MATSAYIN MUSULMI A WAJEN 'YAN SHI'A
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=811

 
DR. UMAR LABDO

MATSAYIN MUSULMI A WAJEN 'YAN SHI'A 

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ 
Gabatarwa Lallai godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman taimakonsa, muna neman gafara tasa.

Muna neman tsari da Allah daga sharrin kawunanmu da miyagun ayyukanmu.

Wanda Allah ya shirye shi, babu mai batar da shi kuma wanda ya batar babu mai shiriya tasa. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai, ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa Muhammad bawansa ne, kuma Ma'aikinsa ne. Tsira da aminci su tabbata a gare shi, da Alayensa, da Sahabbansa, da waxanda suka bi Sunnarsa har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka, 'yan Shi'a suna yawan yin magana dangane da hadin kan Musulmi. Ba sa barin wata munasaba ta wuce ba tare da sun maimaita kira izuwa hadin kai ba, da sukan rarraba da karkasuwa zuwa kungiyoyi da mazhabobi.

Sau da yawa sukan yi kira da hadin kai tsakaninsu da Ahalus Sunna, suna masu karfafa cewa bai kamata a samu sabani ba domin hakan yana raunana Musulmi a gaban abokan gabansu. A wasu lokuta sukan nuna cewa abubuwan da suka raba su da Ahalus Sunna ba wasu muhimmai ba ne, kuma su da Ahalus Sunna duka abu guda ne tunda Shi'a ita ma mazhaba ce kamar sauran mazhabobi.
A wasu kasashe, 'yan Shi'a suna kira da abinda suke wa laqabi da Attakrib bainal Mazahib, ko kuma Atta'aruf, watau kusantar da mazhabobi ga junansu ko kuma fahimtar juna, suna nufin kusanci da fahimtar juna tsakanin tafarkin Shi'a da na Sunna.

A nan Nijeriya kuwa, mun san su da kirarin Islam One, wanda suke bin gine- ginen hukuma kamar makarantu da ofisoshi suna rubutawa, wai suna nufin Musulunci daya ne, babu bambanci tsakanin wani tafarki da wani, ko kuma wata mazhaba da wata.

Amma mene ne hakikanin abinda 'yan Shi'a suka dauki mai bin tafarkin da ba nasu ba, musamman Ahalus Sunna? Shin gaskiya ne suna daukar dukkan Musulmi daya ne, ko kuwa kawai yaudara ce suke yi don su samu karbuwa a wajen mutane?

Mene ne abinda manyan malaman Shi'a suke fadi dangane da Ahalus Sunna, da sauran Musulmi duka, a da da kuma yanzu? Shin sun yarda su Musulmi ne kamar yadda su ma suke da'awar Musulunci, ko kuwa suna daukar su dabam? Ya suka dauki imaninsu da sallarsu da azuminsu da hajjinsu da yankansu da auratayyarsu da sauran ma'amalolinsu da ayyukansu na addini?

Wannan dan karamin littafi zai yi kokarin amsa wadannan tambayoyi, da ma wasunsu, in Allah ya yarda, kuma amsoshin duka za su fito kai tsaye daga bakin manyan malaman 'yan Shi'a, ta hanyar littafansu waxanda suka yarda da su. A qarshe mai karatu zai fita da sahihiyar fahimta ta matsayin Ahalus Sunna, da sauran Musulmi, a wajen 'yan Shi'a ta yadda zai yi hukunci da kansa a kan wannan da'awa ta Rafilawa ta kira zuwa ga hadin kai da kusanto da mazhabobi da fahimtar juna idan gaskiya ce ko kuwa qarya ce da yaudara.

Manufarmu a nan, in Allah ya yarda, ita ce bayanin gaskiya da sauke nauyin da yake kanmu na al'ummarmu, don wanda ya halaka ya halaka a bisa sani kuma wanda ya shiriya ya shiriya a bisa sani. Kuma gamon katarinmu bai zamo ba sai ga Allah, a gare shi muke dogara, kuma gare shi muke komawa.Batun: Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi