LADDUBAN MUSULMI: LOKACIN SANYI
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=815

 
LADDUBAN MUSULMI: LOKACIN SANYI

* ﺑﺴﻢ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ*


Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Wanda yake jujjuya yanayi yanda yaso, Wanda cikin hakan ayoyi da izinoni, yabo da aminci Annabi Muhammad da iyalansa da sahabbansa, lokacin sanyi lokacine mai falala da mumini ke iya ribatarsa wajen neman yardar Allah, hakika magabata sun kasance suna bushara da murna da zuwansa ﻗﺎﻝ ﻋﻤﺮ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ:

) ﺍﻟﺸﺘﺎﺀ ﻏﻨﻴﻤﺔ ﺍﻟﻌﺎﺑﺪﻳﻦ )
ﻭﻗﺎﻝ ﺍﺑﻦ ﻣﺴﻌﻮﺩ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ : )ﻣﺮﺣﺒﺎً ﺑﺎﻟﺸﺘﺎﺀ ﺗﺘﻨﺰﻝ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﺒﺮﻛﺔ ﻭﻳﻄﻮﻝ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﻟﻠﻘﻴﺎﻡ ، ﻭﻳﻘﺼﺮ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﻨﻬﺎﺭ ﻟﻠﺼﻴﺎﻡ).

ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﺍﻟﺒﺼﺮﻱ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ : ) ﻧﻌﻢ ﺯﻣﺎﻥ ﺍﻟﻤﺆﻣﻦ ﺍﻟﺸﺘﺎﺀ ﻟﻴﻠﻪ ﻃﻮﻳﻞ ﻳﻘﻮﻣﻪ ، ﻭﻧﻬﺎﺭﻩ ﻗﺼﻴﺮ ﻳﺼﻮﻣﻪ ).


Akwai ladduba da HUKUNCE-HUKUNCE daya kamata mu kiyaye daga cikinsu:

1: *RIBATARSA DA IBADU MUSAMMAN AZUMI,*
yazo a hadisi Wanda malamai sukayi sabani kan ingancinsa, sai dai ya tabbata daga sayyidina Abu huraira, '' ﺍﻟﻐﻨﻴﻤﺔ ﺍﻟﺒﺎﺭﺩﺓ ﺍﻟﺼﻮﻡ ﻓﻲ ﺍﻟﺸﺘﺎﺀ'' *Ganima mai sauki azumi lokacin sanyi*.

babu shaka yin azumi a sanyi garabasa ne saboda abubuwa kamar haka:

A: Gajartar hantsi da raguwarsa.

B: Rashin zafin rana.

C: Saukin qishirwa.

2: *KIYAYE SHAN RUWA:*
wannan abin neman a likitance, Saboda yin sakaki da shan ruwa yana janyo Rashin lafiya, Bincike na lafiya, ya nuna cewa sakaki da shan ruwa a lokacin sanyi yana janyowa mutuwar karaf daya, saboda idan mutum yabar shan ruwa zuciyarsa zata tsaya daga aiki.

Don haka masu Kula da lafiya suna bada shawarar shan ruwa kafin bacci da bayan tashi daga bacci, da lokacin cin abinci.

3: *Anfani da ruwan zafi wajen wanka da tsaftace jiki,*
Domin ba jarumta bane yin Amfani da ruwa me tsananin sanyi lokacin sanyi domin yana iya janyo mutum Rashin lafiya, Addinin yazo da kare lafiya da ran mutum.

Allah yace:

[ ﻭﻻ ﺗﻠﻘﻮﺍ ﺑﺄﻳﺪﻳﻜﻢ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺘﻬﻠﻜﺔ]☆ Kuma yace [ ﻭﻻ ﺗﻘﺘﻠﻮﺍ ﺃﻧﻔﺴﻜﻢ ﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻛﺎﻥ ﺑﻜﻢ ﺭﺣﻴﻤﺎ]☆ Yazo a hadisi cewa wasu sahabbai sunyi fatawa ga wani dan-uwansu da janaba ta sameshi, lokacin sanyi.

Kuma suna matafiya, kuma bashida lafiya.

Dayayi wanka da ruwan sanyi sai ya mutu, da suka dawo suka fadawa manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam sai yace:

*[ﻗﺘﻠﻮﻩ ﻗﺘﻠﻬﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻻ ﺳﺄﻟﻮﺍ ﺣﻴﻦ ﺟﻬﻠﻮﺍ ﻓﺎﻧﻤﺎ ﺷﻔﺎﺀ ﺍﻟﻌﻲ ﺍﻟﺴﺆﺍﻝ ]*
4: *KYAUTATA ALWALA DA CIKATA, KOMAI TSANANIN SANYI,*
saboda hadisin da Muslim ya rawaito ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ'' ﺃﻻ ﺃﺩﻟﻜﻢ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ ﻳﻤﺤﻮ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻪ ﺍﻟﺨﻄﺎﻳﺎ ﻭﻳﺮﻓﻊ ﺑﻪ ﺍﻟﺪﺭﺟﺎﺕ: ﻗﺎﻟﻮﺍ: ﺑﻠﻰ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻗﺎﻝ: ﺇﺳﺒﺎﻍ ﺍﻟﻮﺿﻮﺀ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﻜﺎﺭﻩ، ﻭﻛﺜﺮﺓ ﺍﻟﺨﻄﺎ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻤﺴﺎﺟﺪ ﻭﺍﻧﺘﻈﺎﺭ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﺑﻌﺪ ﺍﻟﺼﻼﺓ، ﻓﺬﻟﻜﻢ ﺍﻟﺮﺑﺎﻁ ﻓﺬﻟﻜﻢ ﺍﻟﺮﺑﺎﻁ '' ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ.


*Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yace shin* *bazan fada muku abinda Allah yake safe kurakurai dashi ba, kuma yake daga darajoji dashi.*
*Suke eh ya manzon Allah.*
*Sai yace:*
*CIKA ALWALA TAREDA SAMUN ABABEN DA ZASU SA KIN HAKAN.........................*
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﻮﻭﻱ ﻓﻲ ﺷﺮﺡ ﻣﺴﻠﻢ:

ﻭﺇﺳﺒﺎﻍ ﺍﻟﻮﺿﻮﺀ ﺇﺗﻤﺎﻣﻪ ، ﻭﺍﻟﻤﻜﺎﺭﻩ ﺗﻜﻮﻥ ﺑﺸﺪﺓ ﺍﻟﺒﺮﺩ ﻭﺃﻟﻢ ﺍﻟﺠﺴﻢ ﻭﻧﺤﻮ ﺫﻟﻚ. ﺍﻧﺘﻬﻰ .

5: *KIYAYE SALLAR ASUBA CIKIN JAM'I*
hadisai daya sunzo suna tsoratarwa kan Rashin halar asuba da isha a jam'i, Har manzon allah yace sune sukafi nauyi ga munafukai, kayi kokari ya kai bawan allah ka ceci kanka daga fadawa gungu muafukai da barin sallar asuba lokacin sanyi domin bakasa sanda mutuwa zatazo maka ba, Hakanan hadisai sunzo suna bushara ga masu kiyeye sallar asuba a lokacinta cikin jam'i, malamai sukace wadannan hadisai sun kunshi kusan busharori goma ga masu kiyayeta.

6: *RAYA SUNNAR SHAFA KAN HUFFI KO SAFA:*
Lalle shafa kan huffi ko safa ya halatta ga matafiyi da Wanda ke zaune a gida, idan ya saka huffi ko safa lokacin da yayi alwala yayi niyyar shafa kansu, duk lokacin da zai jaddada alwala, Kwana daya da Yini ga mazaunin gida, kwana uku ga matafiyi, Matukar mutum bai kwabe suba aciki wannan lokacin to lalle zai iya shafa a kansu, Wannan yana daga cikin sassaucin shari'a da dage damuwa, musamman lokacin sanyi da ake yawan saka huffi da safa, cirewa da sawa akwai damu ga mutum, sai Allah ya dage wannan damuwar da shafa kan huffi da safa, ya qayyade lokaci na hakan domin kiyaye safta, wannan yana daga cikin ababe masu kayatarwa a addini.

7: *TANADAR ABIN DUMAMA RUWA GA MASU AURE DA GWAGWARE:*
saboda mai aure idan ya sadu da iyali zai bukaci ruwan zafi, idan bashida abin dumamawa sallah da alkairai dayawa zasu iya kubuce masa, musamman da daddare, Hakanan yawan mafarke- mafarke yana faruwa ga gwagware lokacin sanyi musamman da dare, sai hakan yasa suna rasa sallah akan lokacin ta, saboda ga sanyi babu abin dumama ruwa, abinda ya kamata shine mutun ya samu abinda zai rika taskance ruwan zafi dashi.

Domin yin Amfani dashi idan ya bukata.

8: *WASU HUKUNCE- HUKUNCE DA YA KEBANCI LOKACIN SANYI:*
1: Hada sallah biyu kamar azahar da la'asar da isha da asuba, saboda sanyi me tsanani tareda iska.

2: yin sallar nafila kan abun hawa dabbace ko mota.

3: yin adu'a lokacin da iska ta taso, { ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﺳﺄﻟﻚ ﺧﻴﺮﻫﺎ ﻭﺧﻴﺮ ﻣﺎ ﺃﺭﺳﻠﺖ ﺑﻪ، ﻭﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﺷﺮﻫﺎ ﻭﺷﺮ ﻣﺎ ﺃﺭﺳﻠﺖ ﺑﻪ }.

9: *RASHIN CAKUDUWA A MAKWANCI:*
Cakuduwa a makwanci daya, da abin rufuwa daya, ga yara da suke iya rarrabewa, ko ga wadanda suka balaga, mummunan hali daya kamata mu kiyaye wajen tarbiyyar yaranmu.

10: *KULA DA AYOYIN ALLAH DA TADABBURINSU:*
lalle cikin caccanzawar yanayi akwai ayoyi Allah da izina daya kamata mu dauka, wasuma sunzo cikin nassosin shari'a, daga ciki hadisin Abu huraira r.d.

ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﻗﺎﻝ: ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ } :ﺍﺷﺘﻜﺖ ﺍﻟﻨﺎﺭ ﺇﻟﻰ ﺭﺑﻬﺎ ﻓﻘﺎﻟﺖ: ﻳﺎ ﺭﺏ. ﺃﻛﻞ ﺑﻌﻀﻲ ﺑﻌﻀﺎً ﻓﺠﻌﻞ ﻟﻬﺎ ﻧﻔﺴﻴﻦ؛ ﻧﻔﺲ ﻓﻲ ﺍﻟﺸﺘﺎﺀ ﻭﻧﻔﺲ ﻓﻲ ﺍﻟﺼﻴﻒ ﻓﺸﺪﺓ ﻣﺎ ﺗﺠﺪﻭﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﺮﺩ ﻣﻦ ﺯﻣﻬﺮﻳﺮﻫﺎ ﻭﺷﺪﺓ ﻣﺎ ﺗﺠﺪﻭﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﺤﺮ ﻣﻦ ﺳﻤﻮﻣﻬﺎ { ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ.

Wannan ya nuna sanyi ma daga fucin jahannama ne, Wannan zai kara saka mana tsoranta, da nisantar abinda zai jefamu cikinta.

11: *KASHE WUTA MURHU DATA JIN DUMI:*
Lokacin sanyi ana yawan gobara da daddare, saboda iska da akeyi, da sakaki da wasu keyi nayin bacci Subar wuta basu kashe ba, lalle wannan ya sabawa shari'a.

Hadisai sunzo da hani kan haka:

ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻣﻮﺳﻰ ﺍﻷﺷﻌﺮﻱ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ:

}} ﺍﺣﺘﺮﻕ ﺑﻴﺖ ﺑﺎﻟﻤﺪﻳﻨﺔ ﻋﻠﻰ ﺃﻫﻠﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﻠَّﻴﻞ، ﻓﺤُﺪِّﺙ ﺑﺸﺄﻧﻬﻢ ﺍﻟﻨَّﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ، ﻗﺎﻝ '' ﺇِﻥَّ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﻨَّﺎﺭُ ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﻫِﻲَ ﻋَﺪُﻭٌّ ﻟَﻜُﻢْ , ﻓَﺈِﺫَﺍ ﻧِﻤْﺘُﻢْ ﻓَﺄَﻃْﻔِﺌُﻮﻫَﺎ ﻋَﻨْﻜُﻢْ ،''{{ ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ .

ﻭﺭﻭﻯ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﻣﺴﻠﻢ ﻣﻦ ﺣﺪﻳﺚ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ, ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨَّﺒﻲُّ ﺻﻠَّﻯﺎﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠَّﻢ} : ﻻَ ﺗَﺘْﺮُﻛُﻮﺍ ﺍﻟﻨَّﺎﺭَ ﻓِﻲ ﺑُﻴُﻮﺗِﻜُﻢْ ﺣِﻴﻦَ ﺗَﻨَﺎﻣُﻮﻥَ } ''.


Wadannan hadisai ne na manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam da suke hani kan barin wuta ba'a kasheta ba lokacin bacci, Sai dai wannan gamamme ne da lokacin sanyi Dana zafi, Sai dai lokacin sanyi yafi karfi sabo anfi yin sakaki ita.

Allah yasa muna cikin masu cin ganimarsa da neman yardar Allah.

ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻋﻠﻢ ﻭﺻﻞ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻠﻰ النبي 
Batun: Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar