AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA MARABA DA WATAN RAMADA N [17]
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=781

 
I'ITIKAFI DA HUKUNCE- HUKUNCENSA ....[1]

AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA MARABA DA WATAN RAMADA N [17]

•I'ITIKAFI: malamai sunyi bayanin ma'anar i'itikafi cewa shine tsayuwa akan wani abu, ta wannan ma'anar ne ake cewa wanda ya zauna masallaci yana ibada acikinsa, wanda ya ke6e domin bautar ALLAH (SWT).

•••HIKIMAR YIN I'ITIKAFI••• .

Haqiqa ALLAH (SWT) Ya shar'antawa bayinsa yin i'itikafi, wanda manufar hakan ita ce komawar zuciya ga ALLAH (SWT)
domin neman kusanci da neman yardarSa, Kuma ALLAH ne ke debewa mai i'itikafi kewa a lokacin da ya nisanci mutanen dake debe masa kewa domin zai ke6antu ne da ambaton ALLAH, kuma haqiqa ALLAH yana son masu ambatonsa.

•••ZAMAN I'ITIKAFI••• .

ALLAH (SWT) Yace:

"Kada ku yi mubashara (hada jiki) da mata alhali kuna masu yin i'itikafi a masallatai" .
(Surah ta 2 aya ta 187)
I'itikafi abun so ne, wato (Mustahabbi ne) a watan Ramadan da wanin watan Ramadan.

Domin ya tabbata cewa:

Manzon ALLAH (SAW)
Yayi i'itikafin kwanaki 10 na qarshen watan Shawwal" .

(Bukhari 4/226, Muslim 1173)
Kuma Ya tabbata cewa Umar Dan Khattab (RA)
yace wa Manzon ALLAH (SAW): "Ya Manzon ALLAH (SAW) lallai ni a lokacin jahiliyya nayi alwashin yin i'itikafin dare daya acikin masallacin makkah. Sai Manzon ALLAH (SAW)
yace wa Umar (RA) to sai ka cika alwashin da kayi, domin haka sai Umar (RA) yaje Makkah yayi i'itikafin dare daya a masallaci mai alfarma" .

(Bukhari 4/237, Muslim 1656).

Amma mafificiyar i'itikafi shine i'itikafin watan Ramadan, saboda Hadithin Abu- Hurayrah (RA) da yace:

Manzon ALLAH (SAW)
Ya kasance yana yin i'itikafi na kwanaki 10 acikin ko wane watan Ramadan, amma yayi i'itikafi na kwana 20 a shekararsa ta qarshe wanda ALLAH (SWT) Ya kar6i rayuwarsa acikinta" .

(Bukhari 4/225)
Aisha (RA) tace: Manzon ALLAH (SAW) Ya kasance yana i'itikafi a kwanaki 10 na qarshen watan Ramadan har ALLAH Ya kar6i rayuwarsa" .

(Bukhari 4/226, Muslim 1173).

ALLAH YA BAMU IKO, YA KUMA AMSA MANA IBADUNMU (Ameen)
-Faridah Bintu Salis.

(Bintus-sunnah)Batun: Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen