TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH FALALAR SAHABBAI
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=789

 
SHEIKH ABDULWAHHAB ABDULLAH

TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH FALALAR SAHABBAI

Alhamdu lillahi rabbil A'lamin, wa Sallallahu wa sallama ala Nabiyyina Muhammadin Wa ala a'alihi wa sahbihi ajma'in.

Amma ba'ad, hakika hadisi ya tabbata daga Anas Bin Malik radhiyallahu anhu ya ce; ﻛﺎﻧﺖ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺨﻨﺪﻕ ﺗﻘﻮﻝ ﻧﺤﻦ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺑﺎﻳﻌﻮﺍ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ ﻣﺎ ﺣﻴﻴﻨﺎ ﺃﺑﺪﺍ ﻓﺄﺟﺎﺑﻬﻢ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻻ ﻋﻴﺶ ﺇﻻ ﻋﻴﺶ ﺍﻵﺧﺮﻩ ﻓﺄﻛﺮﻡ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻭﺍﻟﻤﻬﺎﺟﺮﻩ Ma'ana Ansar sun kasance a yayin da suke haka ramin khandaku suna cewa;
''Mu ne wadanda suka yiwa Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama mubaya'a akan jihadi muddin muna raye har abada''. Sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ce; ''Ya Ubangiji babu wata rayuwa sai rayuwar lahira.

Ya Allah ka girmama Ansar da muhajirai'' 'Yan uwa wannan ya nuna bai halatta wani mutun ya zagi sahabbai wadan suke kaunar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama shima yake kaunarsu ba, duk wanda ku ka ji yana zaginsu ku Sani wannan tababbe ne, yayi asara duniya da lahira.

wa Sallallahu wa sallama ala Nabiyyina Muhammadin Wa ala a'alihi wa sahbihi ajma'in.Batun: Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar