AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA MARABA DA WATAN RAMADA N [19]
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=783

 
I'ITIKAFI DA HUKUNCE- HUKUNCENSA ....[3]

AZUMI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA MARABA DA WATAN RAMADA N [19]

ABUBUWANDA BAYA HALATTA GA MAI I'ITIKAFI

1• JIMA'I: Yin jima'i da sumbatar mace da wasa da ita baya halatta ga mai i'itikafi da dare ko da rana, idan kuma har hakan ya faru to i'itikafin ya 6aci, saboda hani akan wannan yazo cikin alqur'ani mai girma, ALLAH (SWT) Yana cewa: "kada kuyi mubashara da mata alhali kuna masu i'itikafi acikin masallatai" .

(Surah ta 2 aya ta 187)

2• FITA DOMIN GANIN MARAR LAFIYA: Ba ya halatta ga mai i'itikafi ya fita zuwa ganin marar lafiya a gida ko a asibiti.

3• JANA'IZA: Ba ya halatta ga mai i'itikafi ya halarci sallar gawa sai dai idan sallar gawar ta kasance acikin masallacin da yake i'itikafi ne to zai iya yin sallar gawar tare da Liman. Kar ya fita sai fitar da bata da makawa, saboda Aisha (RA) tace:

"Abunda yake sunnah ga mai i'itikafi kar ya gaida marar lafiya, kar ya halarci jana'iza (sallar gawa) kar yayi jima'i da mace, kuma kar ya shafeta shafar jin dadi" .

(Abu-dawud ya fitar dashi)
4• YASASHSHIYAR MAGANA: Baya halatta ga mai i'itikafi ya shagaltu da wasa da yasassun maganganu a lokacin ibadarsa da ko wane lokaci, saboda Nassin AlQur'ani yayi hani akan wadannan abubuwa, kuma babu fa'ida ta duniya ko ta lahira acikinsu.

5• GIBA DA ANNAMIMANCI: Yin giba da yawo da Annamimanci da sauransu basa halatta ga mai i'itikafi, saboda Giba da Annamimanci Dabi'u ne wadanda ALLAH (SWT) da Manzon ALLAH (SAW)
suka haramta, kamar yadda yazo acikin alqur'ani:

(Surah ta 49 aya ta 12 da kuma Surah ta 68 aya ta 10 zuwa ta 11).

LOKUTAN YIN I'ITIKAFI

Malamai sunyi sa6ani game da mafi qarancin lokacin yin i'itikafi.

Amma Mafi Yawan malamai sun tafi akan cewa mafi qarancin i'itikafi shine dare da yini, dalilinsu shine Hadithin Umar (RA)
wanda ya gabata.

JAN HANKALI

Mutanen mu na wannan zamanin basa bawa i'itikafi muhimmanci da yawa daga cikinsu suna tafiya masallatai da sunan i'itikafi amma sai suje suyita qiran mutanen su a wayoyi alhali suna ikirarin suna i'itikafi wannan ba daidai bane yin hakan wulaqanta bautar ALLAH (SWT) ne.

Da wannan nake jan hankali al'ummar musulmai idan zasu yi i'itikafi su tsarkake Niyyar su, su gabatar dashi domin ALLAH ba tare da sanya wasa acikinsa ba.

ALLAH YASA MU DACE, ALLAH YA AMSA MANA IBADUNMU (Ameen)
-Faridah Bintu Salis.

(Bintus-sunnah)Batun: Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen