TAKAITACCEN TSOKACI A KAN JAWABIN SHEIK DAHIRU BAUCHI
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=822

 
Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

TAKAITACCEN TSOKACI A KAN JAWABIN SHEIK DAHIRU BAUCHI

Jawabin da Malam Dahiru Bauchi ya yi a shirin safe na BBC hausa a yau 21/5/2015, hakika ya fadi daidai cikin wani sashi nasa, ya kuma kasa fadin daidai cikin wani sashi nasa.Ya fadi daidai a inda ya kafirta 'yan Tijjaniyyar nan da suka yi bukin maulidin Sheik Ibrahim Inyas a garin Kano, sannan a wajen wannan buki nasa wasunsu suka yi ta furta kalaman batunci ga Annabi Mai tsira da amincin Allah.

Amma bai fadi daidai ba a inda ya ce babu abin da ake kira Ahlul Hakikati cikin Darikar Tijjaniyyah, ya kuma fadi hakan ne duk kuwa da cewa a cikin Darikar tijjaniyyah a kwai yarda da abin da ake kira Wahdatul Wujudi, shi kuwa Wahdatul Wujudi tabbas yana daga cikin lazimin wannan akida yarda da irin maganar cewa Ibrahim Inyas Allah ne.
Ko shakka babu a cikin darikun Sufaye musamman Darikar Tijjaniyyah a kwai gurbatattun akidu daban daban na tozarta Alqur'ani, da tozarta Manzon Allah mai tsira da amincin Allah, da ma tozarta Zatin Allah shi kanSa, hakika dukkan masu nazarin littattafan wadannan darikun sun san da haka.

To amma dai a takaice muna iya cewa an dan samu ci gaba cikin jawaban da shi Malam Dahiru Bauchi ya yi; domin a da irin wannan bayanin ne na bayyanar da kafircin wasu akidu na Sufaye idan Ahlus Sunnah masu Da'awah suka bayyana su ga Duniya zai a ji wasu daga cikin masu gafala ko son zuciya suna ta cewa: 'Yan Izala na kafirta Musulmi!

Muna fata Malaman Sufaye a ko ina suke za su yi hakuri, su kara tunani su sa tsoron Allah cikin lamuransu su daure su yi Musuluncin nan kamar yadda Annabi Mai tsira da amincin Allah tare da Sahabbansa suka yi shi. Allah Ya taimake mu.

Ameen.Batun: Al'Adun Musulmi Da Darajoji