KANASON ALJANNAH CIKIN SAUKI??
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=809

 
Abdullahi Muhammad Auwal

KANASON ALJANNAH CIKIN SAUKI??

TO GA MAFITA...

Manzon Allaah sallallaahu alaihi wasallam yana cewa:

A wani hadisin kuma yana cewa:

Ma'ana: (Duk wanda yabi wata hanya ko ya ri'ki wata hanya wanda yike neman ilmi a cikinta; to Allaah zai sau'ka'ke yakuma yassare mishi da wannan ilmin hanya zuwa Aljannah).

Wannan hadisin ya nuna mana girma da falala da ilmi ke dashi, daga cikin falalar – wadda kuma itace mafi girma – shine samun Aljannah.
Sai dai wannan hadisin yana maganane akan ilmi na shari'ah kamar yadda wasu malaman suka fassarashi tareda wasu nassoshin Qur'ani da hadisi, sai dai duk wani ilmi mai amfani wanda shari'ah ta yarda dashi shima zai iya shiga karkashin wannan hadisi mai girma kamar yadda wasu malaman suka nuna hakan.

Amma mutum bazai samu wannan falalar ba, sai da sharudda kamar haka:

1- Yi dan Allaah.

2- Bin dokokin Allaah a cikinsa.

3- Aiki da ilmin.

4- Kokarin amfanar da al'ummah da ilmin.

MUNA FATAN ALLAAH YASA MUNA CIKINSU, WADANDA KUMA BASU KAMA HANYAR ILMI BA ALLAAH YASA SUGANE.Batun: Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar