MATSAYIN MUSULMI A WAJEN 'YAN SHI'A - 2
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=812

 
DR. UMAR LABDO

MATSAYIN MUSULMI A WAJEN 'YAN SHI'A - 2

Babi Na daya Ma'anar Ahalus Sunna A Wajen Rafilawa Mai karatun littafan Shi'a zai lura da wasu sunaye, ko kuma laqabai, da suke kiran Ahalus Sunna da su.

Wadannan lakabai suna cikin littafan malamansu na farko da malamansu na zamani. Ba safai sukan kira su da sunan Ahalus Sunna ba sai nadiran. Sunayen dukkaninsu suna nuna kazafi da vatanci da wulakanci. Zai yi kyau mu fara bayani da wadannan sunaye kafin mu shiga magana a kan ma'anar Ahalus Sunna a wajen Rafilawa.

Sunayen Ahalus Sunna A Wajen 'Yan Shi'a Akwai sunaye guda uku da Rafilawa suke amfani da su don ambaton Ahalus Sunna a cikin littafansu da maganganunsu wadanda suka hada da hudubobinsu da laccocinsu da wa'azozinsu.

Wadannan su ne:

1. Nasibawa. Asalin sunan da Larabci nasib, jam'insa nawasib, watau mai kulla gaba, ko wanda ya kafa kiyayya. Abinda suke nufi gaba da kiyayya ga Ahalul Baiti, musamman Ali binu Abi Dalib da Fadima, Allah ya kara musu yarda, da kuma imamai goma sha biyu daga zuri'arsu.
Wannan suna shi ne mafi muni kuma mafi yaduwa a tsakaninsu wanda suke ambaton Ahalus Sunna da shi.

Malaminsu mai suna Hussain Aali Usfur Addarazi Albahrani, yana cewa, ''Al'ada ta gudana, kai har ma da hadisan imamai, a kan cewa nasibi shi ne wanda a wajensu suke kira Sunni.''[1] A wajensu, yana nufin a wajen Ahalus Sunna.

Amma su a nasu wajen nasibawa suke ce da su.

Dubi yadda ya yi nuni ga Ahalus Sunna da lamirin ''su'' domin ya bambance su da ''mu'' wanda a zancensa yake nufin 'yan Shi'a. Wannan kawai ya isa ya nunawa mai karatu yadda dan Shi'a yake daukar kansa da Ahalus Sunna; watau abin mu ne da su.

Malamin Shi'a na wannan zamani wanda ya shahara da tsaurin kai, Muhammad Tijjani Samawi, yana cewa, ''Abu ne da ba ya bukatar a fadi cewa mazhabin nasibawa shi ne mazhabin Ahalus Sunna wal Jama'a.''[2] Haka yake kamar yadda malamin ya fadi. Wannan abu ba ya bukatar a fadi saboda ya shahara a tsakanin Rafilawa kuma a cikinsu babu mai ja a kai.

2. Amawa. Wannan shi ne suna na biyu da Rafilawa ke kiran Ahalus Sunna da shi. Asalinsa da Larabci aami, jam'insa awaam, watau gama-gari, ko tarkacen mutane. Kuma sunan kishiyar lafazin khaas ne (jam'insa khawaas), wanda yake nufin na musamman, ko na-gari. Watau 'yan Shi'a su ne na musamman, masu nagarta, Ahalus Sunna kuwa tarkace, gama-gari. Daga cikin malaman Shi'a da suka yi amfani da wannan suna akwai Alhurrul Amili wanda ya rubuta wani babi mai taken ''Babin Hani Ga Barin Riko Da Abinda Ya Dace Da Amawa'' a cikin littafinsa mai suna Alfusulul Muhimma. A qarqashin wannan babin, ya ruwaito imaminsu na shida, Ja'afar Sadik, yana cewa idan aka samu hadisai guda biyu masu karo da juna, to a dauki wanda ya saba wa ra'ayin Amawa, a kyale wanda ya dace da su.[3] 3. Suna na uku shi ne Jumhur. Wannan suna haka yake ko a Larabci, kuma ba shi da tilo sai jam'i kawai. Ma'anarsa ta yi kama da gama-gari koda yake a wani yayi yana nufin agalabiya, watau mafiya yawa, masu rinjaye, ko kuma majorati, kamar yadda ake fadi da kalmar Turanci ta aro.[4] Wadannan sunaye su ne 'yan Shi'a suke amfani da su wajen ambaton Ahalus Sunna a cikin littafansu, maganganunsu, laccocinsu da hudubobinsu. Kuma ma'anarsu a fili take; suna nuna yadda 'yan Shi'a suka dauki masu bin tafarkin Sunna a matsayin abokan gaba masu kiyayya ga imamai, bare waxanda ba na gida ba, kuma koma- baya wadanda suke gama-gari ne su, tarkace.

Banda wadannan sunaye, akwai wasu lafuza da malaman Shi'a ke amfani da su domin nuni ga duk wani Musulmi wanda ba ya bin tafarkinsu, wanda yana iya hadawa da Ahalus Sunna da wasunsu.

Waxannan sun haxa da almukhalif, watau mai saba mana, da gairuna, watau waninmu, da munafiq, watau munafiki, da sauransu.

Ma'anar Ahalus Sunna A Wajen 'Yan Shi'a Amma idan muka koma ga haqiqanin ma'anar Ahalus Sunna a wajen 'yan Shi'a, to sai mu ga cewa sun gina ta a kan abubuwa uku.

1. Abu na farko: Fifita wanin Ali binu Abi Dalib (RA) a kansa. Dangane da wannan ma'ana ne malaminsu dan hayaki, Ni'imatullahi Aljaza'iri, yake fadin wai, ''An ruwaito daga Annabi(SAW)
cewa alamar nasibawa ita ce gabatar da wanin Ali a kansa.''[5] Watau wanda ya ce wani Sahabi ya fi Ali, ko yana gaba da shi a wajen daraja da falala, ko shi ne Khalifa na farko ba Ali ba, to wannan ya zama nasibi. Babu shakka Ahalus Sunna suna ganin cewa Abubakar da Umar da Usman suna gaba da Ali a wajen falala da fifiko da kuma jerin khalifanci.[6] Kai a cikin kungiyoyin Musulunci ma kaf, ba mai fifita Ali a kan Abubakar da Umar sai 'yan Shi'a (koda yake an samu wasu wadanda suka fifita shi a kan Usman). Saboda haka a kan wannan, duk wanda ba dan Shi'a ba nasibi ne ke nan.

2. Abu na biyu: Yarda da amincewa da khalifancin Abubakar da Umar, Allah ya kara musu yarda.[7] Watau ko da mutum bai fifita su ba, idan dai ya yarda da cewa su khalifofi ne, to ya zama nasibi.

3. Abu na uku: Jibintar Jibtu da Dagutu, kamar yadda suke fadi.[8] Abinda suke nufi da Jibtu da Dagutu su ne Abubakar da Umar, Allah ya kara musu yarda. Watau ba fifita su ba, ba yarda da khalifancinsu ba, ko jibintar su ma kawai, watau son su da daukar su a matsayin 'yan uwa Musulmi, yana mai da mutum nasibi.

Yana daga cikin akidun Rafilawa sanannu cewa mutum ba ya zama Musulmi sai ya barranta daga Abubakar da Umar da manyan Sahabbai tare da su, kuma ya barranta daga duk mai son su, ko jibintar su. Babban malaminsu, Muhammad Bakir Almajalisi, ya tabbatar da wannan aqida tasu inda yake cewa, ''Akidarmu ta barranta ita ce cewa mu muna barranta daga gumaka hubu: Abubakar da Umar da Usmanu da Mu'awiya; da mataye hudu: A'isha da Hafsa da Hindu da Ummul Hakam; kuma muna barranta daga dukkan mabiyansu da magoya bayansu; kuma muna kudure cewa su ne mafiya sharrin halittar Allah a bayan qasa; kuma cewa imani da Allah da Manzonsa da imamai ba ya inganta sai an barranta daga makiyansu.''[9] Daga wadannan bayanai da suka gabata zai bayyana a fili cewa a ganin 'yan Shi'a duk wanda bai kudure aqidarsu ba ta cewa Ali binu Abi Dalib shi da 'ya'yansa su kadai su ne khalifofi, ko imamai, kuma cewa Abubakar da Umar da Usmanu ba wai kawai su ba khalifofi ba ne a'a su kafirai ne gumaka, wanda duk bai kudure wannan akida ba to shi ne nasibi kuma imaninsa da Allah da Manzo bai inganta ba.

Wannan yana nufi, a takaice, duk wanda ba dan Shi'a ba kafiri ne, tun daga kan Abubakar(RA) har ya zuwa ga kai mai karatun wannan littafin, in kai ba dan Shi'a ba ne.

To jama'a, ina karyar hadin kai? Ina karyar takrib da ta'aruf da ''Islam One''? Ina da'awar cewa Musulmi duka daya ne?

Yaya masu barranta daga Abubakar da Umar da Usmanu da A'isha da Hafsa da mabiyansu da magoya bayansu za su hada kai da wani? Shin ana hada kai da kafiri wanda yake goyon bayan mafiya sharrin halittar Allah a bayan qasa?

Amma ba a nan batun ya kare ba. Saurari hukuncin nasibawa waxanda suka yarda da khalifancin Abubakar da Umar, suka fifita su a kan Ali.
Batun: Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi