ZUMUNCI DA WAJABCIN SADARDA SHI
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=805

 
ZUMUNCI DA WAJABCIN SADARDA SHI

ALLAH SUBHANAHU WA TA'ALA YACE:- Ku baiwa makusanta hakkinsu da miskinai da matafiyi, kada kuyi almubazzaranci, Almubazzaranci.

《Suratul isra'i》

MANZON ALLAH SAW YACE:- Wanda duk ya kasance yayi imani da Allah SWA da ranar karshe, yasadar da zumuncinsa.

《Muslim》

MANZON ALLAH SAW YACE:- Mai yanke zumunci bazai shiga aljannaba.

《Bukhari da muslim》

MANZON ALLAH SAW YACE:-
Wanda duk ya kasance yana da ''yan uwa masu rauni, amma bai sadar garesuba kuma ya bayarda sadakarsa izuwa ga wasu, Allah baZai karbi sadakarsaba, kuma baZai kallesu ba ranar alkiyama.

《Dhabarani》

A cikin wadannan hadisan zamu fahinci cewa wajibine akan kowane dayanmu a sadarda zumunci zuwa ga ''yan uwansa makusanta kamar kanni ko yayyin mahaifi da mahaifiya, ''yan uwanka na jini, dangika da sauran abokan arziki.

★Sannan zamu fahimci cewa wajibine akan mutukar muna da dukiya mu taimakama talakawa daga cikin danginmu ka wadansu .

★ Sannan kada mu dauka idan bamu da abinda xamu baiwa wanda zamu ziyarta hakan yana nufin kada muyi ziyara, Haka kuma kada mai dukiya ya dauka ana ziyartarsane saboda abin hannunsa.

★DAGA KARSHE YAN UWA MUJI TSORON ALLAH MU DUKA, MUJI TSORON WUNIN DA ZA'A FITAR DAMU ACIKINSA SANNA A SAKAWA KOWACE RAI ABINDA TA AIKATA KUMA BAZA'A ZALUNCE TABA. YA HAYYU YA QAYYUM KA TSAREMU DAGA SHARI KAWUNANMU.★ ★Jumullar hadisan suna cikin littafin bugyatull muslim na shaykh usman bin abubakr bamakki.★ 。 ★★Dan Uwanku★★ ★★Abubakar Nuhu Koso★★ ★Abu Abdullah Assunney★Batun: Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi