MARABA DA WATAN RAMADAN [13]
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=777

 
AZUMIN MATAFIYI !!!

MARABA DA WATAN RAMADAN [13]

MATAFIYI: shine wanda zai tashi daga wani gari zuwa wani gari, amma a zamanin Annabi (SAW) Matafiya suna kama hanyar tafiya ne da qafa ko akan wata dabba, amma a wannan Zamanin Matafiya suna tafiya ne a Mota ko a Jirgi wata motar ma hada AC.

ALLAH (SWT) Yace: "duk wanda ya kasance daga cikinku a halin rashin lafiya ko halin tafiya to sai ya qirga kwanakin da yasha Azumi domin ya rama daga baya, saboda ALLAH yana son sauqi gareku baya son ku da wahala ko tsanani" .

(Surah ta 2 aya ta 185)
•ZABI GA MATAFIYI:

Haqiqa Hadithai ingantattu sunzo da dama akan za6i ga matafiyi, ko yayi azumi ko yasha bayan Ramadan ya biya.
•Hamza Dan Amr Al- Aslamiyya (RA) ya kasance mai yawan azumi ne, sai ya tambayi Manzon ALLAH (SAW) Cewa: "Shin ko ina iya yin azumi acikin halin tafiya? Sai Manzon ALLAH (SAW) Yace masa: "Kayi Azumi idan kaga dama; kuma ka ajiye idan kaga dama" .

(Bukhari 4/156, Muslim 1121)
•Anas Dan Maalik ya ruwaito cewa: "Nayi tafiya tare da Manzon ALLAH (SAW) acikin watan Ramadan, daga cikinmu akwai masu Azumi Akwai wadanda basa azumi, kuma Manzon ALLAH (SAW)
bai aibanta mai azumi akan wanda baya azumi ba, ko wanda baya azumi akan wanda yake yi ba" .

(Bukhari 4/163-164, Muslim 118)
Wadannan Hadithai duk suna nuni ne akan za6i ba fifiko ba, sai dai mafi yawan Hadithai sun nuna fifita ajiye azumi alokacin tafiya, saboda cewar da Manzon ALLAH (SAW) Yayi:

"Lallai ALLAH (SWT)
yana son ayi aiki da rangwamenSa kamar yadda yake qyamar a aikata sa6onSa" (Ahmad 2/108, Ibn Hibban 2742 An kar6o daga Dan Umar R.A)
Malaman Hadith sun ruwaito cewa: Manzon ALLAH (SAW) Yace: "Ba ya daga cikin aiki mai nagarta yin azumi a lokacin tafiya" .

(Bukhari 4/161, Muslim 1115 An kar6o daga Jabir R.A)
•Abunda Malamai suka rairaye daga Hadithan da suka gabata shine, cewa idan Azumi zai wahalar lokacin tafiya to yinsa baya cikin nagarta, a wannan lokacin barinsa shi yafi a wurin ALLAH da ManzonSa kamar yadda yazo a Hadithin da ya gabata.

Idan kuma Mutum Yana iya yin Azumi ba tare da wata wahala ba, kamar yadda Hadithin Hamza Dan Amr da Hadithin Anas Dan Maleek suka tabbatar to babu laifi yayi azumi. ALLAH shine mafi Sani.

ALLAH YA AMSA MANA IBADUNMU (Ameen)
-Faridah Salis Umar.

(Bintu-sunnah)
Batun: Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen