IMANI DA RASSAN SA GUDA 67, NAWA KAKE DA SU A CIKI.?
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=794

 
DAGA SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

IMANI DA RASSAN SA GUDA 67, NAWA KAKE DA SU A CIKI.?

Manzon Allah saw yace: Imani yana da rassa guda Sitttin bakwai , ko sabain da bakwai, mafi daraja, shine ,Lailaha illalahu, mafi karanta dauke abu mai cutarwa daga hanya, kunya tana daga cikin imani. Muslum ya ruwaito Malamai sunyi bincike domin gano wadannan rassa, sun wallafa littafai da dama akan haka, abinda suka kawo, daga Alkur'ani mai girma, da ingatattun hadisai, kuma sun gaya mana cewa wadannan rassa sun fito daga aiyukan zuciya, da aiyukan harshe, da aiyukan gabbai, kuma imani yana karuwa yana raguwa.

1- Imani da Allah, shi yayi halitta, shi ya mallaka. shi yake gudanarwa.shi ya cancanci bauta. Da sunayansa da siffofinsa.

2- Imani da Mala'ikun Allah, da siffofin su da aiyukan su, da sunayansu.

3- Imani Da Manzannin Allah swt.

4- Imani da littafan Allah swt, 5- Imani da ranar Lahira.

6- Imani da kaddara mai dadi da mara dadi.
7- Imani da tashi bayan mutuwa 8- Imani da tattaruwa a gaban Allah domin hisabi 9- Imani da Aljannah da Wuta.

10- Kaunar Allah, 11- Tsoran Azabar Allah 12- Kauna juna da Fatan samun rahmar Allah 13- Wajabcin dogaro ga Allah 14- Wajancin Kaunar Manzon Allah saw.

15- Wajabcin girmama Manzon Allah saw.

16- kula da addinin sa da kishinsa.

17- Wajabcin Neman Ilmi.

18- Yada ilmi da koyarwa.

19- Girmama Alkur'ani karatunsa, fassararsa, aiki dashi 20 -wajabcin yin tsarki,na wanka da alwala da taimama.

21- Kula da salloli,biyar akan lokaci.

22- Fitar da zakka, ga wadanda suka cancanta.

23- Azumin Ramadan.

24- Shiga i'itikafi, sunnah ne, yana kara imani 25- Aikin Hajji, sau daya wajibi, komawa sunnah.

26- Jihadin kare addini da yadashi, bisa ilmi.

27- Rashin gudu daga filin daga idan ana yaki.

28 – Bayar da daya bisa biyar, ga abinda mutum ya samu na Rikazi, wato ( tono kudi a kasa)
29- Fitar da kaffara idan ta hau kan mutum, na kisa ko rantsuwa, ko zihari, ko karya azumi da gangan 30- Cikawa da Alkawari idan an dauka.

31- Rikon Amana 32- Godiya ga ni'imar Allah da rashin butulci.

33- Kiyaye harshe, fadin alkhairi ko shiru 34- Tsare kafofin musulunci, kamar (media) wanda ya taba addini a mayar masa da martani.

35- kada mutum ya kashe kansa. Ta ko wacce hanya 36- kamai mutunci, 37- Nisantar cin Haram 38- Tuba daga laifuffuka.

39 Bin sunnah sau da kafa da zuciya 40- Yin aiki da lklasi (ayi aiki don Allah kawai)
41- Hakuri, da rashin zalama 42 – Tausayi da jin kai 43- Tawali'u da kan-kan da kai 44- Zuhdu, gudun duniya, da abin hannun mutane 45- Girmama Manya da tausayawa na kasa.

46- Yawan Addua 47, Yawan Zikri 48, yawan salati ga Annabi saw.

49, Yawan Kyauta da alkhairi 50, Yawan Istigfari 51, sada zumunta 52, Biyayya ga iyaye.

53, Tarbiyyar y'ay'a 54, Kula da hakkin iyali.

55, Biyyaya ga na gaba cikin bin Allah.

56, Tsayar da adalci, ga masoyi da makiyi 57, Yin Sulhu tsakanin Jamaa 58, Umarni da kyakyawa da hani da mummuna 59, Yin Gaskiya 60, Neman kudi ta hanyar halal 61, Yin sallama da amsa sallama 62, Bayan da rancan kudi babu ruwa 63, Girmama bako 64, Amsawa mai atshawa 65, Taimakekiniya wajan aikin alkhairi.

66, Dauke abinda zai cuci mutane daga hanya.

67, ka fifita dan uwanka akanka ko kana da bukata.

Allah ya bamu ikon aikatawa.Batun: Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen