HAKKOKIN MUSULMAI A KAN JUNANSU
 
Wannan Labari Ya fito Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
URL na Wannan Labari Shine:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=801

 
DR. MANSUR SOKOTO

HAKKOKIN MUSULMAI A KAN JUNANSU

Hakika Allah ya umurci Musulmai da hadin kai wajen tsayar da Addini, Allah ya ce:

13] "Ku tsayar da Addini kada ku rarraba a cikinsa".

Sai Allah ya hanesu ga rarrabuwa. Kuma wannan shi ne abin da ya shar'anta mana, kuma ya yi wasiyyansa ga Shugabannin Manzanni; Muhammad (saw), Ibrahim (saw), Musa (saw), Isa (saw), Nuhu (saw).

– Kuma Allah ya hanesu a kan sabani, inda ya ce:

46] "Kada ku yi jayayya a tsakaninku sai ku karaya, karfinku ya kare".

– Kuma ya umurcesu da taimakekeniya, inda ya ce:
"Ku taimaki juna a kan aiyukan alheri, da jin tsoron Allah".

Wannan ya sa Shari'a ta ba mu labarin cewa; musulmai suna da hakkoki a kan junansu, kuma ta yi kira ga a kula da su, kuma a kiyayesu, don al'ummar musulmi ta zama al'umma mai karfi da hadin kai, mai tausayin juna, wacce tsaro da zaman lafiya zai jagoranceta.

* Daga cikin hakkokin musulmi a kan dan uwansa musulmi akwai:

1. Kada ya ZAGE shi, ko ya TSINE masa, kuma kada ya FASIKANTAR da shi, ko ya KAFIRTA shi.

– Annabi (saw) ya ce:

« ﺳﺒﺎﺏ ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ ﻓﺴﻮﻕ ﻭﻗﺘﺎﻟﻪ ﻛﻔﺮ» "Zagin musulmi FASIKANCI ne, yakarsa kuma KAFIRCI ne".

– Kuma ya ce:

« ﻻ ﻳﺮﻣﻲ ﺭﺟﻞ ﺭﺟﻼ ﺑﺎﻟﻔﺴﻮﻕ، ﻭﻻ ﻳﺮﻣﻴﻪ ﺑﺎﻟﻜﻔﺮ، ﺇﻻ ﺍﺭﺗﺪﺕ ﻋﻠﻴﻪ، ﺇﻥ ﻟﻢ ﻳﻜﻦ ﺻﺎﺣﺒﻪ ﻛﺬﻟﻚ » "Babu mutumin da zai jefi wani mutum da fasikanci, ko ya jefe shi da kafirci face kalmar ta dawo kansa, in wancan mutumin nasa bai kasance hakan ba".

– Kuma du ya ce:

« ﻭﻟﻌﻦ ﺍﻟﻤﺆﻣﻦ ﻛﻘﺘﻠﻪ، ﻭﻣﻦ ﺭﻣﻰ ﻣﺆﻣﻨﺎ ﺑﻜﻔﺮ ﻓﻬﻮ ﻛﻘﺘﻠﻪ » "Tsine wa mumini kamar kashe shi ne, duk wanda ya jefi mumini da kafirci kamar ya kashe shi ne".

Ma'ana; tsine masa haramun ne kamar yadda kisansa haramun ne, kuma dadai suke a zunubi.

Saboda haka wajibi ne a kan kowane musulmi ya san wannan hakki da yake kansa, kuma ya kiyaye shi a kan dan uwansa musulmi, don a zama al'umma guda daya, kamar yadda Allah yake so, kuma ya yi umurni.

– Aliyu Sani


 

Batu: Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin


Comments 💬 التعليقات