MARABA DA WATAN RAMADAN [16]
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=780

 
FALALAR KWANA GOMA (10) NA QARSHEN WATAN RAMADAN !!!

MARABA DA WATAN RAMADAN [16]

Kwanakin watan Ramadan dukkansu akwai falala acikinsu, sai dai mafi falalarsu sune kwanaki 10 na qarshe. Saboda ayoyin Alqur'ani da Hadithai ingantattu sun zo da bayanin falalarsu. Daga cikin falalar wadannan kwanaki akwai:-

1• Acikinsu ne ake dacewa da daren Lailatul Qadr, ba a nemansa acikin sauran kwanaki face acikin kwana 10 na qarshen Ramadan, saboda Hadithin Aisha (RA)
tace:

Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Ku nemi Lailatul Qadr acikin marar kwanaki 10 na qarshen watan Ramadan" .

(Bukhari 4/225, Muslim 1169)
2• Lallai Manzon ALLAH (SAW) Ya himmantu kuma ya kula sosai da wadannan kwanaki 10 na qarshen watan Ramadan, saboda idan suka zo Manzon ALLAH (SAW) Yana daura gyautonsa (damara) ya dage da ibada ya nisanci iyalansa, yayi ta ayyukan alkhayri da Da'a zuwa ga Ubangijinsa a Masallacinsa.
Aisha (RA) tace:

"Manzon ALLAH (SAW)
Ya kasance yana yawaita qoqarin ibada a kwanaki 10 na qarshen Ramadan, irin qoqarin da baya yin irinsa a kwanakin da ba wadannan ba" .

(Muslim 1174)
3• Yana daga Falalarsa cewa duk wanda ALLAH (SWT) Ya azurta da tsayuwa acikinsa, wato sallolin dare da raya daren ta hanyar bautar ALLAH dayi masa Da'a, to ALLAH Ya yafe masa duk abunda ya gabatar na zunubansa da ya aikata, kamar yadda yazo a Hadith:

Manzon ALLAH (SAW)
Yace: "Wanda duk yayi tsayuwar daren Lailatul Qadr yana mai imani da ALLAH da kuma neman ladar Ubangiji to an gafarta masa abunda ya gabatar na zunubai" .

(Bukhari 4/217, Muslim 759)
4• Yana daga falalar wadannan Kwanaki 10 cewa i'itikafi baya kasancewa sai acikinsu, kamar Yadda Hadithin Aisha (RA) yazo, tace:

"Lallai Manzon ALLAH (SAW) Ya kasance yana yin i'itikafi a kwanaki 10 na qarshen watan Ramadan, kuma haka Manzon ALLAH (SAW)
Yake yi har ALLAH Ya kar6i rayuwarsa" .

(Bukhari 4/226, Muslim 1173)
Ya ALLAH ka bamu dacewa ka sanya mu daga cikin salihan bayinka masu tsayuwa akan bautarka da addininka (Ameen)
YA ALLAH KA AMSA IBADUNMU (Ameen).

-Faridah Bintu Salis.

(Bintus-sunnah)
Batun: Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen