MARABA DA WATAN RAMADAN [4]
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=769

 
FALALAR WATAN RAMADAN MAI ALBARKA !!!

MARABA DA WATAN RAMADAN [4]

•ALLAH mai girma da daukaka yace: "Waccan wata falala ce ta ALLAH yana bayar da ita ga wanda yaso, kuma ALLAH ma'abocin daukakar falala ne mai girma" .

(surah ta 62 aya ta 4)
Yana daga cikin abunda babu sa6ani a tsakanin malamai game da shi cewa lallai watan Ramadan watane mai alkhayri da albarka wanda ALLAH ya ke6ance shi da falala mai yawa, kamar yadda wannan bincike zai bayyana.

•ALLAH mai girma da buwaya ya sauqar da littafinsa a matsayin shiriya ga mutane da waraka ga muminai da hujjoji bayyanannu daga shiriya da kuma rabewa (tsakanin qarya da gaskia). Yana shiryarwa zuwa ga hujja mafi qarfi kuma da yana bayyana tafarkin shiriya. An sauqar dashi ne a daren LAILATUL QADRI daren daraja acikin watan Ramadan mai alkhairai.

•ALLAH (SWT) yana cewa: "Watan Ramadan ne wanda ALLAH ya sauqar da Alqur'ani a cikinsa yana shiriya da rarrabewar (gaskia da qarya) to wanda ya halarci watan daga cikin ku sai ya azumce sa.....
(surah ta 2 aya ta 185)
Sauqar da alqur'ani a wannan watan yana nuni ne akan falalar watan. Daure shaidanu da rufe qofifin wuta da bude qofofin aljanna wata dalala ce da ta ke6anci watan Ramadan.

•Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "idan Ramadan tazo ana bude qofofin aljannah kuma ana rufe qofofin wuta kuma ana daure shaidanu" .

(Tirmizi 682, Ibn majah 1642 daga Abu- hurairah)
kuma duk wannan aiki ana yin sane a farkon daren watan Ramadan .

•Annabi (SAW) yace:

"idan farkon daren watan Ramadan yazo ana daure shaidanu da kangararrun aljanu.

Kuma ana bude qofofin Aljannah ana rufe qofofin wuta ba a bude ko wace qofa daga cikinta, kuma ana bude qofofin aljannah ba a rufe ko wace qofa a cikinta, sannan sai wani mai qira yayi qira (cewa): "Ya kai mai neman alkhairi fuskanci aukin alkhayri kuma Ya kai mai neman aikata sharri ka taqaita (bari)
kar ka aikata! Kar ka aikata" kuma ko wani dare ALLAH yana 'yanta wadansu bayi daga wuta" .

(Bukhary 4/97, Muslim 1079)
Haka kuma samun daren LAILATUL QADRI a watan Ramadan wata falala ce wadda wannan watan kadai keda ita.

ALLAH (SWT)
Yace:"Lallai ne mun sauqar dashi (Alqur'ani)
acikin daren LAILATUL QADRI (daren daraja).

To me ya sanar da kai abunda ake cewa LAILATUL QADRI ?

Mala'iku da ruhi suna sauqa acikinsa, da izinin Ubangijinsu saboda ko wani umurni, aminci ne shi daren har fitar alfijir" .

(surah ta 97 aya ta 1 zuwa ta 5)
ALLAH YA DATAR DAMU DA ALKHAYRINSA (Ameen)
-Faridah Bintu Salis (Bintus-sunnah)Batun: Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen