MARABA DA WATAN RAMADAN [8]
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=773

 
ABUBUWANDA AKA HALATTAWA MAI AZUMI !!!

MARABA DA WATAN RAMADAN [8]

Haqiqa saboda tausayin ALLAH (SWT) ga bayinsa, yana nufinsu da sauqi, baya nufin ya tsananta musu, saboda haka ne ya halatta wa mai Azumi wasu al'amura, kuma ya dauke masa laifi idan ya aikata su, ga wasu daga ciki:-

1• YIN ASWAKI GA MAI AZUMI: Aswaki yana cikin sunnar Annabawa, wanda Annabi (SAW)
yayi umurni da ita kamar yadda yace:

"Badon kar na tsanantawa al'ummata ba dana umurce su da yin Aswaki acikin alwala" (Bukhari 2/311, Muslim 202)
Abunda wannan hadith ke nunwa shine Manzon ALLAH (SAW) bai ke6ance mai azumi ba daga waninsa ba domin haka mai azumi da maras azumi duk zasu iya yin aswaki a kowace alwala.

2• WAYEWAR GARIN MAI AZUMI DA JANABA: Ya kasance Annabi (SAW) Alfijir na riskarsa alhali yana da janaba daga iyalinsa, sai yayi wanka bayan 6ullowar alfijir ya cigaba da azuminsa.
Hadisin Aisha (RA) ya tabbatar da haka da kuma Hadisin Ummu Salma (RA) sunce: "Lallai Manzon ALLAH (SAW)
Alfijir yana riskarsa alhali yana mai janaba daga iyalinsa, sannan yayi wanka, ya cigaba da azumi" (Bukhari 4/123, Muslim 1109)
3• KURKURAN BAKI DA SHAQA RUWA: Manzon ALLAH (SAW) Ya kasance yana kurkuran bakinsa, kuma yakan shaqa ruwa yana mai azumi, sai dai yayi hani ga mai azumi ya kai matuqa wajen wannan, saboda ya umurci wani mutum cewa:

"Ka shaqa ruwa sosai a wajen alwala sai dai, idan azumi kak yi" (Tirmizi 3/146, Abu- dawud 2/308, Ahmad 4/32)
wannan yana tabbatar mana da cewa kada mai azumi ya kai matuqa.

4• ZUBA RUWA MAI SANYI A JIKI DOMIN SANYAYA QISHIRWA:

Imam Bukhari (ALLAH Ya jiqansa) Yace acikin littafinsa:

Babi mai magana akan wankan mai Azumi, Yace: "Ibn Umar (RA) ya jiqa tufafinsa da ruwa, sannan ya sanyasu a jikinsa yana mai azumi" (Fat-hul Bari 4/153)
Haka kuma sha'abiy ya shiga gurin wanka yana mai azumi, kuma Hassan (RA) yace: Babu laifi ga kurkurar baki da yin wanka ga mai Azumi.

Kuma Manzon ALLAH (SAW) Yana zubawa kansa ruwa yana mai azumi saboda Qishirwa da tsananin zafi. (Abu- dawud 2365, Ahmad 5/376)
5• YIN QAHO: daga farko yin qaho yana cikin abubuwan da ke 6ata azumi, sai daga baya aka shafe wannan hukunci, saboda ya tabbata daga Annabi (SAW) cewa yayi qaho yana azumi.

Abdullahi dan Abbas (RA) Ya ruwaito cewa Lallai Manzon ALLAH (SAW) Yayi qaho yana mai azumi. (Bukhari 4/155)
6• DANDANON ABINCI GA MAI GIRKI: wannan babu laifi a kansa ga mai azumi sai dai da sharadin kada dandanon ya zarce cikin maqoshi.

Saboda abin da aka samo daga Abdullahi dan Abbas (RA) yace:

"Babu laifi ga mai azumi ya dandani wani abincin da ake dafawa kamar kunu ko wani abu, matuqar dandanonsa ba zai zarce zuwa maqoshinsa ba" (Bukhari 4/154)
ALLAH YA AMSA MANA IBADUNMU (Ameen).

-Faridah Bintu Salis (Bintus-sunnah).Batun: Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen