MARABA DA WATAN RAMADAN [7]
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=772

 
SAHUR DA HUKUNCE- HUKUNCENSA

MARABA DA WATAN RAMADAN [7]

•SAHUR: Shine abincin da Musulmi ke ci a qarshen rabin kashin daren Azumi, kafin 6ullowar alfijir.

Annabi (SAW) yayi umurni da sahur domin bambantawa tsakanin Azuminmu da Azumin ma'abota littafi (Yahudu da Nasara)
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Banbancin Azuminmu dana ma'abota littafi (Yahudu da Nasara) shine cin abincin Sahur" (Dabarani 6127)
•FALALAR YIN SAHUR:

Akwai albarka cikin yin sahur, wannan kuma yazo a hadith masu yawa, daga cikinsu akwai Hadithin Salman (RA) Yace:

Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Ana sanya albarka acikin abubuwa guda 3:- daga cikinsu akwai sahur" (Dabarani 6127)
Da kuma Hadithin Abu- Hurayrah (RA) Yace:
Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Lallai ALLAH (SWT) Ya sanya albarka acikin sahur" .

wani Sahabin Annabi (SAW) Yace: Na shiga wurin Manzon ALLAH (SAW) a lokacin yana sahur, sai yace: "Lallai (shi sahur) albarka ce wanda ALLAH (SWT) Ya baku ita, kada kuyi wasa da ita" (Nasa'i 4/145, Ahmad 5/970).

Malamai sun tabbatar da cewa an so a jinqirta yin sahur sai kusan 6ullowar alfijir, saboda Manzon ALLAH (SAW)
da Zaid Bin Thabit (RA)
sunyi sahur lokacin da suka qare, sai Annabi (SAW) ya tashi zuwa sallar asuba yayi sallah.

Anas dan Malik ya ruwaito daga Zaid Bin Thabit (RA) yace: "Mun yi sahur da Manzon ALLAH (sAW) sannan ya tashi zuwa sallah, Anas Yacewa Zaid Ibn Thabit, daga qiran sallah zuwa sahur wani lokaci ne ke tsakaninsu?

Sai Yace: Gwargodon (Tsawon) karanta aya 50 (Hamsin)" (Bukhari 4/118, Muslim 1097).

•HIKIMAR YIN SAHUR:

1•Bambanta tsakanin Azumin Musulmi dana Yahudu da Nasara.

2•Yin kyakykyawan shiri domin fuskantar Azumi da rana.

3•Sahur sunnah ce mai qarfi kamar yadda ya tabbata a Hadithai ingantattu.

•HUKUNCIN YIN SAHUR:

Acikin hukuncin yin sahur akwai magana kashi biyu:

1•Sashen Malamai sun tafi akan cewa Sahur Mustahabbi ne (Abin so a shari'a) saboda Hadithai sun nuna haka:

Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Wanda duk zai yi azumi to idan yaso yayi sahur, da wani abu" (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi)
2•Wasu Malamai sun ce Sahur Sunnah ce mai qarfi, saboda Annabi (SAW) ya fada a wani hadith cewa: "ALLAH ne da kansa ya baku shi (Sahur) kada ku barshi" (Nasa'i 4/145, Ahmad 5/270)
Magana mafi rinjaye ita ce: Sahur Sunnar Annabi (SAW) ce mai Qarfi.

ALLAH YA BAMU IKON GABATAR DA IBADUN MU (Ameen).

-Faridah Bintu Salis (Bintus-sunnah)Batun: Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen