WANENE YAKAMATA YAFARAYIN SALLAMA.... WANDA YABUGO WAYA KO WANDA AKA BUGAWA??
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=817

 
WANENE YAKAMATA YAFARAYIN SALLAMA.... WANDA YABUGO WAYA KO WANDA AKA BUGAWA??

Babban Malamin nan kuma Masanin Ilimin Hadith a Wanna Zamanin Ash-sheikh Al-Allãmah Muhammad Nasiruddeen Albãny Yace :

Acikin Littafin :

Al-aqeedatu Auwalan Lau kãnu ya'almun Mujalladi na 1 Shafi na 16-17.

MALLAM Yace :

Abinda Yakamata ga wanda aka bugawa (waya) shine Idan yadauka Yace : NA'AM..... sai shi wanda yabugo wayar idan yaji andauka sai yafarayin SALLAMA, sai kuma wanda aka bugowa wayar shima Ya amsa sallamar..... Ba wai shi (wanda aka bugawa wayar) ne zai farayin sallamar ba.
Shehin Malamin yaci gaba da cewa WANNAN SHINE ABINDA YADACE AYI WANDA NA SANI , sbd mai nemanka a waya kamar mai kwankwasa kofa ne ba su da banbanci (kuma a qã'idah mai kwankwasa kofa Shine yake farayin Sallama '' .

YA ALLAH KAKARA MANA ILIMI MAI AMFANI KUMA KA AZURTA MU DA AIKI DA ABINDA KASANAR DA MU ABISA TAFARKIN ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM.

KANASON ALJANNAH CIKIN SAUKI??

Abdullahi Muhammad Auwal

KANASON ALJANNAH CIKIN SAUKI??

TO GA MAFITA...

Manzon Allaah sallallaahu alaihi wasallam yana cewa:

A wani hadisin kuma yana cewa:

Ma'ana: (Duk wanda yabi wata hanya ko ya ri'ki wata hanya wanda yike neman ilmi a cikinta; to Allaah zai sau'ka'ke yakuma yassare mishi da wannan ilmin hanya zuwa Aljannah).

Wannan hadisin ya nuna mana girma da falala da ilmi ke dashi, daga cikin falalar – wadda kuma itace mafi girma – shine samun Aljannah.

Sai dai wannan hadisin yana maganane akan ilmi na shari'ah kamar yadda wasu malaman suka fassarashi tareda wasu nassoshin Qur'ani da hadisi, sai dai duk wani ilmi mai amfani wanda shari'ah ta yarda dashi shima zai iya shiga karkashin wannan hadisi mai girma kamar yadda wasu malaman suka nuna hakan.

Amma mutum bazai samu wannan falalar ba, sai da sharudda kamar haka:

1- Yi dan Allaah.

2- Bin dokokin Allaah a cikinsa.

3- Aiki da ilmin.

4- Kokarin amfanar da al'ummah da ilmin.

MUNA FATAN ALLAAH YASA MUNA CIKINSU, WADANDA KUMA BASU KAMA HANYAR ILMI BA ALLAAH YASA SUGANE.
Batun: Al'Adun Musulmi Da Darajoji