Sharrudan da suke halasta wa mutum yayi tafiya zuwa garin kafirai
 
Wannan Mataki Na Daga
EsinIslam Media :: http://esinislam.com/MediaHausa
 
Da URL Wannan Labari Ba:
http://esinislam.com/MediaHausa/modules.php?name=News&file=article&sid=839

 
Daga Sharhin riyaadussaliheen na Ibn Uthaymeen

Sharrudan da suke halasta wa mutum yayi tafiya zuwa garin kafirai

•Sharadin Farko: ya zamto mutum yana da ilimi da zai iya kawar da shubuhohi da za'a iya bujuro masa dashi, domin kafirai sukan bijuro wa musulmai shubuhohi dabam dabam, Shubuhohi kan Dabi'un musulmai, da koma meye, domin musulmi ya zamto cikin shakka a koda yaushe, ya zamto bashi da Alqibla, kuma abune sananne inhar mutum yayi shakka kan abinda yake wajibi ne a kudurce ta hakika, toh bai kawo wajibin abinda yake akansa ba,Su kafirai kullum suna shigar wa musulmai shakka, wani daga cikin shuwagabanninsu yake cewa:

kada kuyi kokarin fitar da musulmi daga addininsa zuwa addinin kirista, ya isheku idan ku ka sanya masa shakka kan addininsa, domin idan kuka sanya masa shakka kan addininsa toh kun cireshi daga cikin addinin, wannan ya isar.

Wannan sharadi na farko kenan, ya zamto mutum yana da ilmi gwargwado da zai iya mayar da shubuhohin da zai iya fuskanta in yaje can.
•Sharadi Na Buyu: ya zamto yana da riko da addininsa, wanda wannan riko da addinin nasa zata kiyayeshi wurin fadawa fitinar son zuciya, irinsu shan giya, zina, da sauransu, domin mutum in ya kasance baya riko da addininsa, yayi tafiya irin wannan ana masa tsoron fadawa cikin irin wa'innan nau'uka na tsabon Allah, domin da tsoron Allah ne mutum zai sami karfin kauce wa irin wa'innan ayyukan tsabo.

•Sharadi Na Uku: Ya zamto cewa mutum yana da bukatan wannan tafiya, bawai kawai tafiya ce ta ba dalili ba, kaman ya zamto cewa mutum bashi da lafiya, kuma yana da bukatan zuwa wata kasa daga cikin kasashen kafirai domin neman magani, ko kuma mutum yana neman wani ilmi wanda wannan ilmin babu shi a kasashen musulmai, sai ya tafi zuwa can domin ya koyo wannan ilimin, ko kuma mutum na neman wata kasuwanci sai ya tafi can yaje yayi ya dawo, ma'ana kaman yaje ya sayo wani abu awurin da babu awurin da yake, ko wani abu mai kama da haka, abu muhimmi dai shine ya zamto mutum yana da dalilin zuwa,

A dalilin haka ne ma malam yake ga cewa masu zuwa kasashen kafirai domin yawon shakatawa masu laifi ne, yana ganin duk kudin da aka kashe a dalilin wannan tafiya mara dalili toh haramun ne, kuma hakan bata dukiya ne, kuma za'ayi musu hisabi akan haka, domin irin wannan tafiya yana sabbaba bata lokaci da dukiya da kuma bata dabi'ah, domin mutum mai irin wannan tafiya da wuya kaga ya dawo bai dauko wata dabi'a mara kyau ba, Allah ya kiyayemu wassalatu wassalamu Ala Rasulillah.

Wannan Nassin Bayanin na cikin sharhin Riyadussaliheen na Ibn Uthaymeen karkashin sharhin hadisin farkoBatun: Al'Adun Musulmi Da Darajoji