wannan baro baro.

Kashi na Hudu shi ne hadisan da suke sukar mu a kansu, alhalin yadda suke a littafanmu haka suke a nasu. Kamar Hadisin fitsari a tsaye, da yawa sukan zage mu a kansa, su ce bamu san girman Manzon Allah ba, alhalin Hadisin yana a cikin littafansu su ma! Da kuma Hadisin cewa, ba a gadon Annabawa. A kullum sai ka ji suna zagin sayyidina Abubakar a kansa suna cewa ya shara ta, alhalin Majilisi da wasu Malamansu sun kawo shi ta nasu hanyoyi kuma sun inganta shi.
Kashi na Biyar shi ne irin hadisan da aka inganta su da lafazin da suka zo da shi ingantacce. Sai Malaman Shi'ah su kawo nasu lafazin mai rauni su ce mun inganta shi. In ka bi salsala zaka tarar lalle ya inganta amma ba a yadda suka kawo shi ba. Kuma nasun kitsa shi aka yi domin wata manufa.

Wani lokaci fa har sauyi na ganganci ake yi ma kalma a cikin Hadisi don ta dace da ma'anar da suke so. Kamar yadda suka yi da Hadisin '' ﺗﺮﻛﺖ ﻓﻴﻜﻢ ﻣﺎ ﺍﻥ ﺗﻤﺴﻜﺘﻢ ﺑﻪ ﻟﻦ ﺗﻀﻠﻮﺍ..'' Wannan ''bihi'' da ke cikin Hadisin sukan mayar da shi ''bihima'' kamar yadda zamu gani a nan gaba, don su batar da Ma'anar da Manzon Allah yake nufi su tabbatar da nasu son zuciya. Eh, ya zo da ''bihima'' amma karshensa ''Wa sunnati nabiyyihi'' ne, ba ''Wa itrati'' ba. Kamar yadda yake a cikin MUWATTA na Imam Malik tare da sharhinsa TANWIRUL HAWALIK (2/308). To, amma su sai su kalato wannan riwaya su yi mata kai da waccan.

A nan kuma zamu iya kawo wani hadisin da suke yawan hujja da shi '' ﻣﻦ ﻣﺎﺕ ﻭﻟﻢ ﻳﻌﺮﻑ ﺍﻣﺎﻡ ﺯﻣﺎﻧﻪ ﻣﺎﺕ ﻣﻴﺘﺔ ﺟﺎﻫﻠﻴﺔ'' Mu sam a wurinmu ba haka Hadisin yake ba. Ga yadda yake:

'' ﻣﻦ ﺧﻠﻊ ﻳﺪﺍ ﻣﻦ ﻃﺎﻋﺔ ﻟﻘﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ ﻻ ﺣﺠﺔ ﻟﻪ، ﻭﻣﻦ ﻣﺎﺕ ﻭﻟﻴﺲ ﻓﻲ ﻋﻨﻘﻪ ﺑﻴﻌﺔ ﻣﺎﺕ ﻣﻴﺘﺔ ﺟﺎﻫﻠﻴﺔ '' Banbancin da ke tsakanin wadannan ruwayoyi guda biyu ba karami ba ne. Nasu yana tabbatar da wata akida, namu kuma yana tabbatar da wata ta daban. Amma sai su kawo nasu su yi mana hujja da shi. Idan kana so ka kwatanta su sai ka duba namu a SAHIHU MUSLIM (6/22) hadisi na 4899 da kuma AS SUNAN AL KUBRA na Baihaqi (8/156) hadisi na 17055 sannan sai ka duba nasu a cikin AL KAFI na Kulini (1/377) da KASHFUL ASRAR na Khumaini, shafi na 197.

Bayan ka hakikance banbancinsu sai ka sake duba abinda Khomaini ya ce, wai wannan Hadisi sananne ne a wurin Shi'ah da Sunnah!!!

Haka hadisin khalifofi goma sha biyu Kuraishawa. Su kan dauko ingantattar ruwayarsa su buga ta da mai rauni sai su fitar da cewa Hadisin ya tabbata a yadda suke son kawo shi.

In sha Allahu zamu ci gaba.Batun: Al'Adun Musulmi Da Darajoji