Hukuncin wanda yayi Sallah ba zuwa ga Alqibla ba A mantuwa
 
Wannan Labari Ya fito Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
URL na Wannan Labari Shine:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=830

 
Hukuncin wanda yayi Sallah ba zuwa ga Alqibla ba A mantuwa

Tambaya: Meye hukuncin mutumin da yayi sallah, sai bayan ya gama sannan ya fahimci cewa wannan sallah da yayi ba Alqibla ya fuskanta ba?

Amsa: yana daga cikin sharadin sallah mutum ya fuskanci Alqibla matukar ba wata matsala aka samu ba wadda zata hanashi hakan, inhar ko mutum yaki fuskantar Alqibla alhalin yana da dama toh sallarsa batacciya ce, sabida Allah yace ''Ka juya da fuskarka zuwa ga masallaci Tsararre'' (Baqara 144). Da umarnin da annabi(Sallallahu alaihi wasallam) yayi yace ''Sannan ka fuskanci alQibla kayi kabbara) Bukhari 6667.
Maluman sun tafi akan cewa wanda yayi sallah ba zuwa ga Alqibla ba da gangan ko a halin mantuwa zai sake, sabida bai cika sharadinta ba, an tambayi maluman 'Lajnatudda'imah' kan hukuncin matafiyi da ya isa gari, yayi sallah ba zuwa ga alqibla ba, kuma bai tambaya ba, baiyi bincike ba, suka bada amsar cewa zai sake wannan sallar, sabida rashin bincike da baiyi ba, ko kokari wurin gano alqiblar, (Lajnatudda'imah Majmu'ah ta biyu 5/294).

Da haka, ya wajaba akan wanda yayi sallah ba zuwa ga Alqibla ba yana mai mantuwa ya sake sallansa, amma in ya rasa gane Alqibla sabida rashin wanda zai tambaya, ko kuma wasu dalilai, toh mafi yawan Malamai suna akan bazai sake ba. kuma hakan shine daidai......... Allahu A'alam.

Maraba Da watan Ramadan Watan Albarka

Maraba Da watan Ramadan Watan Albarka

Assalaamu Alaikum Warahmatullahi Wabarkaatuh 'yan'uwa Musulmai ina tayaku murnan Shigarmu wannan wata ta ramadana Mai Albarka. Ina rokon Allah Ya azurtamu dayin aikin alkhairi acikinta, kuma Yasa ayyukanmu su zamto karbabbu, Allah kuma ya yaye mana duk bala'I da musibu da suke addabarmu Yasa Mugama Lafiya.

Bayan Haka inaso in dan jaa hankalinmu ne kan wasu lamura da ya dace muyi acikin wannan wata mai albarka, da kuma abinda ya dace mu kiyaye. Babban abinda wannan wata ta kunsa na ibada itace azumin watan ramadan wanda wannan farilla ce kuma tana daga cikin rukunan musulunci guda biyar. Wadda duk wanda Allah yabashi iko dolene a gareshi yayi wannan azumi. sannan bayan azumi sai tsayuwar dare da ake kira 'tarawihi' shi kuma wannan 'sunnah ce mai karfi' wadda akeso musulmi Ya kiyayeta acikin wannan wata kuma yayita tare da jama'a acikin masallaci sai dai in akwai uzuri. Wannan sallah raka'a 'goma sha daya ce' kaman yanda ya tabbata a hadisin Aisha(R.A) tace :'Manzon Allah ya kasance baya karawa akan raka'a sha daya a sallan dare acikin ramadan ko a wajensa' tsayawa kan raka'a sha daya shi zaifi samar wa mutum natsuwa sosai sannan kuma hakan zai taimaka masa wurin kauce wa tsabanin malamai ga masu Ganin ana iya yin har ashirin da daya, sannan bayan wa'innan ibadu biyu na azumi da tarawihi anaso mutum ya yawaita karanta Alqur'ani mai girma, domin wannan watace ta Qur'ani, sannan karatun qur'ani a wannan wata tana kawo wa mutum lada matuka domin kaman yanda muka sani ne duk wata aikin lada a ramadan ana ninkata. Sannan kuma da halartar majalisin da ake karatun Qur'anin, ko tafsirinsa domin yin tadabburi da Qur'anin da sanin ma'anoninsa. Sannan kuma sai yawaita salatin annabi da zikirori. Ya kamata musulmi ya kasance a kowani lokacinsa ya jike bakinsa da salatin annabi, da kuma zikirori ingantattu wanda suka tabbata. Hakan zai taimakawa mutum da kare kansa da yawan surutai da basu da amfani ko kuma shiga wata hayaaniya. Sannan kuma ya kamata musulmi ya kaurace wa duk wata tsabon Allah, duk abinda zai zamanto cewa tsabon Allah ne toh ya zama wajibi mutum ya kauce mata. Domin azumi bawai kawai kamewa daga abinci ko abin sha bane, A'a ta kunshi kamewa daga duk tsabon Allah, ta maganar banza, ko zage zage, ko gulma, ko kallace kallace da sauransu. Sai mu kiyaye 'yan'uwa. Muyi duk abinda mukasan zai jawo mana yardar Allah, mukauce wa duk abinda zai janyo mana fushinsa. Sannan kada ya zamto bayan gushewar ramadan mudawo muci gaba da ayyukanmu marasa kyau, ya kamata koda bayan ramadan ne muci gaba Da ayyuka ta ibada da biyayya ga Allah da mukeyi acikin ramadan. Ina fatan Allah ya sadamu da alkhairansa. Wassakamu alaikum.



 

Batu: Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen


Comments 💬 التعليقات