AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA MARABA DA WATAN RAMADA N [18]
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=782

 
I'ITIKAFI DA HUKUNCE- HUKUNCENSA ....[2]

AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA MARABA DA WATAN RAMADA N [18]

SHARUDAN I'ITIKAFI

1• MASALLATAI: Yin i'itikafi baya inganta sai acikin masallatai.

Saboda ALLAH (SWT)
Yace: "Kada ku yi mubashara da mata alhali kuna masu i'itikafi acikin masallatai" .

(surah ta 2 aya ta 187)
Amma ba kowane masallaci ake i'itikafi acikinsa ba, domin yazo acikin Hadith cewa:

"Babu i'itikafi (cikakke)
sai a masallatai uku" wato Masallacin Makkah, Masallacin Qudus da Masallacin Madina" (Hadith ne ingantacce malamai sun inganta shi)
Amma wannan Hadith ba yana kore yin i'itikafi bane acikin wanin wadannan masallatai bane, sai dai yana kore cikar ladar i'itikafi a wani masallacin na daban.

2• MUSULUNCI: sharadi ne mai i'itikafi ya kasance musulmi domin ba'a kar6an i'itikafin Kafiri.
3• HANKALI: Dole ne mai i'itikafi ya zamo mai hankali domin ba a kar6ar ibadar Mahaukaci.

4• BALAGA: Wanda zai yi i'itikafi ya zamanto mutum ne wanda hukunce-hukuncen addinin musulunci ke gudana akansa, kuma masani akan addini kuma masani akan i'itikafi da mas'alolinsa.

5• NIYYA: Dole ne mai i'itikafi zai tsarkake Niyyarsa domin ALLAH (SWT) Ya zamanto ba domin Riya ba.

••• ABUBUWANDA SUKA HALATTA GA MAI I'ITIKAFI ••• .

1• Ya halatta ga mai 'i'itikafi ya fita daga masallaci saboda wata buqata ta shari'ah.

Saboda Aisha (RA) tace:

"Manzon ALLAH (SAW)
Ya kasance yana shigar da kansa gare ni yana i'itikafi a masallaci ina cikin dakina, na taje masa shi, a wata Riwayar kuma "In wanke masa kansa" kuma ya kasance a lokacin i'itikafi baya shiga cikin gida sai domin wata buqata ta dan adam" .

(Bukhari 1/342, Muslim 297)
2• Ya Halatta ga mai i'itikafi yayi alwala a masallaci amma alwala sassauqa, amma yin hakan ya zama baya kawo qazanta a masallaci ko cutarwa ga jama'a. Hadith Yazo cewa: "Manzon ALLAH (SAW) Yayi alwala sassauqa a masallaci" .

(Ahmad 5/364)
3• Mai i'itikafi yana da damar sanya shimfidarsa a masallaci, dominan samu daga Hadith, Manzon ALLAH (SAW) Ya kasance idan zai shiga i'itikafi ana kai masa shimfidarsa a masallaci, a bayan wani ginshiqi daga cikin ginshiqan masallaci" .

(Ibn Majah 642)
4• Fita daga cikin Masallaci zuwa wurin wanka amma idan babu wurin wanka a masallacin, to mai i'itikafi yana da damar zuwa duk yake domin yin wanka saboda lalura ce. Saboda Hadithin Aisha (RA) tace:

"Manzon ALLAH (SAW)
Ya kasance baya zuwa gida idan yana i'itikafi sai domin wata buqatar dan adam" .

(Bukhari 1/342, Muslim 297)
ALLAH YA AMSA MANA IBADUNMU (Ameen)
-Faridah Bintu Salis.

(Bintus-sunnah)Batun: Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen